Monday 3 October 2016

Amfani da Kalandar Miladiyya a Saudia

Daga Shehin Musulunci a fcbk
Mal Baban Hamnda

Amfani da Kalandar Miladiyya a Saudia.

Dan shi'a ne ya yi qarfin halin yi min inbox, wai tun a sunanta ma ita qasar larabawa ce ba ta Musulunci ba, ga shi yau ta koma kalandar bature, don haka Iran ce qasar Musulunci tun daga sunanta ma.

Na so ba inbox yayi ba don kar ya musanta ya muka yi da shi, ko ya ce na sauya magana, ko mun yi abu a surru na tona, etc.

To dama dai an sani sarai Saudia zata yi anfani da watan miladiyya ne kawai wajen biyan albashi sabo da matsalar tattalin arziqi. Wannan matsalar an fara ta a manyan qasashen duniya tun kusan shekara 10 baya. Don haka Saudia ta ciri tuta da ta kawo yanzu ko gezau bata yi ba.

Abin sani a nan shi ne, anfani da kalandar hijira tana wajaba ne kawai a ayyuka na ibada, a sauran lamurra Ba wajibi bane. Tun kusan shekaru 10 baya aka yi wa malamai fatawa:

ماحكم استعمال التقويم الميلادي بدلا من الهجري لأسباب كثيرة منها دقة الميلادي في تحديد الأيام ؟

'Ina hukuncin anfani da kalandar Miladiyya a bar ta Hijiriyya sabo da dalilai da yawa, kamar takamaiman yawan raneku dake kalandar Miladiyya?'

Malamai sun kawo nassoshi da maganganun magabata kan wajabcin anfani da kalandar hijiriyya a ayyukan ibada, a sauran abubuwa suka ce:

فالأولى استعمال التقويم الهجري ويمكن أن تقارنه بالتقويم الميلادي

'abin da yafi ko dai a yi anfani da iya kalandar Hijriyya ko kuma a hada ta da Miladiyya'

وأما الاقتصار على الميلادي فيخشى عليه أن يكون فيه عدول عن التوقيت الذي جعله الله للناس مع اتباع الغير في شأنه.

'amma idan aka taqaita a iya Miladiyya to ana tsoron kar a watsar da tsarin lokacin da Allah Ya halastawa mutane shi a bi waninsa"

ثم إنه ليس عندنا نص يفيد منعه ولكن الأولى الالتزام بالتاريخ المعروف عند المسلمين المنصوص في القرآن والسنة

'duk da cewa yin anfani da kalandar da Musulmi suka fi sani, wadanda sune a aka anbace su a Qur'ani da Sunnah, shi ne ya fi, ba mu da dalilin cewa (yin anfani da kalandar miladiyya kadai) laifi ne'

Fatawa mai lamba 106346 ta ranar Alhamis 20 Rabi'ul Auwal 1429 (27/03/2008) a islamweb.

Za a a lura daga fatawar malamai:

1. Dayan biyu duk wanda aka yi dace; ko dai anfani da kalandar Hijriy ita kadai ko kuma a gwama ta da ta Miladiyya; ko su ma a kwanan watan fatawar gwama biyun suka yi.

2. Taqaituwa a kalandar Miladiyya a abubuwan da ba na ibada ba, ba laifi bane sam sam sam.

Kenan, ba wani abu da za a ce a haqiqa ya sauya a Saudiyya domin ta gwama biyun ne, kuma dama can tana anfani da duka biyun a wasu abubuwan, kawai ta shigar da albashi ne yanzu a jerin wadanda Miladiyya za ta shafa. Amma ba wai ta sauya daga Hijriyya zuwa Miladiyya bane ko kadan.

In ma kuma da duk abubuwan da ba na ibada ba, dukan su, za ta taqaita a iya Miladiyya da bata sabawa Allah ba ko kusa, kenan ba wanda yake da haqqin tuhuma ko yi wa Saudiyya kallon banza.

Iran: na san zai yi wahala dan shi'ar ya iya futowa gaban jama'a ya tada wannan maganar, domin tambayar da na masa ta gigita shi ita ce 'in ka tuhumi Saudiyya, ko zaka iya fada min da wace kalanda ake anfani a Iran?'

Duk duniya ba dan shi'ar da zai iya tsayawa ya tunkare ka da wannan maganar, domin a Iran ba wai iya ayyukan mu'a'maloli ba, hatta na ibadar ma ba da kalandar Musulunci suke anfani ba, da kalandar majusancin su suke anfani.

Kuma ba za su iya kare kan su a kan wannan ba.

To yanzu don Allah in banda dan shi'a bakin Ibnu Taimiyya ya kama shi, ta yaya me wannan zai qalubalanci Saudiyya?

Don haka dai Saudiyya bata aikata ko makruhi ba balle zunubi balle a sami damar batanci gare ta.

Allah Ya nuna mana gaskiya Ya bamu ikon bin ta. Allah Ya taimaki Shugabannin Qasa mai Tsarki Ya kare su daga sharrin maqiya da wawaye.

No comments:

Post a Comment