Sunday 12 February 2017

Yada Hoton Gawa

Daga Malaminmu:

Dr. Muhd Sani Umar

Yada Hoton Gawar Dan Uwanka Mumuni Ba aiki Ne Na Masu Sanin Ya Kamata Ba

Wadanda suke dauko hutunan gawawwakin 'yan uwansa musulmi suna yadawa a dandalin sadarwa, wai don su sanar da rasuwarsu ko su yi ta'aziyyarsu, masu yin haka ba sa kyautawa ko kadan. Yin haka alama ce ta rashin wayewa da karancin fahimtar addini.

Gawar dan uwanka tana da alfarma da mutunci, bai kamata ka keta masa wannan mutuncin ba bayan mutuwarsa. Shi ya sa ko wankan gawa ba kowa ake sa wa ba sai wanda aka yarda da shi.

Ka duba, mutum ko barci yake yi ba zai so a dauki hotonsa ana yadawa ba, saboda ba lalle ne ya kasance cikin yanayin da zai so a gansa a cikinsa ba. Ka dubi yanayinka kai kanka, idan za a dauki hotonka kakan shirya don ganin hotonka ya yi kyawon kama, to don menene za ka rika baza hoton gawar dan uwanka bayan mutuwarsa? Kuma shin ba za a yarda da labarin mutuwarsa ba ne sai ka sa hotonsa?

Abin takaici ma wani lokaci wani ya jima da rasuwa amma idan wani ya zo magana a kansa sai ya sako gawarsa a cikin wani yanayi wanda bai dace ba sam, kuma shi mamacin da yana da rai ba zai so a gan shi a wannan yanayin ba.

Wani lokaci 'yan uwa za su yi hadarin mota suna kwance kace-kace cikin jini, sai wani sakarai ya dauko hotunansu yana bazawa wai shi a tunaninsa daidai yake yi, tir da irin wannan aiki na rashin nutsuwa.

Mu kiyaye hakkin yan uwanmu bayan mutuwarsu kamar yadda muke kiyaye shi a lokacin rayuwarsu. Allah ka ba mu kyakkyawar fahimta. Amin.

Sunday 5 February 2017

Rashin Lafiyar Buhari

Rashin lafiyar Buhari.

Daga Malam Baban Hamdan

Da farko dai Buhari mutum ne, bawan Allah, akwai rashin lafiya a kan sa akwai mutuwa, don haka in Buhari ya yi rashin lafiya ko ya mutu ba wani abu ne da ya sabawa al'ada ba.

Allah Ya wa Buhari ni'imomi da yawa da bai wa da yawan mutanen duniya ba. Yau ina shugabannin qasar da su ka yi mulki tare da Buhari a lokacin da ya shugabanci qasar nan a karon farko? Da yawa na sun mutu ba? Wasu tun tuni ba su da lafiya, wasu al'ummar qasar su ne su ka taru su ka kawar da su don ba sa son su, amma yau Buhari ba shi da lafiya duk wani mutumim azziki ya damu, har munafukan da su ke sukansa a baya sun gaggauta lashe amansu na sukansa da su ke yi.

To ku sani, kada rashin lafiyar Buhari ta tada muku hankali, kamar yadda Mallam Garba Shehu ya fada, Buhari ba cikin wani matsanancin yanayi ya ke ba, ko alama.

Ah, yo to ma idan kuna ganin abin da muke fada ba haka bane, ina hankulanku su ke? Ashe ba ku san rashin lafiyar ko wane shugaban qasa a duniyar nan babban labari ne ga manema labaran duniya ba? Shugaban Qasarku ne, amma a tunaninku kun fi kafafen yada labarai na qasa da qasa qishin ruwan son sanin halin da Buhari ya ke ciki da rawar qafar yadawa?

Balle Shugaban Qasa kamar Buhari, lamarinsa ya na maruqar daukan hankalin kafafen yada labaran qasa da qasa sabo da dalilai da yawa.

Ba na so in ja ku a wannan karon, amma insha Allah idan na sami zama zan dora daga inda na tsaya. Maganar dai ita ce kawai a ci gaba da yi wa Buhari addu'a, amma kowa ya kwantar da hankalinsa, insha Allah Buhari ya na tafe cikin nasara da Qarfin Mulkin Allah.