CACAR NAIJA BET A JIHAR KATSINA
GWAMNATI
YA KAMATA A TABBATAR DA DOKAR
HARAMTATA
Watanni
kusan biyar da su ka gabata na so in yi rubutu kan wannan cacar, to amman
kasancewar banda masaniya kan yadda ake yin cacar ya sa nai shiru, amman yanzun
na samu bayani kan ta da kuma irin illarta ga al'umma.
Kamar
yadda na nemi wani dan uwa yayi min bayaninta to ga amsar shi nan.
Mal
Hassan ita naija bet wata caca ce da ta shafi wasanni musamman kwallon kafa da
makamantanta. Wadda ada kake ganin wadanda ba musulmaiba a sabon layi suke da
shaguna. Abinda akeyi shine zaka sa ka kudin akan dan wasa ko club kokuma coach
bisa ga abinda zai faru ga wasan, kowanne akwati akwai adadin kudinsa sannan
akwai farashin biya da zakayi idan kayi nasara kaci idan bakayi nasara ba
shikenan. Idan kana kallon ball zakaga manyan turawa saman high table a
stadiums ana yawan haskosu to sune jigajugan. Kuma ayqnzu anzamantar da abin
sabanin da ta yadda zaka iya yi a internet kokuma zuwa shagonsu dake kusa da
mutum yayanki kati kuma za'a shigar da mutum amatakin jiha ko kasa bakidaya.
Akwai bet mai farashi tun daga N100 har zuwa wuce haka. Suna cewa ko nawa mutum
yaci take zaiga kudinsa. Atakaice dai caca ce ta nejaful wadda muka sani abaya.
Kuma ta shafi sanya kudi, wanda awani lokaci za'a baiwa mutum zabi na cewa
akwai wasa tsakanin wane da wane ko club kaza da kaza. Sai akawo akwati kaza
mai lamba kaza cewar club kaza zasu kaza wannan ma kaza zasu ci kaza. Kuma
kowanne akwai kudinda mutum zai zuba. Kuma antsara hakan ganin kwallo ce tafi
tasiri ga matasa.
MAJALISSAR DOKOKIN JIHAR KATSINA
Kwanan baya majalissa ta
sanya doka kan wannan caca. Muna fatan zasu tabbatar da dokar haramta ta.
Hassan Kabir Yaradua 22/05/2018