Friday 28 July 2017

ILLAR RABA MANYAN WAYOYI GA DALIBAN MAKARANTAR GWAMNATI TA FAMILY SUPPORT KATSINA.

ILLAR RABA MANYAN WAYOYI GA DALIBAN MAKARANTAR GWAMNATI TA FAMILY SUPPORT KATSINA.
Cikin azumin da ya gabata aka baiwa daliban wannan Makaranta manyan wayoyi kirar android tun daga yan aji 3 har zuwa 5.
Watannin da suka gabata mun taba rubutu kan irin yanda tarbiyar yaran makaranta ke tabarbarewa, ana cikin haka kuma sai ga batun raba wayoyi wanda munsan illar da ke tattare da waya a wannan zamani. Kwanakin baya munji wa'azi da ke bayanin fitintunun da ke tattare da wayoyin zamani. 
Mun samu rahotani tun daga cikin azumi zuwa yau irin yanda yaran suka tabarbare tun daga rashin maida hankali da kuma yawan sa chargi a masallatai da suke yi don su yi game da charting. Ni ganau ne a wani masallaci da nake zuwa Tafsir.
A binciken da muka gabatar a cikin wayar mun samu tabbbaci waya ce normal waya kamar sauran android kawai dai ansa wani Application na e-library wanda shima wai a wata-wata ake ma wayar subscription.
Mahaifan yara da dama sun nuna damuwarsu a satin da aka zauna mitin na iyayen yara a satin da ya gabata. Daya daga cikinsu ya bayyana "lallai su basu ji dadi ba da suka bar yaran suka amshi wayoyin ba saboda ni naga dana tsakar dare yana kallon badala da wayar, kuma koda yaushe yana online."
Da wannan makudan kudin da aka kashe wajen sanyan wayoyin nan da yara aka biyawa Waec da Neco da ya fi.
Allah ya datar da shuwagabaninmu  da yin ayyukan alkairi.
Muna kira ga gwamnatin jihar Katsina su ji tsoron Allah su amshe wayoyin.
Wannan photunan na kasa a wayar wani Ustazun yaro suke dan jss3 akwai masu munin da ban dauko su ba.