Thursday 27 April 2017

Koken al'ummar Garin Ketare ga Gwamnati

Sako zuwa ga mahukuntan Jihar Katsina
Daga al'ummar garin Ketare (karamar hukumar
Kankara)
Wani mummunan fasadi ake aikatawa tsawan
watani 3 a garin Ketare da wasu kauyuka a kusa
da shi, mutan garin sunyi bakin kokarin su amma
kasancewar tsageran sun samu goyon baya
kwaran gaske. Na samu wannan koken a satin
nan kuma na bincika na tabbatar da abubuwan
da koken ya kunsa.
Ga koken nan
"Assalamu ailaikum muna Mika koke da neman
taimako domin tada yan kungiyar gala/solo da
aka kawo mana a garin ketare Kuma aka yi masu
masauki a asibitin dake garin ketare kimanin
Wata hudu (4) kenan. Zuwan wadannan yan gala
ya haifar mana da matsaloli kamar haka. Lalata
tarbiya malali. 1. Irin abinda Ke faruwa a
Makarantar primary ta garin ketare Inda aka sami
yara maza da mata suna kwaikwayon irin abinda
yan kungiyar keyi Inda maza Ke hawan kan mata
har ma wani Yaron yana cewa Wata tazo Yayi
mata ciki Wannan ya ya faru Ranar 24/3/2017.
2. Kiran junansu da sunayen batsa irin na yan
kungiyar kamar irinsu kankana uwar ruwa da
sauran su..... 3. Barazanar tsaro wanda abaya
mun sami sauqi Amma yanzu kullum sai ansami
Inda akayi sata a garin
4. Keta haddi da bautar da kananan yara ,mafi
yawan yan matan da ake amfani dasu a wajan da
kadan suka wuce shekara goma . 5.bijirewar da
ya'ya' Ke yima iyayensu.
6. Barazana ta bangaren lapia tsoron yaduwar
cututtukan zamani. Dukkan su sunsabama
dokokin addinin musulunchi da Kuma dokokin
jihar katsina da Al adun muzauna garin
Mun gabatar da wadannan matsaloli a gaban
kwamitin tsaro na karamar hukumar Kankara
Ranar 6/04/2017 Inda kwamitin tsaron ya kasa
dakatar dasu saboda furucin da Magaji dogari
Yayi nacewar Idan aka tadasu to za ayi Bala'i
Inda yasami goyon bayan Staff Officer Kankara
Local Government lmrana dake da awar yana da
daurin gindi a wajan gwamna. Ta dalilin haka
kungiyar ta yadu a garuruwa kamar Ketare da
Burdugau da Kuma Sabon Layi Kuma Suna
samun kariya Daga yan sandan karamar hukumar
Kankara"
Wannan shine koken al'ummar wannan gari.
Akwai hotuna masu motsi na yadda wadanan yan
Galar suke kwana suna kade-kade mazansu da
matansu har gari ya waye.
Daga karshe muna kira ga gwamnatin wannan
jiha da ta dubi girman Allah da ta dau mataki na
gaugawa domin ceto al'ummar wannan yankin.
Haka kuma muna kira da babbar murya da
babbar murya ga wannan gwamnati da tayi
kokarin kafa kungiyar Hisba domin lura da irin
wadanan matsaltsalu.

Hussain Kabir Yaradua
27/04/17

Wednesday 5 April 2017

Jami'ar Al-Qalam ta tallafa ma yan gudun hijira a karo na biyu

Jami'ar musulunci ta Al-Qalam dake Katsina ta qara tallafa ma yan gudun hijira mazauna jihar ta Katsina a jiya Talata 04/04/17. Shugaban Jami'ar Prof Shehu Ado Garki ne ya hannanta kayan ga kungiyar mata masu da'awa wato Da'awah Family Support Katsina wanda ke kula da yan gudun hijirar, Shugaban jami'ar  ya bayyana cewa wannan shine karo na biyu da suka bada irin wannan tallafi,  kayayyakin da aka bada tallafin sun hada da Buhun masara guda 6, sai buhun gero guda 1, sai  buhun shinkafa guda 5, kwalin supergetti guda 7, Jarkokin mai guda 3.
A garin Katsina akwai yan gudun hijira wanda aqalla sun haura mutum 800 wanda qungiyar Da'awah Family Support ke kula da cin su da shansu, mazaunin su da suturarsu da kuma maganinsu DSS. duk wannan qungiya ke kula da su. Kamar yadda Malama Asiya shugaban kwamitin Idps ta kungiyar ta bayyana. Taron bada tallafin ya samu halartar mataimakin shugaban jami'ar Dr. Muhd Muslim Ibrahim, Rajistra, Bursar, Mustapha Audu Radda (P.R.O) da sauran muqaraban jami'ar, daga bangaren Da'awah Family support kuma Akwai Malama Asiya da kuma uwar kungiyar Da'awah Family Support Haj. Amina Ahmad Bawa Faskari, Husain Kabir Yaradua sai kuma Hasan Kabir Yaradua. Daga qarshe muna kira ga al'ummar jihar Katsina musamman masu hannu da shuni da su yi koyi da wannan jami'a wajan taimaka ma yan gudun hijira wanda Duke cikin wani irin mawuyacin hali wanda ta kai wasun su har sun fara bara. Allah ya agaza masu ya kuma bamu ikon taimakawa.

Hasan Kabir Yaradua

05/04/17.