Wednesday 11 October 2017

GWAMNATIN JIHAR KATSINA NA SHIRIN BADA TALLAFIN KARATU A ISLAMIC ONLINE UNIVERSITY (IOU)
A wata zantawa da mai Girma Gwamnan Jihar katsina R.t Hon Alh Aminu Bello Masari yayi da Shugaban Jami’ar Shaharraran mai wa’azin addinai Dr. Bilal Phillips a lokacin da ya kai masa ziyarar Girmamawa a gidan Gwamnatin Jihar a ranar Alhamis 5 ga watan octoba, Shahararen Malamin ya gabatar da Jami’ar da yadda tsarin karatunta ya ke gudana. Wanda daga bisani Gwamnan jihar Katsina ya umurci mai bashi shawara kan harkar ilimin gaba da sakandire da ya tabbatar an bi hanyoyin da ya kamata don a samarwa al’umma guraben karatu a jami’ar. Dakta Bilal Philips ya zo garin Katsina ne don gudanar da Taron tunatarwa na kwana daya wanda Kungiyar Islamic Preaching and Public Services tare da hadin gwuwar HK Yaradua Islamic media su ka shirya taron mai taken ‘’Zaman lafiya da Bin Doka da Oda ga al’umma’’ taron wanda ya gudana ranar Juma’a 6/10/2017 a babban filin wasanni na Muhammad Dikko Stadium Katsina, an gudanar da taron cikin nasara wanda akalla sama da mahalarta 6000 ne su ka halarci taron wanda har da mabiya addinin kirista.
Daga cikin wuraren da Malamin ya ziyarta sun hada da Fadar mai-martaba sarkin Katsina Alhaji Abdulmumin Kabir Usman da kuma Jami’ar Al-Qalam University Katsina, Gidan Sheik Yakubu Musa Hassan Katsina (Sautus-Sunnah). Akwai kuma wasu Daliban Online University yan jihar Katsina, kungiyar Da’awah Family Support Katsina,haka nan kuma Kwamitin Masallacin Bilal Bin Rabah Katsina sun kawo ma Daktan Ziyara a masaukinsa.
Muna fatan wannan yunquri da gwamnatin jihar Katsina za tayi ya tabbata. Don wannan ba karamar dama bace ga al'ummar wannan jiha, muna kuma fatan gwamnatin za ta yi tsari na musamman don ganin an amfana da wannan jami'ar ta yanar gizo.
Usman Gambo Filin Samji
11/10/2017


Saturday 12 August 2017

A MAIDO DA SHARI'AR MUSULUNCI A JIHAR KATSINA

An yi kira da a maido da sharia'ar musulunci kamar yadda aka kafa ta a shekarun da su ka gabata. Malam Haruna Sani Na'ibin limamin Juma'a na Massalacin Jabir Bin Abdullahi da ke unguwar Kwado ya bayyana haka a wani wa'azi da aka gabatar a daren yau. Malamin ya bayyana haka ne da kuma yin kira da a kafa hukumar hisba. Daga nan Malamin ya ja hankalin jagoriri da su ji tsoron Allah su inganta aikin hajjin bana wanda shine aikin hajjin da alhazai su ka fi biyan kudi amman kuma su ka fi wulakanta.
Wadanan da wasu kiraye-kirayen sune abubuwan da Malamai guda 11 su ka dukufa suna yi don fadakar da wannan gwamnati.

Thursday 10 August 2017

RAN GADIN MU ZUWA ASIBITOCIN QANANAN HUKUMOMI



RAN GADIN MU ZUWA ASIBITOCIN QANANAN HUKUMOMI

Bayan rubutun da abokina Mubarak Rabi’u (Da’awah) yayi kan abokinsa da ya je General Hospital Katsina amman bai samu kulawa ba qarshe sai dai ya tafi wata Private asibiti akayi mashi magani. Wannan ne ya sa mu ka shirya tsaf domin fara ran gadin wasu daga cikin asibitocin gwamnatin jihar nan domin gano irin matsalolin da al’umma su ke fuskanta a cikin su fatan ko za a gyara.
Cikin ikon Allah jiya mun fara  ziyartar Comprehensive Health Care Batagarawa L.G wanda shine babban asibitin da ke cikin garin Batagarawa, Batagarawa L.G gari ne wanda babu gari mai fadin qasa a duk fadin jihar Katsina kamar sa amman abun da mu ka gani kuma mu ka ji ya tayar mana da hankali matuqa.
ABUN DA MU  KA JI KUMA MU KA GANI
Mun isa asibitin wajan 10:00pm isar mu ke da wuya mu ka shiga Male Ward anan mu ka tarar da yara Yan Makaranta guda 3 ba su lafiya, yaran su kadai ne sai wani yaro Prefect anan ne mu ka tambayi lafiyars u inda  suka bayyana mana cewa kwanan su uku anan amman  ba wata kulawa da ake masu, ba wani magani da aka rubuta masu ko aka basu, sai dai allurori da aka rubuta masu, a cikin dakin na Male ward babu tsafta ko kadan don kai kace wata ‘yar bola bola ce a ciki, sannan kofofin dakin gaba daya a 6alle su ke, ga sauro ga sanyi don gaskiya duk mai lafiyar da ya je ya kwana a dakin to lallai shima ana iya bashi gado to ina ga marar lafiya. Yaran wallahi sun zama abun tausai matuqa.
Bayan mun fito sai muka nufi Female ward anan ma mun ga yadda marasa lafiya su ke fama da kiran wani ma’aikacin jinya daga nan a kira shi ace jinin ya qare sai ka ji  acan ana qwala masa kira ana ga allurarr an kawo.
Bayan mun fito mun samu zantawa da wani mutum a cikin asibitin inda mu ka tambaye shi ya mu ka ga ma’aikacin can na jinya sai kiran shi ake  baya nan baya can, sai mutumin ya bayyana mana cewa ai shi kadai ne ke wannan aikin kullum haka yake fama a duk fadin asibitin ma’aikacin jinyar shi kadai ne. hakika a yadda mu ka ga ma’aikacin jinyar ya sadaukar da kansa ga wannan aiki sai na ga ai shi kanshi abun tausai ne. Mun je mun same shi mu ka gaisa mu ka tambaye shi ko shi kadai ne ma’aikacin jinya a cikin daren nan inda ya bayyana mana cewa ai duk fadin asibitin ma shi kadai ne kodayaushe yana cikin asibitin. Ya qara da ce mana aikin ya mashi yawa matuqa kawai dai yana yi ne don Allah, haka kuma ya bayyana mana  cewa marasa lafiya daga kusan local govt uku duk anan asibitin ake turo su. Rimi Local G da Charanchi  na cikin su inda har y ace mana yanzun haka akwai file na wani mara lafiya da aka turo mashi daga Rimi Local govt, sannan yace mana cikin dakin matan can akwai mara lafiyar da aka turo daga Jibia Local govt. ya bayyana mana cewa ai qwamma ma nan asibitin duk da ana ganin ta Comprehensive ce duk da ta Rimi General ce amman suna turo masu marasa lafiya wanda hakan ke gwada can Rimi sun fi fuskantar wannan matsalar. Wannan yasa a Ran gadin mu na gaba zamu tsallake Rimi da Charanchi muna fatan za a qara samun bayani daga wajan mazauna garuruwan.
SHAWARAR MU GA GWAMNATI
1. Muna mai bada shawara musamman ga mai girma gwamna wanda kulawar lafiyar al’ummar jihar Katsina duka tana wuyansa (ba Ciyamomi da mun ambace su) cewa ayi kokari a inganta asibitocin nan don gaskiya suna bukatar gyara fiye da gyaran da akayi ma makarantun  boko, sannan suna bukatar ma’ikata don da yawa daga cikin asibitocin nan ba ma’aikatan lafiya balle aje ga masu maintenance dss. Kuma gyaran wadanan asibitocin yafi a ciyo bashi a gina wasu asibitocin don wadanada za a gina din suma qarshe in ba a dau matakin gyaran tsaffin ba to kango za su koma.
2. Muna da dalibai masu yawa wadanda sun yo karatun nan amman suna nan suna zaman banza da gara-rambar yawo da CV. Inda za a dauke su lallai da an rage abubuwa da yawa.
Wannan shawarwarin ba wanda yafi cancanta a bas u kamar mai girma gwamna ko ince gwmantin jiha don wani na iya tunanin cewa mi ya shafi gwamnatin jiha da asibitin Local govt to wannan sai ya koma ya qara bincike lallai zai gano cewar gwamnatin jiha a mataki na farko ita ke da wannan alhaki. Sai kuma ga shi duka qanann hukumomin aljihun suna qalqashin gwamna to kun ga ko anan ma dole ne ita za a daura ma alhaki.
Daga qarshe wannan Rangadi mun yi shi ne ba don komai ba sai don fatan za a bincika a kuma dau mataki har ga Allah ba mu yi shi ba da nufin bayyana gazawar gwamnati ko su ka gare ta ba.
Mu kasance a ran gadi nag aba Insha Allah
Hassan Kabir Yaradua

08/10/2017





Friday 28 July 2017

ILLAR RABA MANYAN WAYOYI GA DALIBAN MAKARANTAR GWAMNATI TA FAMILY SUPPORT KATSINA.

ILLAR RABA MANYAN WAYOYI GA DALIBAN MAKARANTAR GWAMNATI TA FAMILY SUPPORT KATSINA.
Cikin azumin da ya gabata aka baiwa daliban wannan Makaranta manyan wayoyi kirar android tun daga yan aji 3 har zuwa 5.
Watannin da suka gabata mun taba rubutu kan irin yanda tarbiyar yaran makaranta ke tabarbarewa, ana cikin haka kuma sai ga batun raba wayoyi wanda munsan illar da ke tattare da waya a wannan zamani. Kwanakin baya munji wa'azi da ke bayanin fitintunun da ke tattare da wayoyin zamani. 
Mun samu rahotani tun daga cikin azumi zuwa yau irin yanda yaran suka tabarbare tun daga rashin maida hankali da kuma yawan sa chargi a masallatai da suke yi don su yi game da charting. Ni ganau ne a wani masallaci da nake zuwa Tafsir.
A binciken da muka gabatar a cikin wayar mun samu tabbbaci waya ce normal waya kamar sauran android kawai dai ansa wani Application na e-library wanda shima wai a wata-wata ake ma wayar subscription.
Mahaifan yara da dama sun nuna damuwarsu a satin da aka zauna mitin na iyayen yara a satin da ya gabata. Daya daga cikinsu ya bayyana "lallai su basu ji dadi ba da suka bar yaran suka amshi wayoyin ba saboda ni naga dana tsakar dare yana kallon badala da wayar, kuma koda yaushe yana online."
Da wannan makudan kudin da aka kashe wajen sanyan wayoyin nan da yara aka biyawa Waec da Neco da ya fi.
Allah ya datar da shuwagabaninmu  da yin ayyukan alkairi.
Muna kira ga gwamnatin jihar Katsina su ji tsoron Allah su amshe wayoyin.
Wannan photunan na kasa a wayar wani Ustazun yaro suke dan jss3 akwai masu munin da ban dauko su ba.



Monday 26 June 2017

GWAMNA YA SA A RUFE GIDAN GIYA


Alhamdulillah Yanzun ne ake min waya cewa Gwamna ya sa a rufe gidan giyar nan da muka ambata a jiya.
Allah ya sa kama gwamna da alkhairi ya sa a mizanin kyawawan ayyykansa.
Sannan kuma muna San qara shaidama mai girma Gwamna cewa akwai wasu gidajen duk da a lunguna suke wanda sums ya kamata a rufe. Daman ita barna wadda take bayyane ake magancewa. 

Sunday 25 June 2017

Inyamurai Sun bude sabon giya a garin Katsina

Inyamurai sun bude Sabon Giya a cikin tsakiyar garin Katsina.
A cikin Daren nan na 1 Shawwal ne dai ake bikin bude gidan giyar wanda aka ce ma kwana za ayi ana gwangwajewa. Muna kira ga mahukunta da su dauki qwaqwaran mataki kan wannan bada'la da ake Neman shigo mana da ita..

Bani kwai na sai da zakara. Ga poton giya nan mai suna Harp da kuma yadda ake gudanar da shaye-shayen a farfajiyar wajan.

Tuesday 13 June 2017

Amsoshin Tambayoyin Musabaqar Alaye Da Sahabban Annabi (S.A.W)


 Amsoshin Tambayoyin Musabaqar Alaye Da Sahabban Annabi (S.A.W)

الإجابة النموذجية
1
قال ابن عباس yفي قوله تعالى(لِكُلٍّ جَعَلْنَا مِنكُمْ شِرْعَةً وَمِنْهَاجًا) قال هي :
سبيل وسنة

رأي واجتهاد      

حكم وأخلاق
2
قال الحسين بن علي y في قولهI (ثُمَّ جَعَلْنَاكَ عَلَىٰ شَرِيعَةٍ مِّنَ الْأَمْرِ فَاتَّبِعْهَا) قال هي :
السنة

الولاية

الشيوخ
3
قال ابن عباس y: (ما يأتي على الناس عام إلا وأحدثوا بدعة وأماتوا سنة حتى تحيا البدع وتموت السنن )  هذا يدل على :

تحذير الصحابة من البدع  

خوف الصحابة على السنة          
كل ما سبق
4
قال ابن عباس رضي الله عنهما في  قوله I(أَوْ يَلْبِسَكُمْ شِيَعًا ) هي :
الأهواء المختلفة                    

الحيرة والشك                

الحق والعدل              
5
ناظر عبد الله بن عباس yالخوارج وبين لهم الحق بالدليل والبرهان فرجع منهم إلى الحق ألفان . رواه النسائي والبيهقي ..  تدل هذه المناظرة على
حرص الصحابةy على هداية الناس

صحة منهج الخوارج

عدم الرجوع إلى الحق
6
في صحيح البخاري ، وسنن أبي داود: قال ................. لأبيه عليِّ بن أبي طالبt: أيُّ الناس خير بعد رسول الله rقال: أبو بكرt، قلت: ثم مَن؟ قال: ثم عمرt  .       من القائل ؟ :

الحسن بن عليt

الحسين بن عليt
محمد بن علي بن الحنفية رحمه الله
7
يتولون أزواج النبي rويترضون عنهن، ويعرفون لهن حقوقهن، ويؤمنون بأنهن أزواجه في الدنيا والآخرة .    الذين يعتقدون خلاف هذا الاعتقاد في أمهات المؤمنين هم :

أهل السنة والجماعة                
الرافضة

الخوارج
8
سئل هشام بن حسان وهو في الطواف ما كان الحسن tيقول في الإيمان ؟ قال : قول وعمل  .. هذا القول يوافق قول :

المرجئة

الخوارج
أهل السنة والجماعة
9
قال ابن عباسy: ما عندي من تفسير القرآن فهو عن علي بن أبي طالبt . (تفسير التسهيل لعلوم التنزيل لابن جزي).         يدل هذا القول على :
غزارة علم علي t

مخالفة ابن عباس لعلي y

جميع ماسبق
10
قال ابن عباس y : (تكفل الله لمن قـرأ القرآن وعمـل بما فيه أن لا يضـــل في الدنيا ولا يشــقى في الآخرة ) وقرأ قوله I : (فَإِمَّا يَأْتِيَنَّكُم مِّنِّي هُدًى فَمَنِ اتَّبَعَ هُدَايَ فَلَا يَضِلُّ وَلَا يَشْقَىٰ(123) وَمَنْ أَعْرَضَ عَن ذِكْرِي فَإِنَّ لَهُ مَعِيشَةً ضَنكًا )  يدل مثل هذا التوجيه على :
البدع نتيجة البعد عن القرآن والسنة

بعد أهل السنة والجماعة عن مصادر التلقي  

كل ما سبق


11
قال حذيفة بن اليمان t: يا معشر القراء استقيموا وخذوا طريق من كان قبلكم فو الله لئن اتبعتموهم لقد سبقتم سبقا بعيدا ، ولئن أخذتم يمينا وشمالا لقد ظللتم ضلالا بعيدا .  هذا الأثر المراد به اتباع طريقة ومنهج :
الصحابة y

الزعماء

القراء
12
(الْيَوْمَ أَكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُمْ وَأَتْمَمْتُ عَلَيْكُمْ نِعْمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ الْإِسْلَامَ دِينًا) قـــال ابن عباس y: أخبر الله نبيه والمؤمنين أنه قد أكمل لهم الإيمان ولا يحتاجون إلى زيادة أبدا .     يدل هذا على:

جهود الصحابة وآل البيتy في الذب عن منهج السنة

أن ما لم يكن حين نزول الوحي دينا فليس اليوم بدين
كل ما سبق 
13
قوله I)يوْمَ تَبْيَضُّ وُجُوهٌ وَتَسْوَدُّ وُجُوهٌ) فأما الذين ابيضت وجوههم : فأهل السنة والجماعة وأولو العلم ، وأما الذين اسودت وجوههم : فأهل البدع والضلالة ، هذا المعنى ورد عن :
عبد الله بن عباس t

أبوبكر الصديقt

عائشة رضي الله عنها  
14
قال عبدالله بن مسعود t" اتبعوا ولا تبتدعوا فقد كُفيتم "  يدلقوله tعلى :

وجوب اتباع منهج الكتاب والسنة

التحذير من البدع             
جميع ماسبق
15
حذر الحسن t من أهل الأهواء فقال " لا تجالسوا أهل الأهواء ولا تجادلوهم ولا تسمعوا منهم " ..مِن أهل الأهواء :

أهل السنة والجماعة
الرافضة

جميع ماسبق
16
عن أبي بن كعب tقال : ( عليكم بالسبيل والسنة فإنه ما على الأرض عبد على السبيل والسنة وذكر الرحمن ففاضت عيناه من خشية الله عز وجل فيعذبه ... )  يستفاد من هذا الأثر

آثار اتباع السنة

أن سبيل السنة هو سبيل النجاة
جميع ماسبق
17
قال الحسن t: (  لا يصح القول إلا بالعمل ولا يصح العمل إلا بنية ولا يصح قول وعمل ونية إلا بالسنة  )  يستفاد من هذا الأثر :

الاكتفاء بالنية

الاكتفاء بالعمل 
أهمية الاتباع للسنة  
18
قال عمر t وروي ذلك أيضا عن علي t: ( سيأتي أناس يجادلونكم فخذوهم بالسنن فإن أصحاب السنن أعلم بكتاب الله )   يستفاد من الأثر في :
منهجية  الرد على المخالف

النهي عن مجادلة أهل البدع

مخالفة عمر لعلي
19
روى البخاري حديث أبي هريرةt قال: قال رسول الله r ((ستكون فتن القاعد فيها خير من القائم، والقائم خير من الماشي، والماشي فيها خير من الساعي، من تشرف لها تستشرفه))يدل هذا الحديث على :

مواجهة الفتن والمشاركة فيها
اعتزال الفتن وعدم الخوض فيها

الحرص على الفتن والمشي إليها
20
قال الرسول rفي معرض حديثه :(فعليكم بسنتي وسنة الخلفاء الراشدين المهديين من بعدي ، عضوا عليها بالنواجذ وإياكم ومحدثات الأمور فإن كل بدعة ضلالة)     يدل هذا الحديث على :

فضل الخلفاء الراشدين

التحذير من المحدثات في الدين
كل ما سبق