Wednesday 11 October 2017

GWAMNATIN JIHAR KATSINA NA SHIRIN BADA TALLAFIN KARATU A ISLAMIC ONLINE UNIVERSITY (IOU)
A wata zantawa da mai Girma Gwamnan Jihar katsina R.t Hon Alh Aminu Bello Masari yayi da Shugaban Jami’ar Shaharraran mai wa’azin addinai Dr. Bilal Phillips a lokacin da ya kai masa ziyarar Girmamawa a gidan Gwamnatin Jihar a ranar Alhamis 5 ga watan octoba, Shahararen Malamin ya gabatar da Jami’ar da yadda tsarin karatunta ya ke gudana. Wanda daga bisani Gwamnan jihar Katsina ya umurci mai bashi shawara kan harkar ilimin gaba da sakandire da ya tabbatar an bi hanyoyin da ya kamata don a samarwa al’umma guraben karatu a jami’ar. Dakta Bilal Philips ya zo garin Katsina ne don gudanar da Taron tunatarwa na kwana daya wanda Kungiyar Islamic Preaching and Public Services tare da hadin gwuwar HK Yaradua Islamic media su ka shirya taron mai taken ‘’Zaman lafiya da Bin Doka da Oda ga al’umma’’ taron wanda ya gudana ranar Juma’a 6/10/2017 a babban filin wasanni na Muhammad Dikko Stadium Katsina, an gudanar da taron cikin nasara wanda akalla sama da mahalarta 6000 ne su ka halarci taron wanda har da mabiya addinin kirista.
Daga cikin wuraren da Malamin ya ziyarta sun hada da Fadar mai-martaba sarkin Katsina Alhaji Abdulmumin Kabir Usman da kuma Jami’ar Al-Qalam University Katsina, Gidan Sheik Yakubu Musa Hassan Katsina (Sautus-Sunnah). Akwai kuma wasu Daliban Online University yan jihar Katsina, kungiyar Da’awah Family Support Katsina,haka nan kuma Kwamitin Masallacin Bilal Bin Rabah Katsina sun kawo ma Daktan Ziyara a masaukinsa.
Muna fatan wannan yunquri da gwamnatin jihar Katsina za tayi ya tabbata. Don wannan ba karamar dama bace ga al'ummar wannan jiha, muna kuma fatan gwamnatin za ta yi tsari na musamman don ganin an amfana da wannan jami'ar ta yanar gizo.
Usman Gambo Filin Samji
11/10/2017