Tuesday 22 May 2018

CACAR NAIJA BET A JIHAR KATSINA GWAMNATI YA KAMATA A TABBATAR DA DOKAR HARAMTATA



CACAR NAIJA BET A JIHAR KATSINA GWAMNATI
YA KAMATA A TABBATAR DA DOKAR HARAMTATA
Watanni kusan biyar da su ka gabata na so in yi rubutu kan wannan cacar, to amman kasancewar banda masaniya kan yadda ake yin cacar ya sa nai shiru, amman yanzun na samu bayani kan ta da kuma irin illarta ga al'umma.

Kamar yadda na nemi wani dan uwa yayi min bayaninta to ga amsar shi nan.

Mal Hassan ita naija bet wata caca ce da ta shafi wasanni musamman kwallon kafa da makamantanta. Wadda ada kake ganin wadanda ba musulmaiba a sabon layi suke da shaguna. Abinda akeyi shine zaka sa ka kudin akan dan wasa ko club kokuma coach bisa ga abinda zai faru ga wasan, kowanne akwati akwai adadin kudinsa sannan akwai farashin biya da zakayi idan kayi nasara kaci idan bakayi nasara ba shikenan. Idan kana kallon ball zakaga manyan turawa saman high table a stadiums ana yawan haskosu to sune jigajugan. Kuma ayqnzu anzamantar da abin sabanin da ta yadda zaka iya yi a internet kokuma zuwa shagonsu dake kusa da mutum yayanki kati kuma za'a shigar da mutum amatakin jiha ko kasa bakidaya. Akwai bet mai farashi tun daga N100 har zuwa wuce haka. Suna cewa ko nawa mutum yaci take zaiga kudinsa. Atakaice dai caca ce ta nejaful wadda muka sani abaya. Kuma ta shafi sanya kudi, wanda awani lokaci za'a baiwa mutum zabi na cewa akwai wasa tsakanin wane da wane ko club kaza da kaza. Sai akawo akwati kaza mai lamba kaza cewar club kaza zasu kaza wannan ma kaza zasu ci kaza. Kuma kowanne akwai kudinda mutum zai zuba. Kuma antsara hakan ganin kwallo ce tafi tasiri ga matasa. 

 

MAJALISSAR DOKOKIN JIHAR KATSINA 

Kwanan baya majalissa ta sanya doka kan wannan caca. Muna fatan zasu tabbatar da dokar haramta ta. Hassan Kabir Yaradua 22/05/2018

No comments:

Post a Comment