Thursday 15 December 2016

HALIN DA SHI'A TA JEFA QASAR SYRIA

ALLAH KA CECI BAYIN KA NA SYRIA
DAGA  Malam Umar Mansur
Halab! Halab!! Halab!!!
HALAB KAFIN YAQI
Halab Tsohon garine me matuqar girma da muhimmanci ta fuskar tarihi da kasuwanci wanda shine gari na uku mafi girma bayan Istanbul (Qusdandaniyya) da Cairo a zamanin daular Usmaniyya ( othmon empire ).
Garin Halab shine gari mafi girma na biyu a Qasar Siriya wanda yake iyaka da qasar Turkiyya da nisan kilomita 48Km Sannan yana dauke da kimanin mutane miliyan hudu da suke rayuwa a cikinsa. Kamar yadda Jami'ar Halab na daya daga cikin manyan jami'oin qasar siriya me dauke da kimanin dalibai dubu goma sha shida masu karatu a fanni daban daban.
Hakanan Garin na Halab ya shahara da kamfanoni da masana'antun sarrafa auduga, siminti da sauransu wanda hakan yasa yazama daya daga cikin cibiyar hada hadar kasuwanci mafi girma a qasar.
HALAB A YAU !
Hakika duk
abinda zamu naqalto daga abinda mukaji ko muka gani ta kafafen sadarwa wani yanki ne na daga abinda yake faruwa a wannan gari na halab domin an wayi gari YAN SHI'A qarqashin jagorancin Basshar El-Asad da Qungiyoyin hadaka irinsu Iran, Hizbullah na Lebanon, Yan shi'a daga Pakistan, samarin shi'a daga ko ina na duniya tare da Sojojin Rasha karkashin jagorancin PUTIN suna gab da goge sunan halab daga Taswirar duniya(Map) .
An wayi gari saboda irin kisan kiyashi da kisan qare dangi da akeyi a wannan gari ana kimanta wanda suka rage a garin basu wuce mutane dubu dari uku da hamsin ba cikin miliyan hudu. Sannan Labari ya tabbata babu wani asibiti da ya rage a garin duk an rusasu ballantana magani balle ayi maganar likitoci kamar yadda ba a maganar abinci domin qungiyar qawancen yan shi'a qarqashin El-Asad duk sun rusasu sakamakon Harin da suke kaimusu ta sama da ta qasa.
An kama dayawa an kulle a gidan kaso , an azabtar dasu,an yanka na yankawa,an harbe na harbewa, an yi lalata da yara mata a gaban iyayansu sannan a kashesu, an kashe iyaye maza a gaban ya'yansu,anyi lalata da mata a gaban mijinta sannan a kasheta a gabansa ko a kashe miji a gaban matarsa, an kashe jarirai , yara qanana maza da mata, an rusa gidaje, makarantu, masallatai, kasuwanni, asibitoci da masana'antu.
A Yau ta kai a halab yara mata roqon iyayansu sukeyi su kashesu ko su duro daga saman bene su mutu dan kada ayi lalata dasu sannan a kashesu kisan wulakanci wanda akan hakan har fatawa suke nema.
A cikin Mako biyunnan da suka gabata an kashe sama da mutane dubu uku banda wanda suka ji ciwo da kuma wanda suka mace basu a raye basu a mace. Masu kisan nan fa duniya tasansu kuma tasan ko su waye kuma ta san dan me suke kisan amma dayake AHLUS SUNNAH ake kashewa kamar anyi ruwa an dauke babu maganar Human rights. Sannan duk wanda ya karanta Tarihi ze fahimci Jumhuriyar Iran ta yanzu Qoqari takeyi tayi abinda Kakansu SHAH -ISMAIL yayi bayan kafa daular Safawiyyun ta fuskar yada shi'anci takowace irin hanya shiyasa duk wani bala'i da wata fitina dake faruwa a duniyar musulunci a yanzu se kaga da sa hannun Iran a ciki kuma wallahi Tallahi lamarin nan kamar yadda malamina Dr Umar Mansur ya fadane a yau yan shi'a da zasu sami dama a ko ina toh zasuyi mafiyin abinda sukeyi yanzu haka a Halab. A don Haka Wallahi mudaina jin tausayin yan shi'a ko abinda aka musu a Najeriya domin in mukai sakaci ko wauta zamu zama nama a wajen mayunwaciyar kura ,Allah ya tsare.
Muna Roqon Allah ya kawoma yanuwanmu na Halab dauki na gaggawa kamar yadda muke roqansa da ya maida kaidin makirai akansu a duk inda suke.
Via Prince Farhanul Khair
Bursa/Turkey
15/12/2016

Sunday 11 December 2016

NIGERIAN PEACE CORPS DA AL’UMMAR JIHAR KATSINA

NIGERIAN PEACE CORPS DA AL’UMMAR JIHAR
KATSINA
Kamar yadda mu ka ji kuma mu ka gani cewa
Mahukuntan Nigeria sun gabatar da qudurin su
na sanya wannan hukuma a cikin jerin
hukumomin tsaro na kasar Nigeria. Wannan yazo
a daidai lokacin da matasan kasar ke cikin halin
rashin aikin yi wadda samun damar kan ceci
matasa da yawa a wannan Kasa. Kusan ka iya
cewa jahohi da dama sun yi maraba da wannan
yunkurin na daukar ‘yan peace corps musamman
yadda ‘yan peace corps din suka dade suna ma
kungiyar hidima tsawon shekaru biyar, amman
ban da jiha ta Katsina inda wasu mutane ke ma
‘yan kungiyar kallon mayaudara, kusan kwana
biyar da su ka gabata dan uwa na Husain
Kyar'adua ya yi rubutu don ya bayyana ma
al’ummar jihar Katsina halin da ake ciki a jihar
dangane da kungiyar da kuma kokarin da
Kwamandan su yake na ganin ya ba Katsinawa
hakkinsu. A cikin rubutun nashi wasu masu ganin
cewa su sun waye da kafofin yada labarai na
zamani su kai ta maganganu wadanda za su sa
shakku musamman ga masu sha’awar shiga
kungiyar wanda ga alama basu san komi ba
game da batun.
HALIN DA KUNGIYAR TA KE CIKI A KATSINA
A wajan shekarar 2012 ne kungiyar ta bayyana a
jihar Katsina inda mafi akasarin wadanda su kai
rijista da kungiyar matakin karatun su bai wuce
na Sakandire ba, hakan ne ma yasa mutane
masu zurfin karatu su ka rena aikin suke masu
izgili kala-kala, ban mantawa akwai jajirtattu a
cikin ‘yan Peace corps din wadanda su kai ta
kokarin samar ma kungiyar gindin zama a
wannan jiha wanda karshe wasun su har
makarantun sakandire su kai balantiya suna
zuwa don rage ma malamai aiki, wannan kadan
ne daga jajircewarsu. To abun mamaki wanda
anan gaba zai iya kawo ma tsaffin ‘yan kungiyar
matsala shine rashin samun masu karatu mai
zurfi wadanda za su zama shuwagabanni a
matakin jiha da kasa wanda yanzun maganar da
ake adadin mutane 4000 ne aka ce an ba jihar
amman har yanzun basu samu mutane 500 ‘yan
asalin jihar wadanda su kai rijista ba,ranar
alhamis din da sukai rally akalla wadanda ba 'yan
jihar Katsina ba kusan mutum dari wadanda
galibin su graduate ne su ka zo sukai rijista a
quota Katsina. wannan na gwada cewa karshe
dole a cike gurbin su da ‘yan wasu jihohi
wadanda su ka dau abun da muhimmanci wanda
har an fara hakan.
Kan haka ne Hussain ya so ya jawo hankalin
al’umma cewa ayi himma wajan shiga aikin kada
ace wai sai Shugaban Kasa yasa hannu sannan
za a yi don a lokacin zai iya zama sai mai hanya,
ko kuma mu komo muna cizon yatsa muna zagin
wasu cewa sun kawo mutanen jihar su. Karamin
misali anan NPower ga kuma Civil Defense
wadanda aka rika ce masu kafi banga.
Kira naga al’umma shine mu yi kokari mu shiga
aikin nan don cike gurabun da aka tanadar ma
jihar. Sannan daga karshe ina kira ga duk mai iko
kan tallafa ma matasan jihar, to ga dama ta
samu ta taimakon rayuwar matasa.
An ruwaito cewa a Kano gwamnan su ya biya ma
mutum 2000 kudin shiga haka ma a jihar Yobe ya
biya ma mutum 3000. Mu kuma a jihar mu a na
tai masu yarfe.
ALLAH YA SA AL'UMMAR MU SU FARKA
Hasan Kabir Yaradua ( Hk Yaradua )
11/12/2016

Sunday 20 November 2016

Gangamin Tallafin Yan Gudun Hijira

#GANGAMINTALLAFINIDPS: GARABASA TA SAMU - HANYAR RAHMA KAI TSAYE! 
الراحمون يرحمهم الرحمان ارحموا من فى الأرض يرحمكم من فى السماء
Masu tausayi, Allah Mai Rahma Ya na tausaya ma su. Ku tausayawa bayin Allah a bayan Kasa, sai Allah Mai Rahma da ke Sama Ya yi maku Rahma!
1. SHIN KUN SAN HALIN DA YAN GUDUN HIJIRA KE CIKI A BORNO A YANZU?
Daure ku biyo mu domin ziyarar gani da ido a wurare daban-dabam na 'yan Gudun hijira a Jihar Borno.

2. Ko kun San cewa Al'ummar Musulmin Jihar Kano sun aika Tallafin gaggawa na Trailer 10 ta abinci da Tufafi da qimarsu ta fi #200,000,000 (Naira Miliyan Dari Biyu) kuma mun je mun raba hannu da hannu ga wadanda suka cancanta? 

3. Ko Allah Ya sa kuna cikin wadanda suka tallafa da Abinci ko Tufafi ko kudi don wannan aikin?
Ku biyo mu a shafinmu na facebook don ganin hotuna da videos na Al'ummar da muka kai wa tallafin da yanda muka damka amanar da kuka dora mana.

4. Ko ka yi shirin fara bada tallafinka na akalla N1,000 a wata don ceto wadannan bayin Allah daga yunwa da CUTUTTUKA?
Ka na iya turowa kai tsaye ta wadannan lambobin account:
JAIZ BANK 000 0024 550 ko StanbicIBTC 000 123 6900
Sunan Account: Council of Ulama Kano

5. Shin kun shirya bada gudunmawar ku ta wasu hanyoyi daban dabam?
Ku tuntu6e mu kai tsaye:
    A. Dr Said Ahmad Dukawa (0701 211 9622) or
   B. Engr  Basheer Adamu Aliyu (0815 738 3838)

6. Shaitan ya hana ka yin wadancan duka? 
Kar ka bari ya hana ka aikawa da wannan sakon ta hanyar facebook ko whatsapp da sauran su.
Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam ya ce "duk wanda ya yi nuni ga alheri zai samu lada kamar wanda ya aikata alherin."

Sunday 30 October 2016

Abubuwan Da Yariman Saudiya Yayi Kafin Rataye shi

Abubuwan Da Yariman Saudiya  Yayi Kafin  Rataye Shi-- Darasi Ga Kowa

Ismai'l Karatu Abdullahi

Kasar Saudiya, kasacewarta ta yi ƙaurin suna a duniya kan gudanar da hukuncinta kan gaskiya ga duk wanda ya aikata abunda bai dace ba, tana hukunci ne daidai da abunda ya aikata. Kutunan Saudiya masu adalci ne, basu bambamtawa wajen zartar da hukunci.

Wani abun misali ya faru a ranar 18 ga watan Oktoban shekara ta 2016,  inda aka rataye wani basarake ta dalilin kashe wani ɗan Saudiya mazauni ƙasar.

Yariman mai suna Turki Bin Saud Bin Turki Bin Saud Al Kabeer, an rataye shi. An yi masa haka ne daidai da abunda ya aikata kamar yadda dokan ƙasarsu ya kasance.

Yariman, mintuna kaɗan kafin a rataye shi, yayi wasu abubuwa  waɗanda za su kasance darasi a gare mu.

Ga kamar yadda ya yi: An Kashe Saud Bin Turki ne bisa kisan gilla da yayi wa wani- Adalci ga Kowa.

Mintuna kaɗan kafin rataye shi, ya nemi a bar shi ya gana da iyalanshi, kuma ya samu. Ya ɗauki kimanin awanni 4 tare da iyayensa da danginsa,  ba sai an yi bayanin abunda ya gudana ba kowa zai iya sani kamar yin ban kwana, ƙarfafa masa zunciya da neman gafara.

Daga bisani sai Limamin Masallacin Al Safa ya ce a ɗauko shi daga ganawar da iyalinsa waɗanda suka ta kiran sunanshi suna bankwana , babu abunda za ta ji sai kuka da alamun baƙin ciki. 

Muhammad Al Maslookhi ne ya watsa a shafinsa na "Twitter", Su kuma Shafin Saudi "News site Al Marsad", suka ruwaito.

Masu rataya suka ɗauke shi zuwa ofishin 'yan sanda inda nan ne zai rubuta wasiyarsa ta ƙarshe, amma bai iya rubutawa ba.

Da misalin karfe 11 na safe, iyalan wanda  Yariman ya kashe, suka iso inda aka sanar da su za a rataye ahi.

Yariman, yayi alwala, sannan ya jira lokacin da za a rataye shi.

Babba wansa, yayi ƙoƙarin magana da iyalin wanda  Yariman ya kashe   domin nema wa ƙaninsa gafara, da kuma ko zasu karɓi diyya, a yinkuri na karshe kafin a rataye Yariman amma sun ƙi yarda.

Bayan sallar Azahar, 'yan'uwan Yariman suka sake neman wannan alfarman daga iyayen waɗanda aka kashe amma sun ƙi amincewa.
    
Kamar yadda kuka sani musulunci ba addini ba ne mai danne hakkin kowa ba. Kamar yadda 'yan'uwan Yarima suka nemi iyalan wanda Yarima ya kashe da su karɓi diyya amma suka ƙi, don haka dole a zartar wa Yariman hukunci daidai da abunda ya aikata.

Yarima yayi sallar Azahar da La'asar. Bayan nan da karfe 4:13  aka rataye shi. Har aka rataye shi, babu abinda ya ke fitowa daga bakinshi sai karatun Alkur'ani da ambaton neman yafiya ga Allah.

Kar ku manta, an rataye Yariman ne sakamakon kashe wani da yayi da bindiga.

Addu'armu Allah Ya gafarta wa wanda aka kashe da shi da yayi kashin.

©Zuma Times Hausa

SHUGABA BUHARI YA YI ALLAH WA'AZI DA HARIN YAN SHI'A A DAKIN ALLAH

Shugaba Buhari ya yi Allah-wadai da harin 'yan shi'a a kan Dakin Allah.

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da harin da aka kai da makami mai linzami kan garin Makkah. Kanfanin Dillacin Labarai na Qasa mai Tsarki, Saudi Press Agency (SPA) ya ruwaito cewa Shugaba Buhari ya kira Sarki Salmanu dan AbdulAziz Alu Sa'ud, inda bayan ya jajanta masa mugun nufin da aka nufi garin na Makkah, ya yi addu'ar Allah Ya ci gaba da tsare garin Makkah da TsarewarSa da dukan Musulmi.

Shi ma Sarki Salman ya roqi Allah Ya taimaki Nigeria Ya kaita ga cin nasara, Ya kuma kareta daga sharrin maqiya.

http://spa.gov.sa/1553765

Haqiqa wannan waya ta Buhari ta qara nuna irin qaunar da Baban ya ke da ita ga Dakin Allah da ma Qasa mai Tsarki.

Allah Ya taimaki Baba Buhari Ya tsare shi da TsarewarSa. Allah Ya tozarta duk masu yunqirin cutar da DakinSa Ya hana musu biyan buqata.

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=1599634673396214&id=100000490902329&ref=bookmarks

Saturday 29 October 2016

Friday 28 October 2016

WA'AZIN WALIMAR AURE

WA'AZI DA WALIMAR AURE NA GIDAN SHEIK HABIBU YAHYA KAURA
DAGA CIKIN MALAMAI
1. Sheik Abdullahi Bala Lau
2. Sheik Kabir Gombe
idan Allah ya kai mu gobe Katsinawa za su sha WA'AZI daga Manyan Malamai na Jibwis ta kasa
Wa'azin zai gudana gobe ASABAR 29/10/16 a Masalacin Kerau,  Bayan Sallar Isha'i.
Mai masaukin Baki Sheik Yakubu Musa Katsina

Thursday 27 October 2016

DON MATASA

​​SHIRIN DON MATASA​

​DA'AWAH ​​​FAMILY SUPPORT ASSOCIATION​​​​

Na farin cikin gayyatar matasa Maza/Mata zuwa shiri na musamman da ta shirya kamar haka
A dakin taro na Social Dev, Filin Samji Katsinah,  A gobe Juma'a 28/10/16 da misalin karfe 3:00 pm

*​​​​YA KU MATASA KAR KU BARI A BAKU LABARI​​​*

​​​​​​MUNA MAKU MARABA​​​​​​

Wednesday 26 October 2016

Na Ga ‘Mutuwa’ A Ranar Tunawa Da Shahadar Husaini (R.A) (3)

Dr. . Muhd Sani Rijiyar Lemo
Na Ga ‘Mutuwa’ A Ranar Tunawa Da Shahadar Husaini (R.A) (3)

Assalamu Alaikum,
A baya mun ji yadda Marubucinmu da abokan
tafiyarsa suka auka cikin wani kango wanda
waɗansu gungun mutane suke zaune cikinsa, ana
rera musu waƙe suna amshi. To mai ya faru
bayan shigarsu. As-Sheikh Ali at-Tantawi ya ci
gaba da cewa,
“Muka tsallaka sahu-sahu muka shiga. Jama’a na
zazzaune, duk sun yi shiru, kamar mutuwa ta
gitta, bayan da shi mawaƙin ya yi shiru, da alama
dai hutawa suke yi kafin su ci gaba.
Mun kutsa ciki ne har sai da muka isa sahun
farko inda mai bayar da waƙe yake bayarwa.
Yana zaune a kan kujera, a gefe da shi akwai
wasu ƙarin kujeru waɗanda babu kowa a kansu,
sai aka ba mu muka zauna. Ba da jimawa ba aka
ci gaba da rera waƙe. Duk sa’adda mawaƙin ya
rera wasu baitoci sai ya ɗan dakata kaɗan, can
sai ka ga su kuma sauran jama’ar sun ɗaga
hannuwansu sama sun tattake sun bugi ƙirajesu
da su, ji kake wani jib!! kamar katangar wannan
kango tana motsawa saboda ƙarar wannan bugun
ƙirji da suka yi. Sannan ya sake rera wasu
baitocin, su kuma su sake jibga hannuwansu a
kan ƙirajensu, har sai da ƙirajensu suka yi ja jawur
saboda tsananin duka, gumi ya jiƙa su sharkaf.
Kowa a cikinsu yana cike da baƙin-ciki da jimami
na abin da aka yi wa Husaini (R.A), zuciyarsa
kuma ta cika da gaba da ƙiyayya ga Banu
Umayya da mutanen Sham, waɗanda wannan
waƙen ya ɗorawa alhakin jinin Husaini (R.A).
Ana tsakar haka ne, sai kawai ɗaya daga cikin
ɗaliban da muke tare da su, allurar kirkinsa ta
motsa, sai ya mike tsaye wai zai gabatar da ni a
wajen wannan mawaƙi don ya nuna masa irin
ƙaunarsa gare ni, tare da fada masa girman
matsayina da martaba ta a gurinsu. Sai jin shi na
yi yana faɗawa maƙin nan cewa, ‘Wannan babban
malaminmu ne, kuma mutumin ƙasar Sham ne,
sannan kuma babban marubuci ne, ya yi wallafe-
wallafe dadama, a cikin littattafansa da akwai
littafinsa ma mai suna ‘Abubakar As-Siddiq’, da
kuma wani mai suna ‘Umar bn Alkhattab’, da …
da…” ya ci gaba da lissafa su. Ina!! Ai ban gama
jin ƙarshen maganarsa ba, sai kawai na shiga yin
kalmar shahada, don ta zama mini ita ce ƙarshen
maganata a zamana na duniya.
Ban sake fahimtar abin da wannan ɗalibi nawa
yake faɗa wa wannan mawaƙi ba, domin zuciyata
tini ta ɓallo ta faɗo ƙasan cikina, kamar yadda
kasan irin yadda ‘lifter’ take faɗowa daga dogon
bene yayin da sarƙoƙin dake ɗauke da ita suka
tsinke. Kawai ni a lokcin na saddaƙar mutuwa zan
yi. Na juya ina ta dube-dube ko zan ga maguda,
amma ina! Wuri ya cika maƙil, ga katanga ta
kewaye ko ina, babu mafita sai wannan ƙofar
ɗaya da muka shigo daga gare ta, tsakanina ko
da ita ban da waɗannan mutane masu kirji a
waje ba abin da nake gani. Sannan me kake
zaton zai faru idan mutanen nan suka gane
cewa, ni mutumin Sham ne?! Kuma ni ne
mawallafin littfin tarihin Abubakar da Umar?! Ta
yaya zan yi in tabbatar musu cewa, babu
hannuna a cikin kashe Husaini?! Kuma babu
hannun kakanni na a ciki, saboda su ‘yan asalin
ƙasar Masar ne, ba mutanen Sham ba ne?! Don
haka su fahimci babu hannuwansu a kashe
Husaini. Wai ma tukunna ma za su ba ni damar
in kare kaina ne har da zan musu wannan
bayanin? Kuma ma idan na yi ƙokarin kare kaina,
kuna ga ma za su yarda da ni ne har su gaskata
ni?!
Daga nan kawai na sakankance na gama yawo,
yau sai buzuna, abin da ya rage mini shi ne in ci
gaba da yin addu’a a asirce, idan na zo mutuwa
in yi mutuwa mai sauƙi, amma babu maganar
kubuta.
Shi kuma abokina Anwar fa, mai yake ciki, domin
shi ne ya shigar da mu wannan matsalar. Da na
saci kallosa sai na ga kamanninsa sun canza,
launinsa ya canza kala, ya koma ruwan kalar
lemon tsami. Na kalli fuskar Sayyid mai koren
rawani ko zan fahimci matakin da yake shirin
ɗauka a kain, sai ban fahimci komai daga
wajensa ba, na dai bar al’amarina a wajen Allah.
Muka ɗauki tsawon awanni saba’in a jere cikin
wannan hali na fargaba da firgici da tsoro, babu
wani abu da ya canza. Duk wani minti ɗaya
matsayin awa ɗaya nake ganinsa. Aka ci gaba da
waƙe har aka kai ƙarshe. Can sai na kula mutane
su fara shirin fita, don na ga suna ta ɗauko
rigunansu suna mayarwa jikinsu. To daga nan ne
na fahimci matsalata dai ta zo ƙarshe, hankalina
ya fara dawo wa jikina. Na dubi agogona sai na
ga ashe ba awanni saba’in muka yi ba, mintina
ashirin ne kachal. Tsabar dai tsananin firgicewa
ne kawai ya sanya na ga tsawon lokacin. Daga
nan na yi bankwana da ‘Sayyid’ na nufi ƙofa na
fita. Na ji ni kamar na mutu na dawo Duniya.
Muka kwana biyu a Hillah. Da muka sake haɗuwa
da ‘Sayyid’ muka tattauna, sai na fahimci shi ba
mai tsattsauran ra’ayi ne ba, (ko kuma dai taƙiyya
ya yi min). Sai nake tuna masa abin da ya faru,
sai ya ce, “Ka godewa Allah da ya kuɓutar da
kai, kuma bai bar wannan jama’a sun ji abin da
wannan ɗalibi naka ya fada ba”. Sai na ce, “Ashe
kai ba za ka kare ni ba idan sun so auka min?
Sai ya yi dariya ya ce, “Idan na kare ka, ni kuma
wanene zai kare ni?! Wallahi ba wata kariya da
zan ba ka, zan ƙale ka da su, ka fuskanci
makomarka!’…”.
Wannan shi ne yadda babban marubucinmu
Sheikh Ali At-Tantawi ya tsallake rijiya da baya,
yayin da ya tsinci kansa a tsakiyar ƙatti madaka-
ƙiraza, a Husainiyya ta garin Hilla cikin Ƙasar Iraƙi.
Ya rubuta wannan labari na shi a cikin littafinsa
mai suna ‘Az-Zikrayāt’, juzu’i na 3, shafi na
379-388. Allah ka ganar da su gaskiya. Amin

Tuesday 25 October 2016

Na Ga ‘Mutuwa’ A Ranar Tunawa Da Shahad Husaini (R.A) (2)

  

 Na Ga ‘Mutuwa’ A Ranar Tunawa Da Shahada                            Husaini (R.A) (2)


Dr.Muhd Sani R/Lemu


‘Yan uwana masu karatu, kamar yadda na yi
muku alkawari a baya cewa, zan tsakuro muku
wani abu mai kama da taɓa-ka-lashe daga
cikin rubutun babban marubucin nan Ash-
Sheikh Ali at-Tantawi da ya rubuta ƙarkashin
waccen matashiya ta sama, a littafinsa mai
suna “Az-Zikrayaat” wato ‘Tuna Baya’. Ka da
ku manta na faɗa muku cewa, ba zan iya kawo
rubutunsa yadda yake ba, cike da fasaharsa da
taswirarsa, sai dai in kwatanta, domin an ce,
‘linzami ya fi ƙarfin bakin kaza’.
Malam dai ɗan asalin ƙasar Syria ne, amma ya
yi zaman karatu a Masar, sannan ya koyar a
Iraƙi, ya ziyarci wasu ƙasashe dadama, daga
ƙarshe ya yada zango a ƙasar Saudiya, a nan
Allah ya yi masa rasuwa a shekarar (1999
A.D). A zamansa a Bagadaza ta ƙasar Iraƙi ya
fita wata rana inda ya ga ‘mutuwa’ amma Allah
ya kuɓutar da shi, daga baya ya yi rubutu a
kan wannan labari, inda yake cewa,
“Ranar Ashura a Iraƙi wata rana ce ta daban.
Duk garin yakan koma tamkar ana zaman
makoki, kai ka ce, jiya-jiyan nan ne aka kashe
Husaini (r), ko kuma ka ce har yanzu Banu
Umayya ne ke rike da ragamar mulki; ko kuma
wadanda aka kashe Sayyidina Husaini (r) tare
da su, su ne a kan kujerar mulki. Mutane sun
manta da cewa, Duniyar fa ta canza, wasu
ƙasashe sun gushe, wasu kuma sun kafu,
komai a doron ƙasa ya canza akan yadda da
yake, kaɗai al’adar waɗannan mutane ne ita ce
ba ta canza ba har yanzu, jiya-a-yau.
Mu Musulmi duka muna son Annabi (S.A.W),
duk wanda ma ba ya son shi fiye da yadda
yake son kansa to imaninsa bai cika ba. Kuma
muna son duk mai son Manzon Allah (S.A.W).
Kuma jikokinsa Hasan da Husaini suna son shi,
don haka mu ma muna sonsu, muna son iyalan
gidan Manzon Allah duka, don haka ne ma
muke sa su a cikin salatin da muke yi wa
Annabi (S.A.W). Amma duk da haka ba za mu
taɓa yarda mu aikata abin da Annabi bai yi
umarni da aikata shi ba, don kuwa ba za mu
saɓa masa ba mu riƙa yin gaban-kanmu. Abin
da muka ga wasu mutane a Iraƙi suna yi ya
saɓawa koyarwar Annabi (S.A.W) kuma ba zai
taɓa amincewa da haka ba.
A wannan rana ta Ashura Abokina Anwar ya
buƙaci mu tafi garin Hillah (yanki ne na ‘yan
shi’a a Iraƙi) yawon buɗe ido. Sai na yarda.
Kuma muka nemi wasu ɗalibanmu su uku su yi
mana rakiya. A cikinsu akwai wani basamuden
ɗalibi, idan na tsaya kusa da shi dakyar kaina
yakan gota kwankwasonsa kaɗan, wani lokaci
ma nakan tsokane shi in ce masa, wai kai ba
ka gamuwa da matsalar iskar shaƙa (Oxygen) a
sararin samaniya idan kana tsaye?!. Amma
kuma duk da haka yaro ne mai kirki, mai
kyawawan halaye, sunanshi Abdullahi Adi. Ka ji
sunan shi ma ‘Adi’ kamar sauron ɓurɓushin
Adawa mutanen Annabi Hudu. (A.S). Sauran
ɗaliban guda biyu, ɗayansu ɗan Sunna ne,
gudan kuma ɗan Shi’a ne.
Kashe Sayyidana Husaini wata mummunar
aika-aika ce, e, zan sake maimaitawa,
mummunar aika-aika ce, a fahimci hakan da
kyau. To fa amma da jimawa wasu mawaƙa da
marubuta Adabin larabawa sun yi ta ƙarin
gishiri mai yawa a wajen bayanin wannan
‘aika-aika’ domin sun mayar da ita wani fage
na sukuwar dawakan adabinsu, da sakin
linzamin waƙoƙinsu. Lalle kam sun yi sukuwa
yadda suke so, to amma fa sun lullube gaskiyar
al’amarin da ƙurar sukuwar dawakansu.
Waƙi’ar kashe Husaini, waƙi’a ce da ta faru tun
shekaru masu yawa da suka wuce. Marubuta
iri-iri, kama daga marubutan tarihi da mawaƙa
da marubutan adabi da al’adu kowa ya yi ta
rubutu a kai, kuma kowa yana zana irin tashi
taswirar yadda waƙi’ar ta kasance. Kusan babu
wani labari mai sanya idanu su rika kwararo da
hawaye da ba a faɓa ba a kai. Duk wani abu
da yake nuna zalunci da rashin imani da
ƙeƙashewar zuciya, da nuna rashin mutunci da
tumasanci, duk sai da aka tattaro su aka zuba
su a cikin labarin wannan waƙi’a. Kai yau da a
ce Miyagun mutanen na da aka yi a tarihi irin
su, Nero ko Genghis khan, ko ma yahudawan
da suka fi su sharri a yau irin su Begin da
Shamir, su ne ake ba da labarin an yi musu irin
abin da masu ba da labarin waƙi’ar Karbala
suke faɗa, to babu shakka sai ka tausaya
musu idan ka ji, sai ka jajanta musu a kai. To
kuma balle a faɗa maka cewa, duk wannan
abu ya faru ne ga ‘ya ‘yan Nana Fatima, jikokin.
Ma’aiki (S.A.W) yaya za ka ji a ranka?!
Wannan shi ne zai sa ka fahimci dalilin da ya
sa muke ganin abin da ake yi a ranar Ashura
game da Husaini irin wanda ba a yi wa Ali ko
Mazon Allah kwatankwacinsa, alhali kuwa sun
fi shi daraja nesa ba kusa ba.
Muna tsakar yawo a garin Hillah ne, sai muka
gan mu a wani babban fili an zageye shi da
katanga, da ƙofar shiga guda ɗaya a buɗe.
Sannan muka ji wani sautin rera waƙe mai cike
da tausayi yana fitowa daga cikin wannan
kango. Muna leƙawa sai kawai mu ga wasu
mutane a ciki zaune babu komai na tufafi a
jikisu in banda abin da suka rufe al’aurarsu
zuwa cibiyoyinsu. Sun bar ƙirajensu tsirara a
waje. A tsakiyarsu sai muka hango wani zaune
sanye da koren rawani (alamar shi Sayyid ne
Ahlul Baiti). Wannan mutum shi ne mai ba da
waƙen, sauran jama’ar dake zagaye da shi
sahu-sahu suna masa amshi.
Daga nan sai abokina Anwar ya tambaye ni
cewa, ko za mu shiga wannan kangon ne? Sai
na ce mu tambayi waɗannan ɗaliban domin su
ne ‘yan gari, su suka fi mu sanin ƙasarsu. Sai
suka ce mana kada mu yarda mu shiga. Ai
kafin mu ankara shi gogan naka Anwar har ya
shige. Daga nan muma muka yanke shawarar
mu bi bayansa.
Mu kwana a nan, za mu ci gaba….

Monday 24 October 2016

NA GA 'MUTUWA' A RANAR TUNAWA DA SHAHADAR HUSAINI (R.A)​ Fitowa ta 1

NA GA 'MUTUWA' A RANAR TUNAWA DA SHAHADAR HUSAINI (R.A)
                                
                                                            Fitowa ta 1
✍ Rubutawa:            Dr Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo, Kano



As-Sheikh Ali at-Tantawi kawarren marubuci ne a cikin harshen larabci. Malami ne kuma tsohon Alkali ne, sannan kuma masanin larabci ne. Ya yi rubuce-rubuce masu yawa a fannonin ilimi daban-daban, kamar Tarihi, da Tarbiyya, da Siyasa, da Adabin Larabawa, da zamantakewa da al’adu.
    Ni dai ina matukar sha’awar karanta rubuce-rubucensa, kuma ina jin dadinsu, saboda kasancewa Sheikh Ali wani marubuci ne mai salon rubutu na musamman. Salon maganarsa yana da matukar dadin karantawa, ga shi ya kware sosai wajen sarrafa harshen larabci. Ni dai ban taba ganin marubuci mai iya ba da kwatancen abubuwa ba kamar Sheikh at-Tantawi, gaskiya ya kware a wannan janibin, idan yana maka kwatance kamar me! Sannan baya ga haka at-Tantawi mutum ne mai barkwanci, idan ya yi wata maganar sai ka ga mai karatu shi kadai yana ta dariya ba tare da na kusa da shi ya san dalilin dariyarsa ba. Don haka yake nishadantar da mai karanta littafinsa, idan ya fara karanta littafinsa ba zai so ya bari ba.
    Ina cikin karanta littafinsa ne mai suna “Az-Zikraayat” wato kamar dai ka ce a Hausa ‘Tina Baya’ ko kuma ‘Diary’ da Turanci. Ina tsakiyar karatunsa ne sai kawai na ci karo da wani tubutunsa mai dauke da waccen matashiyar ta sama. Na so a ce duk masu karanta wannan rubutu nawa za su iya karanta wancan rubutu na Sheikh at-Tantawi daga littafin da na ambata a cikin madarar larabcinsa. Saboda a gaskiya ta Allah ba na zaton akwai wani harshe wanda ba na larabci ba da za a fassara wannan makala tashi da shi kuma ya yi daidai da yadda take da larabcinta, a wajen fasaharta da gwanintar sarrafa harshe dake tattare da shi, tare da abin da ta kunsa na fadakarwa da ilimantawa mai yawa.
    Amma duk da haka zan iya tsakuro wa masu karatu dan taba-ka-lashe daga wannan makala ta Malam at-Tantawi. Amma fa ku fahimta fasahata da fasahar yaren da zan yi fassarar da shi, ko kusa ba za a daidaita shi da fasahar Marubucinmu ba da ta yaren Laraci harshen Al-Kura’ni, kuma harshen Annabin tsira, Allah ya kara masa salati da sallama. Amma dai da babu gwamma babu dadi.
Ku saurare ni ina nan tafe da tsakure Insha Allah. Allah ya sa mu dace.


Daga: ​ZAUREN FIQHUS SUNNAH

KARATUN HAUZA DAGA MAJALISIN MAL BABAN HAMDAN


MAJALISI NA [ 1 ] na Sheikh Baban Hamdan


GAMUWA A KAN SAHIHIYAR AQIDA, SHINE RABA-GARDAMA A TSAKANIN MUTANE, SHINE HADIN KAN MUSULMI. SABANIN HAKA, HADIN-BAKI NE DA YAUDARAR JUNA.

MUTUM ZAI ZAMA MUSULMI NE KADAI, IDAN YA QUDURCI:

(1) BA ABIN BAUTA SAI ALLAH SHI KADAI, YA SHAIDA DA MANZANCIN ANNABI MUHAMMAD S.A.A.W.
(2) YA TSAIDA SALLAH
(3) YA AZUMCI WATAN RAMALANA
(4) YA BADA ZAKKA
(5) YAYI AIKIN HAJJI IDAN YA SAMI IKO.

IMANI, SAHIHIYAR AQIDA: SHAIKH SALIHUL FAUZAN, YACE:

وقد بقي النبي صلى الله عليه وسلم في مكة بعد البعثة ثلاثة عشر عامًا يدعو الناس إلى التوحيد، وإصلاح العقيدة؛ لأنها الأساسُ الذي يقوم عليه بناءُ الدين

"TUN DA AKA AIKO SHI, ANNABI S.A.W. YANA MAKKA SHEKARU 13 YANA KIRAN MUTANE ZUWA TAUHIDI DA GYARAN AQIDA, DOMIN ITACE ASASIN DA AKE GINA ADDINI AKAN TA"

A CIKIN LITTAFIN SA "AQIDATUT TAUHID" SHEHI YACE, SAHIHIYAR AQIDA ITACE:

الإيمان بالله وملائكته وكتبه ورسله واليوم الآخر، والإيمان بالقدر خيره وشره، وتُسمَّى هذه أركانُ الإيمان.

"IMANI DA ALLAH, DA MALA'IKUN SA, DA LITTAFAN SA, DA MANZANNIN SA, DA RANAR LAHIRA, IMANI DA QADDARA; AL-KHAIRI DA SHARRIN TA. WADANNAN SU AKE KIRA RUKUNAN IMANI"

'YAN SHI'A, WADANNAN SUNYI MUKU? IDAN SUNYI MUKU, TO KO A CIKIN DAREN NA MA, ZAMU FARA DA KALLON YADDA MUKA QUDURCI WADANNAN RUKUNNAI, TARE DA SANIN MADOGARAR MU AKAN AQIDUN NAMU.

IDAN KUNA DA ABIN DA BAKWA SO A CIKI, KO KU KARA, TO SAIKU LISSAFA SU, SAI SHIGA JERIN ABABEN DA ZAMU TATTAUNA AKAN SU, DOMIN KOWA YA SAN ABIN DA BAI SANI BA, GWARGWADON HALI, YA FAHIMCI ABIN DA BAI FAHIMTA BA.

ALLAH S.W.T. YACE:

واعتصموا بحبل الله جميعاً ولا تفرقوا

BISMILLAH...

MAJALISI NA [2] na Sheikh Baban Hamdan

RUKUNAN DA MUKA GAMU AKAN SU A MAJALISI NA [2], SUNA NAN A QUR'ANI. WANNAN NE; A GANI NA والله أعلم ; YA SA BA MUYI SABANIN WANDA YA SAME SU, SHINE MUSULMI, MUMINI BA.

ANA HAKA NE, SAI MALAMIN SHI'A MAI "ASALUS-SHI'ATI WA USULUHA, 59" MUHAMMAD HUSSAIN KASHIFUL GIDA' YACE:

الشيعة الإمامية زادت ركناً خامساً وهو الاعتقاد بالإمامة

"SHI'A SUN QARA RUKUNI NA BIYAR SHINE QUDURIN IMAMA"

ZA A IYA CEWA RUKUNI NA 6 NE, BA NA BIYAR BA, KO MUCE SUN RAGE RUKUNI DAYA, SAI SUKA QARA DAYA, YA ZAMA NA BIYAR, DOMIN DAMA RUKUNAN DA MUKAYI ITTIFAQI A KANSU BIYAR NE.

KO YAYA DAI, LAMARI NE DA YA HAIFAR DA SABANI, MUSAMMAN BAYAN HUKUNTA WANDA BAI BADA GASKIYA DA SHI BA, KAMAR YA QARYATA MANZANNI NE, WATO DAI, YA FITA DAGA ISLAM.

A "TALKHISUS SHAFIY NA DUWSIY, 4/131" DUWSIN YA CE:

ودفع الإمامة كفر كما أن دفع النبوة كفر لأن الجهل بهما على حد واحد

"YADDA KORE ANNABTA YAKE KAFIRCI, KORE IMAMA MA KAFIRCI NE, HUKUNCIN DAUKE KAI DAGA GARE SU DAYA NE"

WATA MATSALAR ITA CE, MATSAYIN IMAM. HAKANE, DUK WANDA YA YARDA SHI MUSULMI NE, TOH FA, DOLE YA BADA GASKIYA DA DOKACIN ABIN DA ALLAH YAZO MASA DASHI. AMMA ZAI GA ANYI KUDU DA KARE, IDAN YAJI SABON ABU, DA BAI GAMSU ALLAH NE YA HUKUNTA SHI BA.

INA SON A FAHIMCI, GAMSUWA KO RASHIN TA, KAN ALLAH NE YA HUKUNTA IMAMA, DALILI NE DA WANI ZAI QUDURCE TA KO YAYI WATSI DA ITA. KENAN, HANYA DAYA DA ZA A WARWARE SABANIN, ITACE TATTAUNAWA CIKIN LUMANA, DON A GAMSAR DA KOWA "EY KO A'A" BISA KARANTARWAR AL-QUR'ANI.

IMAM KHUMAINIY, CIKIN "AL-HUKUMATUL ISLAMIYYA 52" YACE:

إن من ضرورات مذهبنا أن لأئمتنا مقاماً لا يبلغه ملك مقرب ولا نبي مرسل

"DOLE NE A MAZHABAR MU, A QUDURCI IMAMAN MU SUNA DA WANI MATSAYI DA DUK KUSANCIN MALA'IKA (DA ALLAH) KO WANI MANZO DA AKA TURO, BAI KAI SHI BA"

MUHAMMAD JAWAD MUGNIYA "TAFSIRIN KASHIF 1/197" YA CE:

إن قول الإمام نبياً كان أو وصياً هو قول الله

"LALLAI MAGANAR IMAMI; ANNABI KO WASIYYI; DAI-DAI TAKE DA MAGANAR ALLAH"

MUZAFFAR A "AQA'IDUL IMAMIYYA 70" YACE:

ونعتقد أن الإمام كالنبي

"MUN QUDURCI CEWA IMAMI KAMAR ANNABI NE"

BANBANCIN SU TA FUSKAR WAHAYI NE, KAMAR YADDA KASHIFUL GHIDA' YACE A SHAFI 59:

إن الإمام لا يوحى إليه كالنبي وإنما يتلقى الأحكام منه مع تسديد إلهي

"LALLAI IMAMI BA A YI MASA WAHAYI IRIN NA ANNABI, SHI YANA KARBAR HUKUNCE-HUKUNCE NE TA HANYAR RUHI DAGA ALLAH"

A LURA CEWA WANNAN RUKUNIN DA 'YAN SHI'A SUKA QARA, YA BAYU GA BUDE KOFAR WASU HUKUNCE-HUKUNCE DA IMAMI ZAI KARBO DAGA ALLAH, YA ISAR DASU GA MABIYAN SA.

ASHE BA MATSAYIN AKE JA DASHI BA, AMMA ANA SARA NE ANA DUBAN BAKIN GATARI! ALLAH S.W.T. YA CE:

اليوم أكملت لكم دينكم وأتممت عليكم نعمتي ورضيت لكم الإسلام دينا

"A YAU NA CIKA MUKU ADDININ KU, NA CIKA NI'IMA TA A GARE KU, KUMA NA YARJE MUKU MUSULUNCI A MATSAYIN ADDINI"

KENAN, IDAN WANI YAZO DA WASU HUKUNCE-HUKUNCE SABABBI, DOLE AYI TAKA-TSAN-TSAN, DON KAR A MANTA DA MAGANAR ALLAH, A QOQARIN BIYAYYA GA ALLAH.

A HANU DAYA, ALLAH YA YARJEWA MUTANE MUSULUNCIN DA MUKA FARA DA RUKUNAN SA, GABANIN QARIN RUKUNI NA BIYAR KO NA SHIDA, WATO IMAMA DA 'YAN SHI'A SUKAYI.

TO SAI ABIN YA ZAMA WANI IRI, GASHI MUN DAUKO TAFIYA TARE, TIRYAN-TIRYAN, KAMAR YADDA QUR'ANI YA NUSASH-SHE MU, SAI 'YAN SHI'A SUKA FUTO DA WADANNAN QARE-QAREN, KAMAR YADDA SHI MALAMIN SHI'A KASHIFUL GIDA' YA FADA.

KENAN IDAN ZAMU HADU A KAN QUR'ANI, SAI MU TSAYA GA MUSULUNCIN MUTUM KO KAFIRCIN SA, GWARGWADON RUKUNAN DA QUR'ANI YA TABBATAR.

ME KUKE GANI?

DANGANTAKA DA AURATAYYA TSAKANIN AHALUL BAITI DA SAHABBAI



DANGANTAKA DA AURATAYYA TSAKANIN AHALUL BAITI DA SAHABBAI 

Umar Muhammad Labdo Jami’ar Jihar Kaduna Kaduna Yuni, 2010 ISBN 9683075978 

Abubuwan dake ciki Gabatarwa……………………………………………………………………….. Babi Na Xaya: Ahalul Baiti Da Sahabbai…............................................................ Ma’anar Sahabbai a Wajen Ahalus Sunna……………………………………… Matsayin Sahabbai a Wajen Ahalus Sunna…………………………………….. Fifikon Sahabbai a Junansu……………………………………………………. Haqqin Sahabbai a kan Musulmi……………………………………………… Ma’anar Sahabbai a Wajen ‘Yan Shi’a………………………………………… Matsayin Sahabbai a Wajen ‘Yan Shi’a……………………………………….. Ma’anar Ahalul Baiti a Wajen Ahalus Sunna…………………………………. Matsayin Ahalul Baiti a Wajen Ahalus Sunna………………………………… Ma’anar Ahalul Baiti a Wajen ‘Yan Shi’a……………………………………… Matsayin Ahalul Baiti a Wajen Rafilawa………………………………………. Matsayin Imamai a Wajen ‘Yan Shi’a…………………………………………. Babi Na Biyu: Qarerayin Rafilawa ga Ahalul Baiti da Sahabbai……………… Sahabbai Sun Qwacewa Ali Khilafa…………………………………………… Sahabbai Sun Wulaqanta Faxima……………………………………………… Umar Ya Qwaci Xiyar Ali……………………………………………………... Sahabbai Sun Yaqi Ali………………………………………………………… Maganganun ‘Yan Shi’a Suna Karo Da Juna………………………………… Haqiqanin Alaqar Ahalul Baiti da Sahabbai…………………………………. Babi Na Uku: Dangantaka Da Serekuta Tsakanin Sahabbai da Ahalul Baiti…. Qabilar Quraishawa…………………………………………………………….. Nasaba da Auratayyar Quraishawa…………………………………………….. Nasaba da Auratayyar Annabi(SAW)…………………………………………. Khadija xiyar Khuwailid(RA)…………………………………………………… Sauda xiyar Zam’a(RA)…………………………………………………………. A’isha xiyar Abubakar(RA)…………………………………………………….. Hafsa xiyar Umar(RA)………………………………………………………….. Zainab xiyar Khuzaima(RA)…………………………………………………… Ummu Salma xiyar Abu Umayya(RA)………………………………………… Zainab xiyar Jahash(RA)………………………………………………………. Juwairiyya xiyar Harith(RA)…………………………………………………… Safiyya xiyar Huyayyu(RA)……………………………………………………. Ummu Habiba xiyar Abu Sufyan(RA)………………………………………….. Maimuna xiyar Harith(RA)……………………………………………………… Nasaba da Auratayyar Abubakar Siddiq(RA)…………………………………... Nasaba da Auratayyar Umar binul Khaxxab(RA)……………………………… Nasaba da Auratayyar Usman binu Affan(RA)………………………………… Nasaba da Auratayyar Ali binu Abi Xalib(RA)………………………………… Nasaba da Auratayyar Xalha binu Ubaidillah(RA)…………………………….. Nasaba da Auratayyar Zubair binul Awwam(RA)……………………………… Nasaba da Auratayyar Abdurrahman binu Auf(RA)…………………………… Nasaba da Auratayyar Sa’ad binu Abi Waqqas(RA)…………………………… Nasaba da Auratayyar Sa’id binu Zaid(RA)……………………………………. Nasaba da Auratayyar Abu Ubaida(RA)……………………………………….. Nasaba da Auratayyar Mu’awiya binu Abi Sufyan(RA)……………………….. Serekuta Tsakanin ‘Ya’yan Sahabbai da Ahalul Baiti…………………………. Serekuta Tsakanin Jikokin Sahabbai da Ahalul Baiti………………………….. Babi Na Huxu: Suna Linzami……………………………………………………. ‘Ya’yan Ali Masu Sunayen Sahabbai……………………………………………. Ha’incin Malaman Shi’a…………………………………………………………. Faxakarwa Dangane Da Sunaye…………………………………………………. Sunayen Mata Masu Kyawu……………………………………………………… Rufewa……………………………………………………………………………
 Gabatarwa
 Da sunan Allah, mai rahama, mai jin qai Lallai godiya ta tabbata ga Allah, muna gode masa, muna neman taimakonsa, muna neman gafara tasa. Muna neman tsari da Allah daga sharrin kawunanmu da miyagun ayyukanmu. Wanda Allah ya shirye shi, babu mai vatar da shi kuma wanda ya vatar babu mai shiriya tasa. Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kaxai, ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa Muhammad bawansa ne, kuma Ma’aikinsa ne. Tsira da aminci su tabbata a gare shi, da Alayensa, da Sahabbansa, da waxanda suka bi Sunnarsa har zuwa ranar sakamako. Bayan haka, babu shakka duk mai darasun Ilmul Firaq, watau ilmin qungiyoyi a Musulunci, zai san cewa qungiyar Shi’a an gina ta a kan harsashen qarya da yaudara. A cikin dukkanin qungiyoyin bidi’a, masu dangana kansu ga Musulunci, babu masu yawan qarya kamar ‘yan Shi’a. Wannan haka yake a da, kuma haka yake a yanzu. Almajirin Imam Malik mai suna Ashhabu ya ruwaito cewa an tambayi Malik dangane da su, sai ya ce, “Kada ka yi magana da su, kuma kada ka karvi ruwaya daga gare su domin suna yin qarya.” Kuma ruwaya ta inganta daga Imam Shafi’i, ya ce, “A cikin ‘yan bidi’a kaf, ban tava ganin waxanda suka fi Rafilawa qarya ba da shaidar zur.” Har yau, Shaihul Islam Ibnu Taimiya ya ce dangane da su, “Masana a fannin Hadisi da ruwaya sun haxu a kan cewa Rafilawa sun fi dukkan qungiyoyin bidi’a qarya. Qarya a cikinsu ta daxe; saboda haka malaman Musulunci suna sane da kevantarsu da yawan qarya.” ‘Yan Shi’a suna qira qarya su dangana ta ga Allah mai girma da xaukaka; suna yin qarya ga Annabi(SAW); suna yin qarya ga shugabannin Ahalul Baiti; suna yin qarya ga Sahabbai; kuma suna qarya ga xaixekun mutane da gama-garinsu. Daga cikin qarerayin da suka laqa ma Sahabban Annabi da iyalin gidansa, Ahalul Baiti, suna cewa wai gaba da qiyayya mai tsanani ta kasance tsakanin Ahalul Baiti da Sahabbai, kuma wai shugabannin Ahalul Baiti kamar Ali da Faxima, Allah ya qara musu yarda, suna ganin manyan Sahabbai irin su Abubakar da Umar da A’isha da Hafsa, Allah ya qara yarda a gare su, sun yi ridda, sun kafirta. Manufar wannan littafi ita ce rusa wannan qarya daga tushenta, da kuma tabbatar da yadda soyayya da qauna da ban girma da ‘yan uwantaka da zumunta suka kasance a tsakanin Sahabbai da Ahalul Baiti, Allah ya qara musu yarda baki xaya. Littafin ya fara da tattauna ma’anar Ahalul Baiti da Sahabbai daga mahangar Ahalus Sunna da Rafilawa, tare da bayanin matsayinsu a aqidar ko wanne daga vangarorin biyu. Wannan shi ne jigon babi na farko wanda yake tamkar gabatarwa ne ga littafin. Sai babi na biyu wanda ya bijiro da wasu daga qarerayin ‘yan Shi’a ga Ahalul Baiti da Sahabbai, da bayani filla-filla na vacin waxannan qarerayin, tare da kafa hujjoji daga littafan malaman Rafilawa da kansu a kan hakan. Babi na uku, wanda shi ne qashin bayan littafin, ya tattare bayanai ingatattu na tarihi waxanda suke nuna yadda dangantaka ta jini da serekuta ta haxa tsakanin Ahalul Baiti da Sahabbai, tun kafin zuwan Musulunci har zuwa tsara uku ko huxu bayan Musulunci, ta yadda ba ta yiwuwa a ce masu irin wannan dangantaka sun yi gaba ko qiyayya . Babin ya nuna a fili yadda yawancin manyan Sahabbai, waxanda Rafilawa suke da’awar cewa suna gaba da Ahalul Baiti, a haqiqa ‘yan uwantaka ta jini ta haxa tsakaninsu da Annabi(SAW) shi da kansa, da kuma sauran danginsa Banu Hashim da Banul Muxxalib. Babi na huxu kuma yana nuna soyayyar Ahalul Baiti ga manyan Sahabbai hatta bayan mutuwarsu, inda suke sanya wa ‘ya’yansu sunayensu don tunawa da su da riqon alqawarinsu da kuma neman albarkarsu. Wannan haqiqa ta tarihi, wacce ta fito daga littafan Rafilawa su da kansu, tana qara tabbatar da qaryar ‘yan Shi’a domin ga al’ada mutane ba sa sawa ‘ya’yansu sunayen maqiyansu. A qarshe, ina roqon Allah Maxaukaki da ya amfani Musulmi da wannan xan littafi, ya qaddara masa yarda da karvuwa a zukatan bayi masu neman gaskiya da shiriya, kuma ya ba ni ladan abinda na yi dai-dai a cikinsa, ya kankare zunuban kurakurai da tuntuven alqalami. Allahumma amin. Kaduna U. M. Labxo Mayu, 2010 Babi Na Xaya: Ahalul Baiti Da Sahabbai Ahlul Baiti da Sahabbai su ne babban jigon da za’a yi magana a kansa a cikin wannan littafi. A wannan babi na farko, za mu duba ma’anar waxannan sunaye a wajen Ahlus Sunna da ‘Yan Shi’a da matsayinsu a wajen ko wane. Ma’anar Sahabbai A Wajen Ahalus Sunna Sahabbai jam’in sahabi ne. Sahabi kuwa shi ne duk mutum (mace ko namiji) da ya gamu da Annabi (SAW) yana musulmi, kuma ya mutu a kan Musulunci. Abinda ake nufi da “ya gamu da Annabi (SAW)” watau ya haxu da shi, ya gan shi, ko ya zauna da shi na wani lokaci mai tsawo ko gajere. Abinda ya sa ba’a ce ya gan shi ba kawai, saboda a shigar da makaho, domin shi makaho tana yiwuwa ya gamu da shi amma bai gan shi ba. Kuma an ce “ya gamu da shi yana musulmi” saboda a fitar da kafirai waxanda suka gamu da shi amma ba su karvi Musulunci ba.To waxannan ba’a ce da su Sahabbai. Haka nan aka ce “ya mutu a kan Musulunci” domin a shigar da waxanda suka gamu da shi suna musulmi sa’an nan suka yi ridda a bayan rasuwarsa, amma kuma suka komo Musulunci kafin mutuwarsu. Waxannan ana lasaftasu a cikin Sahabbai. Amma waxanda suka yi ridda kuma suka mutu a kan riddar to waxannan ba’a sa su cikin Sahabbai. Wasu malamai sun sharxanta balaga. Watau sai wanda ya gan shi yana baligi shi ne ya zama sahabi, amma wanda ya gan shi yana qaramin yaro, to wannan ba sahabi ba ne. To amma idan yaro ya tasa, ya isa shekerun tamyizi, watau shekarun da akan aiki yaro ko kuma yaro yake kunyar fita ba wando, kamar shekara biyar zuwa bakwai, mai waxannan shekaru idan ya ga Annabi(SAW) ana lasafta shi a cikin Sahabbai. Kuma babu laifi mu qara jaddada cewa abubuwan da aka ambata duka dangane da ma’anar sahabi, babu bambanci tsakanin mace da namiji. Watau kamar yadda ake da Sahabbai maza haka nan ake da Sahabbai mata. Kuma duk hukuncinsu da darajarsu xaya ne. Don haka a taqaice, Sahabbai su ne mutane, maza da mata, waxanda Allah ya arzuta su da saduwa da Annabi ko kuma suka yi zama da shi. Wasu sun daxe tare da shi, sun lazimce shi, kamar abokansa da ‘yan uwansa da matansa. Wasu kuma sun zauna da shi lokaci kaxan, imma shekaru ko watanni ko kwanaki. Akwai ma waxanda suka gan shi sau xaya kawai, kamar waxanda suka haxu da shi a wajen hajjin ban kwana, ko waxanda ya wuce ta garinsu a kan hanyarsa zuwa wani wuri, ko kuma waxanda suka kawo masa ziyara, suka yi mubaya’a, kuma suka koma garuruwansu. Akwai wasu mutane da suka musulunta a zamanin Annabi (SAW) amma ba su samu ganinsa ba, ba su tava gamuwa da shi ba, kamar mutanen Qasar Yaman da suka musulunta a hannun Mu’azu binu Jabal da Abu Musal Ash’ari (RA), da kuma Najashi sarkin Habasha. Irin waxannan ba’a lasafta su cikin Sahabbai. Matsayin Sahabbai A Wajen Ahalus Sunna Sahabban Annabi(SAW) suna da matsayi maxaukaki a wajen Ahalus Sunna. A haqiqa, Ahalus Sunna ba sa fifita kowa a kan Sahabbai sai annabawa da manzanni kawai. Sahabbai su ne mafi xaukaka, mafi girma kuma mafi zavuwar bayin Allah bayan annabawa da manzanni. Wannan matsayi na Sahabbai Ahalus Sunna sun gina shi a kan ayoyi na Alqur’ani da hadisai na Annabi(SAW) waxanda suke tabbatar da shi. Ubangiji Maxaukaji ya yi bayanin abubuwan da suke nuna matsayin Sahabbai a cikin littafinsa mai tsarki. Allah ya tabbatar da imaninsu. Ya ce, “Kuma waxanda suka yi imani kuma suka yi hijira, kuma suka yi jihadi a cikin hanyar Allah, kuma da waxanda suka bayar da masauki kuma suka yi taimako, waxannan su ne muminai da gaskiya, suna da gafara da wani abinci na karimci. Kuma waxanda suka yi imani daga baya, kuma suka yi hijira kuma suka yi jihadi tare da ku, to, waxannan daga gare ku suke.” (Suratul Anfal: 74-75). A cikin aya ta farko, Ubangiji ya yi bayanin waxanda suka yi imani kuma suka yi hijira (waxannan su ne Muhajiruna), da kuma waxanda suka bayar da masauki ga masu hijirar (su ne Ansar), ya tabbatar da cewa su ne muminai na gaskiya. Waxannan kungiyar mutane biyu, Muhajiruna da Ansar, su ne Assabiqunal Auwaluna: Sahabbai waxanda suka yi rigaye wajen shiga Musulunci, imaninsu da rigayensu sun tabbata, kuma wanda duk ya shiga Musulunci daga bayansu yana biye da su ne. Allah ya tabbatar da tsarkin zukatansu da ihlasinsu kuma ya tabbatar da cewa kome suke yi dominsa ne suke yi da neman falalarsa da yardarsa. Ya ce, “Muhammadu Manzon Allah ne. Kuma waxannan dake tare da shi masu tsanani ne a kan kafirai, masu rahama ne a tsakaninsu, kana ganin su suna masu ruku’i masu sujada, suna neman falala daga Ubangijinsu da yardarsa.” (Suratul Fathi: 29). Kuma ya ce, “(Ku yi mamaki) ga matalauta masu hijira waxanda aka fitar daga gidajensu da dukiyoyinsu, suna neman falala daga Allah da kuma yarda, kuma suna taimakon Allah da Manzonsa. Waxannan su ne masu gaskiya.” (Suratul Hashri: 8). Bayan Ubangiji ya tabbatar da imanin Sahabbai da tsarkin niyarsu, kuma ya tabbatar da fifikonsu ba kawai a kan wannan al’umma ba, a’a har ma da sauran al’ummai. Ya ce, “Kun kasance mafi alherin al’umma wadda aka fitar ga mutane, kuna umarni da alheri kuma kuna hani daga abinda ake qi, kuma kuna imani da Allah” (Suratu Ali Imrana: 110). Imam Ibnu Kathir yace, “Wannan aya tana nufin dukkan al’umma, amma kuma mafifita a cikin wannan al’umma su ne na farkonta.” Har yau, Allah Mxaukaki yana cewa, “Kuma kamar wannan, muka sanya ku al’umma matsakaiciya (mafificiya, adala) domin ku kasance masu bayar da shaida a kan mutane.” (Suratul Baqara: 143). Wannan aya ita ma ma’anarta kamar ta farko ce. Allah ya yarda da Sahabban Annabi (SAW) kamar yadda ya tabbatar a wurare da dama a cikin littafinsa. Y ace, “Kuma masu rigaye na farko daga Muhajiruna da Ansar da waxanda suka bi su da kyautatawa, Allah ya yarda da su, kuma suma sun yarda da shi, kuma ya yi musu tattalin gidajen Aljanna: qoramu suna gudana a qarqashinsu, suna madawwama a cikinsu har abada. Wancan ne babban rabo mai girma.” (Suratut Tauba: 100). Kuma ya ce, “Lalle ne haqiqa Allah ya yarda da muminai a lokacin da suke yi maka mubaya’a a qarqashin itaciyar nan domin ya san abinda ke cikin zukatansu, sai ya saukar da natsuwa a kansu, kuma ya saka musu da wani cin nasara makusanci.” (Suratul Fathi: 18). A cikin wannan aya ta biyu akwai abubuwan lura. Allah ya tabbatar da imanin Sahabbai, ya kira su muminai, sa’an nan kuma ya shaida cewa ya yarda da su. Babu shakka wannan ba qaramar shaida ba ce ga Sahabbai, Allah ya qara yarda a gare su baki xaya. Waxannan kaxan ne daga cikin ayoyi da Ahalus Sunna suka gina matsayin Sahabbai a kansu. Bari mu duba vangaren hadisai mu gani. Hadisai da dama na Annabi(SAW) sun yi bayanin matsayin Sahabbai, martabarsu da falalarsu. A cikin wani hadisi, Manzo(SAW) yana cewa, “Ku tsoraci Allah, ku tsoraci Allah dangane da Sahabbaina. Kada ku riqe su abin jifa a bayana. Wanda duk ya so su, to da sona ne ya so su. Kuma wanda ya qi su, to da qina ne ya qi su. Wanda ya cutata musu haqiqa ya cuta min, wanda ya cuta min ya cuta ma Allah, kuma wanda ya cuta ma Allah ya kusanta ya kama shi.” Wannan hadisi yana nuna maxaukakin matsayi na Sahabbai inda aka gwada sonsu da son Annabi(SAW) kuma aka gwada cutata musu da cuta ma Allah. Wannan kuwa saboda zavin da Allah ya yi musu ne da baiwa da ya yi musu ta imani da tsarkin niyya da taimakon Annabi(SAW) wajen isar da saqon Musulunci. A cikin wani hadisin kuma, Manzo(SAW) yana cewa, “Kada ku zagi Sahabbaina; lalle da xayanku zai ciyar da kwatankwacin (dutsen) Uhudu na zinare da ba zai kai (matsayin) mudu ba na xayansu, ko rabin mudu.” Wannan hadisi yana nuna tazara dake tsakanin Sahabbai da waninsu, yadda qanqanen aikinsu ya fi na waninsu kome girmansa. Wannan kuwa saboda rigayensu ne ga shiga Musulunci da tsarkin niyyarsu da kasancewarsu mataimakan Annabi(SAW) wajen iyar da manzanci. Fifikon Sahabbai A Junansu Sahabbai su ne mafifita a wannan al’umma. Dalilai na Alqur’ani da Sunna sun tabbatar da cewa a cikin halittar Allah kaf babu wanda yake sama da su sai annabawa da manzanni kawai. Kuma kamar yadda suke su ne mafifita a cikin al’umma, to haka nan a junansu akwai fifiko. Kuma wannan yana cikin abinda ya kamata musulmi ya sani kuma ya zama wani vangare na aqidarsa dangane da Sahabbai. Mafifici a cikin Sahabbai kafataninsu shi ne Abubakar, Allah ya qara yarda a gare shi. A cikin wannan al’umma Abubakar shi ne na biyu. Watau daga Annabi(SAW) sai shi a wajen daraja da xaukaka. Mai biye masa shi ne Uamr xan Khaxxabi, daga shi kuma sai Usmanu xan Affana, sai kuma Ali xan Abu Xalib, Allah ya yarda da su. Waxannan huxu su ake cewa KhulafaurRashiduna, watau Khalifofin Annabi Shiryatattu. Masu biye ma waxannan a wajen falala su ne Sahabbai shida cikon goma waxanda Annabi(SAW) ya yi musu albishir da aljanna tun daga nan duniya. Waxannan su ne ake kira AsharatulMubasshara, watau Goma waxanda aka yi ma albishir da aljanna. Su ne huxun da aka ambata a sama, watau Abubakar da Umar da Usmanu da Ali, da kuma Xalha binu Ubaidillah, Zubairu binul Auwam, Sa’ad binu Abi Waqqas, Sa’id binu Zaid, Abu Ubaidah Amir binul Jarrah da Abdurrahman binu Awf, Allah ya yarda da su. Masu bin waxannan a daraja su ne Ahalu Badar, watau waxanda suka halarci yaqin Badar tare da Annabi(SAW). Su kimanin xari uku da goma sha uku ne. Daga su kuma sai waxanda aka yi ma albishir da aljanna banda goman da aka ambata. Waxannan sun haxa da Faxima xiyar Manzon Allah(SAW) da ‘ya’yanta guda biyu, Hassan da Hussaini, Allah ya yarda da su, da Thabit binu Qais da Bilal binu Rabah, da wasu masu dama. Bambanci tsakanin waxannan da goman da aka ambata na farko shi ne, su waxancan goman a lokaci guda ne Annabi(SAW) ya yi musu albishir xin su goma baki xaya. Su kuwa sauran a lokuta dabam-daban ne aka yi musu bishara. Daga waxannan sai Ahalu Bai’atilRidwani, watau Sahabbai waxanda suka halarci Sulhin Hudaibiya. Wannan sulhu ya faru a shekara ta shida bayan hijira tsakanin Annabi(SAW) da mushirikan Makka. Kuma a nan ne aka yi wannan mubaya’a ta yarda da ake cewa Bai’atulRidwani. Allah ne ya ba da labari cewa ya yarda da waxanda suka yi wa Annabi wannan mubaya’a, shi ya sa ake ce mata mubaya’ar yarda. (Duba Suratul Fathi, aya ta 18). Kimanin Sahabbai dubu da xari huxu ne suka yi wannan mubaya’a. Wannan shi ne tsarin fifikon daraja na Sahabbai a junansu. Kuma fifikon an gina shi ne a kan rigayen Sahabban ga shiga Musulunci da hidimarsu da sadaukar da kansu ga addini. Ba’a gina shi a kan jini, kusanci na qabila ko dangantaka ba, da sauransu. Haqqin Sahabbai A Kan Musulmi Sahabban Annabi(SAW), Allah ya yarda da su baki xaya, suna da haqqoqa a kan ko wane Musulmi waxanda ya wajaba a kiyaye da su. Haqqoqan sun haxa da: 1. Son su da qaunar su saboda Allah da Manzonsa suna son su. 2. Imani da fifikonsu a kan sauran dukkanin al’umma. 3. Imani da fifikon Abubakar, sa’an nan Umar, sa’an nan Usman, sa’an nan Ali a bisa wannan jeri. An ruwaito daga Abdullahi binu Umar(RA) yana cewa, “Mun kasance muna faxi, alhali Annabi yana raye, Abubakar ne ya fi, sa’an nan Umar, sa’an nan Usmanu, sa’an nan Ali. Kuma Annabi ya ji hakan amma bai hana mu ba.” 4. Kamewa ga barin ambaton tuntuvensu da kurakuransu, da nesantar shiga shara ba shanu dangane da savanin da ya afku a tsakaninsu. 5. Imani da alfarmar matan Manzon Allah(SAW) dukkaninsu, tare da cewa su uwayen muminai ne, kamar yadda Allah Maxaukaki ya tabbatar a cikin faxinsa, “Annabi ne mafi cancanta ga muminai bisa ga su kansu, kuma matansa uwayensu ne.” (Suratul Ahzabi: 6). Kuma a kudure cewa mafifitansu su ne Khadija da A’isha, Allah ya yarda da su baki xaya. Abinda ya gabata a taqaice shi ne aqidar Ahalus Sunna dangane da Sahabbai. Kuma wannan quduri ne wanda aka gina shi a kan koyarwar addinin Musulunci matsakaiciya. Watau koda yake Ahalus Sunna suna ganin matuqar girman Sahabbai, to amma ba sa kai su sama da matsayin da Shari’a ta ajiye su. Ga misali, ba sa ganin cewa su ma’asumai ne, ko sun san gaibu, da sauransu. Amma suna xaukar su a matsayin zavavvun bayin Allah waxanda suke da daraja maxaukakiya saboda rigayensu ga shiga addini da zamantakewarsu da Annabi(SAW). Ma’anar Sahabbai A Wajen ‘Yan Shi’a Babu bambanci tsakanin ‘yan Shi’a da Ahalus Sunna dangane da ma’anar Sahabbai. Su ma ‘yan Shi’a Sahabi a wajensu shi ne mutumin da ya gamu da Annabi(SAW) yana musulmi, kuma ya mutu a kan Musulunci. Wannan ma’ana ‘yan Shi’a sun aro ta daga malaman Ahalus Sunna kuma suka tabbatar da ita a cikin littafansu. Malamansu da kansu sun yi na’am da cewa sun aro wannan ma’ana daga Ahalus Sunna, kamar yadda babban shaihinsu Muhammad Almamiqani ya bayyana. Matsayin Sahabbai A Wajen ‘Yan Shi’a Inda ake samun bambanci tsakanin ‘yan Shi’a da Ahalus Sunna dangane da Sahabbai shi ne a wajen matsayinsu. A yayin da Ahalus Sunna suke xaukaka Sahabbai zuwa ga mafi xaukakar matsayi, qasa da matsayin annabawa kawai, su kuwa ‘yan Shi’a suna saukowa da su zuwa mafi qasqancin matsayi, qasa da matsayin manyan kafirai, kai qasa ma da matsayin Iblis kansa. A nan, kuma kafin mu shiga bayanin matsayin Sahabbai a ganin ‘yan Shi’a, yana da kyau mu tunawa mai karatu cewa duk abinda za mu faxi a wannan wuri, za mu naqalto shi ne kai tsaye daga littafan malaman Shi’a waxanda suka yarda da su, kuma suke a kan kare su a tsawon zamuna. ‘Yan Shi’a suna qudure gaba da qiyayya da wulaqanci da qasqanci masu tsanani ga Sahabban Annabi(SAW), kuma suna ajiye su a mafi qasqancin matsayi kamar yadda muka ambata a baya. Rafilawa suna qudure cewa Sahabbai baki xayansu sun yi ridda kuma sun kafirta sai ‘yan kaxan daga cikinsu. Ya zo a cikin mafi ingancin littafi a wajensu, watau littafin Alkafi na babban malaminsu mai suna Muhammad binu Ya’aqub Alkulaini, an ruwaito daga imaminsu na biyar, Muhammad Albaqir, wanda suke yiwa alkunya da Abu Ja’afar, cewa ya ce, “Mutane baki xaya sun yi ridda bayan Annabi(SAW) sai mutum uku kawai. (Mai ruwaya ya ce): sai na ce: Su waye mutum ukun? Ya ce: Miqdad binul Aswad da Abu Zarrin Algifari da Salman Alfarisi.” Wannan shi ne hukuncin ‘yan Shi’a a kan Sahabbai cewa dukkaninsu sun yi ridda sai mutum uku kawai. Amma wani malaminsu mai suna Muhammad binu Nu’uman Almufid ya savawa wannan ruwaya kaxan inda ya xaga adadin Sahabban da ba su yi ridda ba zuwa bakwai. Kuma har ila yau, wannan malamin ya naqalto ijima’in malaman Shi’a a kan wannan aqida. Aqidar ‘yan Shi’a dangane da Sahabbai ba ta tsaya a kan kafirta su ba kawai, amma suna ganin cewa su Sahabbai su ne mafiya sharrin halittar Allah. Watau ke nan suna ganin cewa ko a cikin kafiran ma su manya ne. Kuma suna qudure cewa imani da Allah da Manzonsa ba ya inganta sai an barranta daga gare su, musamman dai manya-manyansu kamar Abubakar da Umar da Usmanu da A’isha da Hafsa da sauran ire-irensu. Muhammad Baqir Almajalisi, xaya daga cikin manyan malamansu ‘yan baya (ya rasu a shekara ta 1111 bayan hijira), yana cewa, “Aqidarmu ta barranta ita ce cewa mu muna barranta daga gumaka huxu: Abubakar, Umar, Usman da Mu’awiya; da mataye huxu: A’isha, Hafsa, Hindu da Ummul Hakam; kuma muna barranta daga dukkan mabiyansu da magoya bayansu; kuma muna qudure cewa su ne mafiya sharrin halittar Allah a bayan qasa; kuma cewa imani da Allah da Manzonsa da imamai ba ya inganta sai bayan an barranta daga maqiyansu.” Har ila yau, Rafilawa suna qudure cewa khalifofi guda uku, watau Abubakar da Umar da Usman; da kuma uwayen muminai, watau matan Annabi(SAW) musamman A’isha da Hafsa, Allah ya yarda da su baki xaya, za’a yi musu azaba mai tsanani ranar Alqiyama tare da mafi sharrin bayi da manyan xagutan kafirai. Ya zo a cikin Tafsirul Qummi na Ali binu Ibrahim binu Hashim Alqummi, xaya daga manyan malaman Shi’a magabata (ya mutu a shekara ta 307 bayan hijira), a wajen fassarar Suratul Falaq, ya ce, “Falaq wata rijiya ce a Jahannama, ‘yan wuta suna neman tsari saboda tsananin zafinta. Sai ta roqi Allah saboda tsananin zafinta a yi mata izini ta yi numfashi. Da ta yi numfashi sai ta qone Jahannama baki xaya. A cikin wannan rijiya akwai wani akwati, mutanen dake cikin rijiyar suna neman tsari saboda tsananin zafin akwatin wanda ake kira sunduqi. To a cikin wannan sunduqin akwai mutane shida daga al’umman farko da mutane shida daga al’umman qarshe. Shidan dake daga al’umman farko su ne xan (Annabi) Adam wanda ya kashe xan uwansa (watau Qabila ke nan wanda ya kashe Habila); da Lamaruzu (na zamanin Annabi) Ibrahim wanda ya jefa Annabi Ibrahim a wuta; da Fir’auna (na zamanin Annabi) Musa; da Samiri wanda ya bautawa xan maraqi; da wanda ya yahudantar da Yahudawa da kuma wanda ya nasarantar da Nasara. Su kuwa mutane shida waxanda suke daga al’umman qarshe su ne: na xayan, da na biyun, da na ukun, da na huxun da mutumin Khawarijawa, da Ibnu Muljam (wanda ya kashe Sayyidina Ali), Allah ya la’ance su baki xaya.” Abinda mai littafin yake nufi da na xayan shi ne Abubakar, na biyun Umar, na ukun Usman, na huxun Mu’awiya, Allah ya yarda da su baki xaya. Voye sunayen waxannan khalifofi da yin nuni gare su da alqaluma abu ne da duk wanda ya saba da karatun littafan ‘yan Shi’a ya sani. Kuma a lura da yadda ya qare maganar da la’antar su, domin a wajensa su ne mafi kafircin al’umman qarshe waxanda suka cancanci zama a cikin wannan akwati na wuta. ‘Yan Shi’a suna halasta la’antar Sahabbai, har ma suna xaukar la’antar tasu a matsayin ibada wacce suke neman kusanci ga Allah da ita. Wani babban malaminsu da ake cewa Mulla Kazim ya ruwaito cewa Imaminsu na huxu, Ali binu Hussain binu Ali binu Abi Xalib, wai ya ce, “Wanda ya la’anci Jibtu da Xagutu (yana nufin Abubakar da Umar) la’ana guda Allah zai rubuta masa lada dubu sau dubu, ya kankare masa zunubi dubu sau dubu, kuma ya xaukaka masa daraja dubu sau dubu saba’in. Kuma wanda ya la’ance su da yammaci la’ana guda za’a rubuta masa kamar haka.” Banda wannan kuma akwai addu’o’i na musamman da aka wallafa don la’antar Abubakar da Umar, Allah ya yarda da su, waxanda Rafilawa suke yin wurdi da su, suna maimaita su safe da yammaci, kamar yadda Musulmi yake maimaira wurdan safe da na yamma a bayan sallolin farilla. Daga cikin irin waxannan addu’o’i akwai wata da ta shahara wacce suke kira Du’a’u Sanamai Quraishin, watau addu’ar gumakan Quraishawa biyu (Suna nufin Abubakar da Umar). Ga yadda lafazin addu’ar yake da Larabci kafin daga baya mu kawo fassararta da Hausa: Allahumma salli ala Muhammad, wa ali Muhammad, wal’an sanamai Quraishin wa jibtaihima, wa xagutaihima, wa ifkaihima, wa ibnataihima allazaini khalafa amraka, wa ankara wahyaka, wa jahada in’amaka, wa asaya Rasulaka, wa qallaba dinaka, wa harrafa kitabaka…. Allahumma il’anhuma fi makanunis sirri wa zahiril alaniya, la’anan kathiran abadan, da’iman sarmadan, la inqixa’a li amadihi wa la nafada li adadihi, la’anan ya’udu auwaluhu wa la yaruhu akhiruhu, lahum wa li a’awanihim, wa ansarihim, wa muhibbihim, wal musaddiqina bi ahkamihim…. Allahumma azzib hum azaban yastagithu minhu ahalun nari, amin ya Rabbal Alamin. Ma’anar addu’ar: Ya Allah ka yi daxin tsira ga Muhammad da alayen Muhammad. Kuma ka la’anci gumakan Quraishawa biyu, da jibtinsu da xagutunsu, da qarerayinsu da xiyansu mata biyu. Waxanda suka sava umarninka,suka yi musun wahayinka, suka butulce ma ni’imarka, suka juya addininka, suka sauya littafinka…. Allah ka la’ance su a cikin voyayyen sirri da zahirin dake sarari, la’ana mai yawa ta har abada, madauwamiya ta dun-dun-dun, wacce babu yankewa ga nisanta kuma babu qarewa ga adadinta, la’ana wacce farkonta zai riqa komowa kuma qarshenta bai tafiya, gare su da masu mara musu da mataimakansu da masu qaunarsu da masu koyi da maganarsu da masu gaskatawa da hukunce-hukuncensu…. Ya Allah ka yi musu azaba, azabar da ‘yan wuta za su riqa neman tsari da ita, amin ya Ubangijin Talikai. Ana gayyatar mai karatu da ya sake karanta wannan addu’a, sa’an nan ya yi tunani a kan abinda ta qunsa na zunzurutun qiyayya da qeta da mummunan fata ga waxannan manyan Sahabbai, Abubakar da Umar, Allah ya yarda da su. Abinda ya gabata a wannan vangare xan misali ne kaxan na yadda Rafilawa suka xauki Sanabban Annabi(SAW) da kuma matsayinsu a wajensu. A haqiqa akwai abubuwan ban mamaki dangane da qiyayyar ‘yan Shi’a ga Sahabbai da kafirta su, da la’antar su, da lanqaya musu miyagun lafuzza na zagi da cin mutunci da shiga irili waxanda alqalaminmu ba zai iya kattaba su ba sa saboda muninsu. Ma’anar Ahalul Baiti A Wajen Ahalus Sunna Bayan mun ga ma’anar kalmar Sahabi da yadda Ahalus Sunna da ‘yan Shi’a suka xauki Sahabbai da kuma matsayin da ko wane ya ajiye su, bari yanzu mu juya ga kalmar Ahalul Baiti don mu yi darasun ta, kuma mu yi nazarin yadda qungiyoyin biyu suka xauki Ahalul Baiti. Asalin kalmar ahalu tana nufin matar mutum, kuma tana nufin xaya ko da yawa (watau kalmar tilo ce kuma jama’u a lokaci guda). Ita kuwa kalmar baiti abinda take nufi gida. Idan aka ce ahalul baiti na mutum to ana nufin mutanen gidansa wanda ya haxa da matansa da ‘ya’yansa da dukkan wanda yake gidan na zuri’a da makusanta. Akwai kuma xaya kalmar mai kama da wannan kuma mai ma’anarta, watau alu, ko kuma kamar yadda muke cewa da Hausa: alaye. Waxannan kalmomi biyu ma’anarsu xaya, ba bambanci. Amma idan aka danganta waxannan kalmomi ga Annabi(SAW), aka ce Ahalu Baitinsa ko kuma Alayensa, to malamai sun yi savani dangane da ma’anarsu, ko kuma mu ce dangane da waxanda suka qunsa daga cikin iyalin Annabi(SAW) da zuri’arsa. Ra’ayi na farko. Masu wannan ra’ayi suna ganin cewa Ahalul Baiti, ko kuma Alaye, su ne waxanda sadaka ta haramta a kansu. Dalilin masu wannan ra’ayi shi ne hadisin da Bukhari ya ruwaito cewa, “Manzon Allah(SAW) ya kasance ana kawo masa dabino lokacin girbinsa; sai wannan ya kawo dabino, wancan ya kawo dabino har ya taru ya yi tsibi. Sai Hassan da Hussaini (suna yara) su riqa yin wasa da dabinon. Sai (wata ran) xayansu ya xauki dabino guda ya sa a bakinsa. Sai Manzon Allah(SAW) ya gan shi, sai ya fitar da dabinon daga bakinsa, sa’an nan ya ce, “Ba ka san cewa Alayen Muhammadu ba sa cin sadaka ba?!” Wannan hadisi ya nuna a fili cewa Hassan da Hussaini suna cikin Alayen Annabi, watau Ahalul Baiti nasa. Amma su ke nan su kaxai ne Ahalul Baiti ko kuwa? A’a, akwai wasu bayan su. Bayanin hakan kuwa an same shi a cikin hadisin da Muslim ya ruwaito cewa, “Abdul Muxxalib xan Rabi’a ya ba da labari cewa babansa Rabi’a xan Harisa xan Abdul Muxxalib da shi da Abbas xan Abdul Muxxalib sun faxawa Abdul Muxxalib xan Rabi’a da Falalu xan Abbas, Allah ya yarda da su, (suka ce): Ku tafi wurin Manzon Allah(SAW) ku ce masa: Ka saka mu cikin masu aikin tattara sadaka. Sai ya ce musu: Waxannan sadakokin dattin mutune ne kawai kuma lalle ba sa halasta ga Muhammadu da Alayen Muhammadu.” Wannan hadisi yana nunawa a bayyane cewa ba ‘ya’yan Annabi ne kawai, ko jikokinsa, suke Ahalul Baiti ba, a’a har ma da baffanninsa da ‘ya’yayensu. Domin su waxannan mutane guda biyu da aka ambata a cikin hadisin cewa sun tambaye shi ya saka su cikin masu aikin tattara zakka, watau Abdul Muxxalib xan Rabi’a da Falalu xan Abbas ‘ya’yan baffanninsa ne, guda abokin wasansa ne, gudan kuma xan abokin wasansa ne. Saboda haka, xaya qani ne, xayan kuma xa ne a wajensa. (Abdul Muxxalib da aka ambata a hadisin an sa masa sunan kakansa na biyu ne.) Wannan shi ne ra’ayin malamai kashi na farko, cewa ‘ya’yan Annabi(SAW) da jikokinsa da baffanninsa da zuri’arsu su ne Ahalul Baiti. Daga cikin masu wannan ra’ayi akwai Abu Hanifa da Shafi’i da Ahmad binu Hanbal da wasu malaman mazhabar Malikiyya. Ra’ayi na biyu. Masu wannan ra’ayi suna ganin cewa alayen Annabi(SAW) su ne ‘ya’yansa da jikokinsa da kuma matansa na aure kawai. Sun kafa hujja da hadisai guda biyu. Na farko hadisin Humaidin Assa’idi cewa Sahabbai sun tambayi Annabi(SAW) ya za su riqa yi masa salati? Sai ya ce, “Ku ce: Ya Allah ka yi tsira ga Muhammad da matayensa da zuri’arsa kamar yadda ka yi tsira ga Ibrahim, kuma ka yi albarka ga Muhammad da matayensa da zuri’arsa kamar yadda ka yi albarka ga Ibrahim, lalle kai ne abin godewa, mai girma.” Na biyu hadisin da yake cewa, “Ya Allah ka yi tsira ga Muhammad da alayen Muhammad.” Suka ce hadisi na biyu ya fassara na farkon, kuma ya nuna qarara cewa matan Annabi(SAW) da zuri’arsa su ne alaye, ko kuma Ahalul Baiti nasa. Yawancin malaman Malikiyya suna cikin masu wannan ra’ayi, kuma shi ne zavin manyan malamai, ciki har da Ibnu Taimiya, Allah ya rahamshe su baki xaya. Wannan ra’ayi yana da qarfi ainun kuma masu shi suna da hujjoji qarfafa da dalilai masu yawa, bayan waxanda muka ambata a sama. Daga cikinsu akwai hadisin Innar Muminai A’isha, Allah ya qara mata yarda, ta ce, “Alayen Muhammad ba su tava qoshi da gurasa tare da abin tsomi (miya ko romo) ba kwana uku a jere, har ya koma ga Allah mai girma da xaukaka.” A wannan hadisi, Innarmu A’isha, Allah ya qara mata yarda, tana ba mu labarin yanayin rayuwar iyalin Annabi(SAW) da irin abincin da ake ci a gidansa. Kuma ta yi amfani da kalmar alu, ko kuma alaye, wacce babu shakka ta haxa da matansa da ‘ya’yansa. Har yau, masu wannan ra’ayi sun kafa hujja da aya, faxin Allah Maxaukaki, “Ya matan Annabi! Ba ku zama kamar kowa ba daga mata, idan kun yi taqawa, saboda haka, kada ku sassautar da magana, har wanda ke da cuta a cikin zuciyarsa ya yi xammani, kuma ku faxi magana ta alheri. Kuma ku tabbata a cikin gidajenku, kuma kada ku yi fitar gaye-gaye irin fitar gaye-gaye ta jahiliyar farko. Kuma ku tsaida sallah, kuma ku bayar da zakka, kuma ku yi xa’a ga Allah da Manzonsa. Allah na nufin ya tafiyar da qazanta kawai daga gare ku, ya mutanen Babban Gida (Ahlal Baiti). Kuma ya tsarkake ku tsarkakewa.” (Suratul Ahzab: 32-33). Suka yi bayani cewa, waxannan ayoyi waxanda suke magana da matan Annabi kai tsaye sun kira su Ahalul Baiti, saboda haka duk wanda ya shiga qarqashin wannan suna to bayansu yake bi. Kuma wannan magana haka take idan aka duba ta a hankalce; domin matan mutum su ne haqiqanin mutanen gidansa, saboda ko ‘ya’yan mutum wannan sifa ba ta lazimtarsu a ko da wane lokaci; domin suna iya ficewa daga gidan (su zama ba mutanen gidan ba) imma zuwa gidajen aure idan ‘ya’ya mata ne ko kuma su yi gidan kansu idan maza ne. Matan mutum kuwa su ne mutanen gidansa na har abada. Muna qara karfafa wannan ra’ayi, muna bayyana hujjojinsa a fili, saboda mai da martani ga ‘yan Shi’a waxanda suke ganin cewa matan Annabi(SAW), Allah ya yarda da su, ba sa cikin Ahalul Baiti, kamar yadda za mu gani a nan gaba kaxan in Allah ya yarda. Ra’ayi na uku. Masu wannan ra’ayi suna ganin cewa, alayen Annabi(SAW), watau Ahalul Baiti, su ne mabiyansa dukkaninsu baki xaya har zuwa ranar Alqiyama. A wajen masu wannan ra’ayi duk Musulmi Ahalul Baiti ne domin ma’anar alu, ko kuma alaye, a wajensu shi ne mabiya. Daga cikin dalilansu sun kafa hujja da waxannan ayoyi: faxin Allah Maxaukaki, “Wuta ana gitta su a kanta, safe da maraice, kuma a ranar da Sa’a take tsayawa, ana cewa: Ku shigar da mutanen Fir’auna (alu Fir’auna) a mafi tsananin azaba.” (Suratu Gafir: 46). Da faxinsa Maxaukaki, “Lalle mun aika iskar tsakuwa a kansu, face mabiyan Luxu (alu Luxin), mun tserar da su a lokacin asuba.” (Suratul Qamar: 34). Suka ce a cikin waxannan ayoyi biyu an yi amfani da lafazin alu Fir’auna da alu Luxin ana nufin mabiyan Fir’auna da mabiyan Annabi Luxu(AS), wanda yake nuna ma’anar alu shi ne mabiya. Daga cikin masu wannan ra’ayi akwai wasu ‘yan mazhabar Shafi’iyya, ciki har da mashahurin malamin nan, Imam Annawawi mai littafin Arba’una Hadisan. Akwai wasu ra’ayoya dangane da ma’anar Ahalul Baiti banda waxanda muka ambata, amma ba za mu tsawaita da ambatonsu ba. Za mu taqaita a kan uku da muka rattaba saboda qarfin hujjojinsu, musamman ma ra’ayi na tsakiya wanda shi ne zavin manyan malamai. Saboda haka, ma’anar Ahalul Baiti a wajen Ahalus Sunna su ne matan Annabi(SAW) da zuri’arsa, watau ‘ya’yansa da jikokinsa, haka zalika baffanninsa da zuri’o’insu waxanda suka karvi Musulunci. Duk wata falala da baiwa da daraja wacce ta kevanci alaye to ta game waxannan duka, kuma duk sa’ad da Musulmi ya yi wa alaye salati tare da Annabi(SAW) to a gare su duka salatin yake faxawa. Matsayin Ahalul Baiti A Wajen Ahalus Sunna Ahalus Sunna suna xaukar Ahalul Baiti a matsayin Musulmi na gari, masu baiwa da xaukaka, waxanda Allah ya zave su, ya kevance su da falala da baiwa saboda kusancinsu da Annabi(SAW). Saboda haka suna girmama su irin girman da ya cancance su a Shari’a, ba tare da wuce gona da iri ba, kuma suna qaunar su saboda sonsu son Annabi ne, kuma son Annabi son Allah ne. Waxanda suke a cikinsu Sahabbai ne, kamar Ali da Faxima da Hassan da Hussaini da Abbas da xansa Abdullahi, da Ja’afar da Aqilu da sauransu, to waxannan suna ba su daraja biyu: kasancewarsu Sahabbai kuma kasancewarsu alaye. Waxanda kuma ba Sahabbai ba ne, ba su rayu tare da Annabi ba, kamar sauran ‘ya’yan Faxima qanana Ruqayya da Ummu Kulthum, da sauran ‘ya’yan Ali waxanda ya haifa da wasu matan nasa dabam, irin su Muhammad binul Hanafiyya da ‘yan uwansa, da sauran zuri’o’in baffanin Annabi(SAW): zuri’ar Abbas, zuri’ar Hamza, zuri’ar Aqilu, zuri’ar Ja’afar, da sauransu, to waxannan ana ba su darajarsu da Allah ya ba su ta kusanci ga Annabi(SAW) da haxa dangantakar jini da shi. Haka nan kuma, Ahalus Sunna suna yin salati ga Ahalul Baiti tare da Annabi a duk sa’ad da suka yi masa salati. Ahalus Sunna suna son Ahalul Baiti so irin na Musulunci, so na Shari’a, ba so na jahiliyya ba. Saboda haka ba su wuce makaxi da rawa a wajen qaunar su da girmama su. Ba sa danganta musu almarori, ko su qudure cewa suna da wani kayan gado na annabta wanda suka kevanta da shi koma bayan sauran Musulmi, ko su ce sun san gaibu, ko kuma su kaxai suka cancanci khilafa, da sauran irin waxannan qudure-qudure na masu addini da jahilci ko son zuciya. A wajen mu’amala da Ahalul Baiti, Ahalus Sunna suna tsayawa a kan koyarwar Alqur’ani da Sunna, ba sa wucewa ko taqi xaya. Ma’anar Ahalul Baiti A Wajen ‘Yan Shi’a A wajen ‘yan Shi’a, Faxima da Ali da ‘ya’yansu Hassan da Hussaini da zuri’arsu su kaxai su ne Ahalul Baiti. Sun gina wannan ra’ayi nasu a kan wani hadisi da suke ruwaitowa cewa, Innar Muminai Ummu Salma, Allah ya qara mata yarda, ta ce, “Ayar ‘Allah na nufin ya tafiyar da qazanta kawai daga gare ku, ya mutanen Babban Gida, kuma ya tsarkake ku tsarkakewa’ ta sauka a xakina ina zaune kusa da qofa, sai na ce: Ya Ma’aikin Allah, ni ba na cikin mutanen Babban Gida? Sai ya ce: ‘Ke kina bisa alheri, ke kina cikin matan Annabi(SAW).’ Ta ce: A cikin xakin Manzon Allah da Ali da Faxima da Hassan da Hussaini suna zaune, sai (Annabi) ya lulluve su da wani tufafi, sa’an nan ya ce, ‘Ya Ubangiji, waxannan su ne iyalin gidana, ka tafiyar da qazanta daga gare su kuma ka tsarkake su tsarkakewa.” Wannan hadisi malaman Ahalus Sunna sun ruwaito irinsa amma banda qarin da aka ce wai Innar Muminai Ummu Salma ta tambayi Annabi(SAW) ko ita ba ta cikin Ahalul Baiti, ya ce e. Wannan qarin bai inganta ba. Amma su Rafilawa sun yarda da wannan qarin kuma a dalilinsa ne suka kore matan Annabi(SAW) daga cikin Ahalul Baiti. Sai dai ba Uwayen Muminai kawai suka kore ba, sun ma kore har da wasu ‘ya’yan Faxima xin. Faxima ta haifawa Ali ‘ya’ya huxu. Su ne Hassan da Hussaini da Ruqayya da Ummu Kulthum. Ruqayya ta rasu tana qarama, amma Ummu Kulthum ta girma kuma ubanta ya aurawa Sarkin Musulmi Umar ita, har ta Haifa masa xa mai suna Zaidu, kuma tana cikin matansa da suka yi masa takaba. Shi wannan xan Zaidu ya girma amma bai bar baya ba. Sa’an nan ‘yan Shi’a sun kore sauran xiyan Annabi duka maza da mata, da zuri’o’insu daga jimillar Ahalul Baiti. Kamar yadda suka kore dukkan baffanin Annabi da zuri’o’insu. Babu shakka akwai abin ta’ajibi dangane da ma’anar Ahalul Baiti a wajen ‘yan Shi’a. Su a wajensu Ali da Faxima da ‘ya’yansu guda biyu kawai, banda sauran, su ne Ahalul Baiti. To me ya sa ba sa maganar Ummu Kulthum, ba sa lasafta ta a cikin Ahalul Baiti alhali kuwa ita ma xiyar Faxima da Ali ce kamar Hassan da Hussaini ba bambanci? Kuma ta ya za’a yi maganar mutanen gidan mutum amma a ce matansa ba sa ciki? Wane irin gida ne za’a ce matan gidan ba mutanen gidan ba ne, sai ‘ya’ya ne kawai mutanen gidan? Wannan hukunci ya sava hankali da al’ada kamar yadda ya sava da nassoshin Shari’a. Abu guda kawai wannan hukunci ya dace da shi, shi ne son zuciya wanda Rafilawa suka gina yawancin addininsu a kai. Wani abin mamakin kuma shi ne, ko a cikin ‘ya’yan Faxima xin, su ‘yan gaban goshin, banda Ummu Kulthum wacce suka jefar a juji, ko su ‘yan gaban goshin a cikinsu akwai wasu zavavvu fiye da wasu. ‘Ya’yan Hussaini sun fi ‘ya’yan Hassan qima, kuma a cikinsu ne ake da imamai tara tsaba, ko kuma goma in mun haxa har da ubansu Hussaini. Shi kuwa Hassan shi kaxai shi ne imami, amma a cikin zuri’arsa babu imami ko xaya. Don me ya sa aka samu wannan bambanci? Babu dalili, ba hujja sai son zuciyar ‘yan Shi’a kawai wanda, kamar yadda muka faxi a baya kaxan, shi ne tushe da suka gina addininsu a kai. Duba ka gani, mai karatu, yadda Shaixan yake wasa da hankulan ‘yan Shi’a. Xiyan Faxima, Allah ya qara mata yarda, su kaxai su ne Ahalul Baiti. Kuma a cikinsu banda Ummu Kulthum. Kuma, har yau, a cikin zavavvun, Hassan da Hussaini, zuri’ar Hussaini suke da imamai, duk da cewa shi ne qani, amma zuri’ar Hassan ba imami ko xaya a cikinsu. Mutane masu aiki da hankali sun yi ta tambaya: Da wane dalili ‘ya’yan Hussaini suka fi ‘ya’yan Hassan? Babu amsa mai gamsarwa sai ko hasashen tasirin Majusancin mutanen Iran. Tarihi ya tabbatar da cewa, a zamanin Sarkin Musulmi Umar binul Khaxxabi, bayan an ci daular Majusawa ta Farisa (Iran) da yaqi, Musulmi sun ci ganimar dukiyoyi da mataye. Daga cikin wannan ganima, Umar ya baiwa Hussaini(RA) kyautar ‘yar Sarkin Farisa mai suna Shaharbano wacce Hussaini xin ya mayar da ita sa-xaka. Wannan gimbiya kuma kwarkwara ita ce ta haifawa Hussaini xansa Ali wanda ake ma laqabi da Zainul Abidin, wanda kuma ta hanyarsa ne zuri’ar Hussaini ta xore. To da yake yawancin ‘yan Shi’a mutanen Farisa ne, sai suka laqe ma zuri’ar Hussaini saboda ‘ya’yan xiyarsu ne. Dalili ke nan da ya sa suka fifita su a kan zuri’ar Hassan. Matsayin Ahalul Baiti A Wajen Rafilawa A wajen ‘yan Shi’a, Ahalul Baiti, kamar yadda suka fahimce su, su kaxai su ne Musulmi kuma babu mai zama Musulmi sai wanda yake son su kuma yake jivintar su, jivinta da so waxanda suka dace da fahimtar Rafilawa. A kan wannan ne suka gina aqidarsu cewa Sahabbai duka sun yi ridda bayan rasuwar Annabi(SAW) sai mutum bakwai kawai. Waxannan mutane su ne Miqdad binul Aswad, Abu Zarrin Algifari, Salman Alfarisi, Ammar binu Yasir, Abu Sasan Al’ansari, Huzaifa binul Yaman da Abu Amra, Allah ya qara musu yarda. Waxannan Sahabbai bakwai da Rafilawa suka yarda da Musuluncinsu, babu abinda ya raba su da sauran Sahabbai ‘yan uwansu sai kawai cewa sun yi qaurin suna da kasancewa su masoyan Ali binu Abi Xalib ne kuma sun goyi bayansa a rikicin da ya faru tsakaninsa da Mu’awiyya binu Abi Sufyan. Wannan yana nuna cewa, a ganin ‘yan Shi’a ba Musulmi sai Ahalul Baiti, sai kuma waxanda suka bi su, suka jivince su. Don haka ne suka sanya imani da imamai a matsayin xaya daga shika-shikan Musulunci. Babban malamin Hadisi a wajen ‘yan Shi’a, Muhammad binu Ya’aqub Alkulaini, ya ruwaito Abu Ja’afar, imamin Rafilawa na shida, yana cewa: “An gina Musulunci a kan abubuwa guda biyar: sallah da zakka da hajji da azumi da wilaya (watau imama).” Don haka, matsayin Ahalul Baiti a wajen Rafilawa ya wuce a ce wai su zavavvu ne, ko masu girma, ko masu falal a addini. A’a, wuce nan! Ahalul Baiti a wajen ‘yan Shi’a su ne addinin kansa. Don su aka halicci duniya da lahira, suna sama da annabawa da manzanni da mala’iku makusanta, don haka ya wajaba a bauta musu. Wannan zai bayyana a fili idan muka yi darasun matsayin imamai a wajen Rafilawa. Matsayin Imamai A Wajen ‘Yan Shi’a Matsayin imamai a wajen Rafilawa babu sama da shi, domin suna aza su sama da annabawa da manzanni, kuma a wani yayi su ba su sifofin allantaka. ‘Yan Shi’a suna xaukar imamai a matsayin ma’asumai, waxanda ba sa kuskure kuma ba sa aikata zunubai qanana ko manya, kamar annabawa da manzanni ba bambanci. Saboda haka, ba sa mantuwa, ba sa tuntuve, ba sa sha’afa, ba sa rafkanuwa. Dangane da wannan, wani babban malaminsu da ake kira Muhammad binu Nu’uman Almufid, yana faxin, “Lalle imamai waxanda suke tsaye matsayin annabawa wajen zartar da hukunce-hukunce da tsai da haddoji da tsare shari’o’i da ladabtar da talikai ma’asumai ne kamar ismar annabawa, kuma bai yiwuwa su yi rafkanuwa a cikin wani lamari na addini, kuma ba sa mance wani abu na hukunce-hukunce.” Wani malamin nasu mai suna Abu Ja’afar Muhammad binu Ali binu Hussain binu Musa binu Babawaihi Alqummi (wanda aka fi sani da laqabin Assaduq) yana cewa, “Qudurinmu dangane da annabawa da manzanni da imamai shi ne cewa su ma’asumai ne, tsarkaka ne daga dukkan wani datti. Kuma cewa su ba sa aikata zunubi qarami ko babba, kuma ba sa savawa Allah abinda ya umarce su kuma suna aikata abinda aka umarce su. Wanda ya kore musu isma dangane da wani abu na lamarinsu to haqiqa ya jahilce su, kuma wanda ya jahilce su to shi kafiri ne.” ‘Yan Shi’a Rafilawa suna qudure cewa imamansu sun san gaibu, kuma suna da sanin abinda ya faru tun farkon halitta da abinda zai faru har zuwa ranar Alqiyama. Malaminsu Kulaini ya ruwaito daga imaminsu na shida, Abu Abdillahi, ya ce, “Na rantse da Ubangijin Ka’aba, na rantse da Ubangijin wannan ginin (Ka’aba) -ya maimaita sau uku- da na kasance tare da (Annabi) Musa da Haliru da na faxa musu cewa ni na fi su sani, da na ba su labarin abinda ba su sani ba; domin Musa da Haliru(AS) an ba su sanin abinda ya kasance ne (kawai) amma ba’a ba su sanin abinda zai zo da abinda zai kasance ba har zuwa ranar Alqiyama. Mu kuwa (watau imamai) mun gaji wannan ilmi daga Manzon Allah gado na haqiqa.” Malaminsu, Muhammad binu Nu’uman Almufid, ya tabbatar da wannan aqida tasu. Ya ce, “Imamai daga zuri’ar (Annabi) Muhammad (SAW) sun kasance suna sanin abinda yake voye cikin zukatan wasu bayi, kuma sun san abinda zai kasance kafin kasancewarsa.” Rafilawa suna qudure cewa wahayi yana sauka ga imamansu. Domin tabbatar da haka, sun ruwaito daga imaminsu Abu Abdillahi, ya ce, “Mu ana ba mu guzuri (na ilmi) dare da rana, kuma ba don ana ba mu guzuri ba da abinda yake gare mu (na ilmi) ya qare. (Mai ruwaya) Abu Basir ya ce: Allah ya sanya ni fansar ka, wane ne yake zuwa muku? Ya ce: Daga cikinmu akwai wanda yake gani da ido quru-quru; daga cikinmu akwai wanda yake ji da kunnensa amo kamar amon sarqa a cikin tasa. (Mai ruwaya) ya ce: Na ce: Allah ya sanya ni fansarka, waye yake zuwa muku da wannan? Ya ce: Wani halitta ne wanda ya fi Jibirilu girma.” Mai karatu yana iya gani cewa wannan ruwaya ba ta bar wani yanayi na saukar wahayi ga annabawa da manzanni ba face ta tabbatar da shi ga imamai. Har ila yau, ‘yan Shi’a suna wuce gona da iri wajen son imamansu da girmama su da kambama su har su fifita su a kan annabawa da manzanni da mala’iku makusanta ga Ubangiji. Ya zo a cikin irin ruwayoyin da suke danganawa ga Annabi(SAW) cewa wai ya ce da Ali(RA): “Lallai Allah mai girma da xaukaka ya fifita annabawansa manzanni a bisa mala’iku makusanta, kuma ya fifita ni a kan dukkanin annabawa da manzanni. Ya kai Ali, fifiko a bayana ya tabbata a gare ka da imamai masu zuwa a bayanka.” A cikin wani littafin nasu mai suna Haqqul Yaqin fi UsulidDin, mai littafin, Abdullahi binu Shabbar, yana cewa, “Ya wajaba a yi imani cewa Annabinmu da alayensa ma’asumai suna da fifiko a kan annabawa da manzanni da mala’iku makusanta saboda hujjoji masu yawan gaske da suka zo da haka.” Banda wannan duka, Rafilawa suna tabbatar wa da imamansu sifofin allantaka. Daga cikin irin abubuwan da suke danganta wa Ali binu Abi Xalib(RA) akwai wannan ruwaya cewa wai ya ce, “Ni ne idanun Allah; ni ne hannun Allah; ni ne qofar Allah.” A wata ruwayar kuma ya ce, “Ni ne ilmin Allah; ni ne zuciyar Allah mai kiyayewa; ni ne harshen Allah mai furuci; ni ne idanun Allah masu gani; ni ne haqarqarin Allah; ni ne hannun Allah.” Danganta irin waxannan ruwaroyi na qarya bai tsaya kan Ali ba kawai, a’a har ma ga Annabi(SAW) suna dangantawa. Sulaim binu Qais ya ruwaito cewa Manzon Allah(SAW) ya faxi ga Ali kamr haka: “Ya Ali, kai kana daga gare ni, ni ina daga gare ka. An gauraya namanka da namana, da jininka da jinina…. Wanda ya yi musun wilayarka ya yi musun allantakar Allah. Ya Ali, kai ne tutar Allah mafi girma a bayan qasa bayana, kuma kai ne bango mai girma a ranar Alqiyama. Wanda ya shiga inuwarka ya rabanta domin hisabin talikai duka yana hannunka kuma makomarsu na gare ka. Mizani naka ne; siraxi naka ne; taron Alqiyama naka ne; hisabi naka ne. Wanda ya fake da kai ya tsira kuma wanda ya sava maka ya halaka. Allah ka shaida, Allah ka shaida.” Kamar yadda mai karatu yake iya gani, a wajen ‘yan Shi’a imamai su ne komai. Suna gaba da annabawa da manzanni kuma suna tarayya da Ubangiji a allantakarsa. Wannan ya sa aka samu wasu daga cikinsu waxanda suke bauta musu kuma suna bayyana wannan a fili ta wajen irin sunayen da suke saka wa ‘ya’yansu, kamar Abdul Hussain, Abdul Amir, da sauransu. Babi Na Biyu Qarerayin Rafilawa Ga Ahalul Baiti Da Sahabbai Allah Maxaukaki ya sifanta “waxannan da ke tare da Annabi” watau Sahabbansa waxanda suka haxa da alayensa da sauran mabiyansa, da wasu sifofi. Ya ce, “Muhammadu Manzon Allah ne. Kuma waxannan da ke tare da shi masu tsanani ne a kan kafirai, masu rahama ne a tsakaninsu, kana ganin su suna masu ruku’i masu sujada, suna neman falala daga Ubangijinsu, da yardarsa. Alamarsu tana a cikin fuskokinsu, daga kufan sujuda. Wannan shi ne siffarsu, a cikin Attaura. Kuma siffarsu a cikin Injila, ita ce kamar tsiron shuka wanda ya fitar da reshensa, sa’an nan ya qarfafa shi, ya yi kauri, sa’an nan ya daidaita a kan qafafunsa, yana bayar da sha’awa ga masu shukar, domin (Allah) ya fusatar da kafirai game da su.” (Suratul Fathi: 29). Wannan aya ta tabbatar da abubuwa kamar haka: 1. Muhammadu(SAW) Manzon Allah ne. 2. Waxanda suke tare da shi masu tsanani ne a kan kafirai. 3. Masu rahama ne a tsakaninsu. 4. Suna yawaita sallah. 5. Domin neman yardar Allah. 6. Akwai ambatonsu da yabo a cikin Attaura da Linjila. 7. Masu qin su kafirai ne. A nan muna jawo hankalin mai karatu ga abu na uku: Allah ya tabbatar da siffar rahama da jin qai a tsakanin Sahabbai junansu ga juna. Rahama ta fi soyayya qarfi saboda ita ta haxa matuqar qauna tare da tausayi da tausasawa da fifitawa a kan kai, kamar yadda yake a tsakanin iyaye da ‘ya’yansu ko ma’aurata a yayin da suka jitu, zaman aure ya yi tsawo. Da wannan siffa Allah ya siffanta “waxannan da ke tare da Annabi(SAW)”, watau alayensa da Sahabbansa. Amma ‘yan Shi’a su suna ganin ba haka ba. Su a ganinsu akwai matuqar gaba da qiyayya, qeta da mugunta, mugun nufi da kausasawa a tsakanin Sahabban Manzon Allah(SAW) da alayensa, watau Ahalul Baiti. Wannan shi ne addinin Rafilawa wanda suke qudurewa a zukatansu, kuma suna ganin duk wanda bai yarda da haka ba to shi ba Musulmi ba ne. Amma Ahalus Sunna su a ganinsu wannan ra’ayi na ‘yan Shi’a qaryatawa ne ga Alqur’ani, kuma qarya ce tsagwaronta a kan zavavvun bayin Allah na gari. Kai a cikin wannan aqida ma akwai suka ga Annabinmu Muhammad(SAW) domin “waxanda suke tare da ko wane annabi” mutanen kirki ne, don me sai Sahabban Annabinmu kawai su ne ba su da nagarta? Mabiyan Annabi Nuhu(AS), ga misali, “waxanda suke tare da shi” ko kuma mu ce Sahabbansa,mutane ne na gari. Allah ya yabe su a cikin Alqur’ani, ya ce, “Aka ce: Ya Nuhu! Ka sauka da aminci daga gare mu da albarka a kanka, kuma rahama ta tabbata a kan waxansu al’ummomi daga waxanda suke tare da kai.” (Suratu Hud: 48). Haka nan Sahabban Annabi Isa(AS), watau Hawariyyawa, su ma mutane ne na qwarai. Allah ya yabe su har ma ya umarce mu da mu yi koyi da su. Ubangiji Maxaukaki ya ce, “Ya ku waxanda suka yi imani! Ku kasance mataimakan Allah, kamar abinda Isa xan Maryama ya ce ga Hawariyawa: Waxanne ne mataimakana zuwa ga (aikin) Allah? Sai Hawariyawa suka ce: Mu ne mataimakan Allah.” (Suratus Saff: 14). Haka ma duka sauran annabawa Sahabbansu mutanen kirki ne kuma Allah ya yabe su, don me sai Sahabban Annabinmu ne kawai su ne ba na kwarai ba? Babu shakka a cikin wannan akwai suka da cin zarafi ga Annabi(SAW). Muna roqon Allah ya shiryi ‘yan Shi’a masu wannan karkatacciyar aqida. Domin tabbatar da wannan karkatacciyar aqida ta su, malaman Shi’a suna qira qarerayi suna dangana su ga waxannan zavavvun bayi, kuma suna tabbatar da su a cikin littafansu, kamar yadda suke tarbiyantar da mabiyansu a kan qudure su da yaxa su. Waxannan qarerayi su ne za mu yi bayanin su a taqaice a wannan babi. Sahabbai Sun Qwacewa Ali Khilafa Qarya ta farko da malaman Shi’a suka laqa ma Sahabbai da Ahalul Baiti ita ce wacce ta shafi khilafa, watau shugabancin Musulmi bayan rasuwar Manzon Allah(SAW). Suka ce khilafa haqqin Ali ce, Allah ne ya naxa shi da kansa, kuma ya umarci Annabi da ya bayyanawa Musulmi hakan. Kuma wai Annabi ya yi wasiyya, ya bayyana a fili cewa Ali ya gaje shi a shugabancin al’umma bayansa. Amma, a cewarsu, sai gaggan Sahabbai irin su Abubakar da Umar da Usman da Abdurrahman da Xalha da Zubair; da sauransu, suka haxa baki suka haramtawa Ali wannan haqqi nasa saboda hassada da qiyayya. Kuma da wannan Rafilawa suka yiwa Sahabbai kuxin goro, suka ce duka sun kafirta, sun yi ridda saboda sun qi zartar da wasiyyar Annabi(SAW). A ra’ayin ‘yan Shi’a, wannan shi ne dalili na farko da ya jawo gaba da qiyayya tsakanin Ahalul Baiti da Sahabbai saboda Sahabbai sun wulaqanta shugaban Ahalul Baiti, watau Sayyidina Ali, sun qasqanta shi, sun hana masa haqqinsa, kuma sun tilasta masa yin mubaya’a ga Abubakar da biyayya a gare shi. Sahabbai Sun Wulaqanta Faxima Qarya ta biyu da Rafilawa suka qagawa Ahalul Baiti da Sahabbai don su nuna cewa gaba ta wanzu a tsakaninsu shi ne abinda suke faxi cewa wai Sahabbai, musamman Abubakar da Umar, sun wulaqanta Nana Faxima, sun ci zarafinta kuma sun zalunce ta. Suka ce Abubakar, a matsayinsa na shugaban Musulmi, ya hana ta gadon mahaifinta kuma wai Umar ya buge ta har ya karya qashin haqarqarinta kuma ya sa ta yi varin cikin da take xauke da shi. Kuma wai duka wannan ta’annuti manyan Sahabbai suna gani ba wanda ya ce uffan, maimakon haka ma duka sun goyi baya. Kuma wai mijinta, Ali binu Abi Xalib, ya kasa yin komai a kan wannan wulaqanci da zalunci saboda an rinjaye shi, an raunana shi, kuma Sahabbai waxanda dama duka sun yi ridda, sun haxe bakinsu, babu mai goyon bayansa. Umar Ya Qwaci Xiyar Ali Qarya ta uku mai ban takaici kuma mai ban dariya a lokaci guda ita ce faxinsu cewa wai Sayyidina Umar a lokacin da yake khalifa ya qwaci xiyar Ali binu Abi Xalib, watau Ummu Kulthum xiyar Faxima kuma qanuwar Hussaini, ya aure ta da qarfi, ba tare da izini ko yardar ubanta ba. Kalmar da suke amfani da ita wajen ba da labarin wannan almara ita ce “gasab”, watau fashi ko kuma qwace. A zamanin Jahiliyya “gasab” yana faruwa, watau fashin ‘ya’ya mata, inda za’a samu wani qaqqarfan namiji, amma mara mutunci, ya gamu da yarinya ta tafi xaukar ruwa a rafi, ko ya iske ta a gidansu, ya kama ta ya tafi da ita da qarfin tsiya. Idan ubanta jarumi ne, ko kuma yana da dangi masu taimakon sa, sai ya je a buga ya qwato ta. Idan kuwa ba haka ba, to sai ya haqura da auren “gasb”. Wai irin wannan suke nufin Umar ya yiwa Ali! Sahabbai Sun Yaqi Ali Qarya ta huxu ita ce faxinsu cewa wai Sahabbai, a qarqashin shugabancin Innar Muminai Nana A’isha da Xalha da Zubair, sun yaqi Sayyidina Ali kuma sun goyi bayan Mu’awiya binu Abi Sufyan a rikicin khilafa da ya wanzu tsakaninsa da Ali. A kan wannan qarya ‘yan Shi’a suka gina gabarsu da Innar Muminai A’isha, suna kafirta ta, suna la’antar ta kuma suna jifan ta da abin qazafi wanda Allah ya barrantar da ita daga gare shi. Sahabbai Sun Kashe Hussaini Qarya ta biyar da Rafilawa suka laqa ma Sahabbai ita ce cewa wai sun kashe Sayyidina Hussaini binu Ali(RA) a yayin da suka haxe baki suka mara wa abokin hamayyarsa, Yazid binu Mu’awiya, baya kuma suka yaqe shi a qarqashin tutar Yazid xin inda shi Hussaini ya yi shahada a Karbala. ‘Yan Shi’a sun yi amfani da mutuwar Hussaini a fagen fama wajen rura wutar qiyayya a zukatan mabiyansu, a yayin da suka mayar da ranar rasuwarsa ranar alhini da biki na shekara-shekara kuma suka wajabta xaukar fansarsa a kan dukkan Ahalus Sunna. Maganganun ‘Yan Shi’a Na Karo Da Juna A taqaice waxannan qarerayi guda biyar da su Rafilawa ke kafa hujja a kan ra’ayinsu na dangantaka tsakanin Ahalul Baiti da Sahabbai. Amma waxannan qarerayi maganganun ‘yan Shi’a su da kansu suna warware su. Da farko dai an san Ali binu Abi Xalib da jarunta da sadaukantaka da bardanta. Haka yake a cikin littafan Rafilawa da na Ahalus Sunna, ba bambanci. Kai ko a Adabin Hausa da waqen Hausawa, an san Ali a matsayin jarumi mai tsananin tumbe, mai ban kashi a fagen fama, wanda ba ya jin tsoron ya buga da kafirai komai yawansu. Daga cikin kirarinsa a Adabin Hausa ana cewa: Aliyu garga mazan fama, gadangu qusar yaqi. Kas kafiri, qi kafiri, gaba da maqi sallah, almakashin maqiya Baban Zara. Aliyu haidara, Ali jan zaki, Aliyu jijiya ba nama ba. A littafan ‘yan Shi’a kuwa, suna danganawa Ali ayyukan bardanta da sadaukantaka waxanda ko ifiritan aljanu ba su iya kwatanta irin su. To ya mutum jarumi kamar Ali za’a ci zarafin matarsa, uwar ‘ya’yansa, kuma xiyar Manzonsa, amma ya qyale?! Kuma ta yaya mai siffa irin wannan za’a qwaci xiyarsa, a aure ta a kan tilas ba da yardarsa ba?! Dangane da batun khilafa kuwa da cewa Allah ne da kansa ya naxa Ali kuma Annabi(SAW) ya yi wasiyya da haka, Rafilawa suna ruwaitowa a cikin littafansu cewa Ali(RA) ya qi khilafa a yayin da aka zo yi masa mubaya’a kuma ya guje ta. Sun ruwaito cewa, a lokacin da Sahabbai suka nemi Ali domin yi masa mubaya’a bayan kisan Usmanu, ya ce da su: “Ku qyale ni, ku nemi wanina. Ni in zama waziri a gare ku ya fiye min in zama sarki.” Kuma har ila yau, sun ruwaito shi yana cewa, “Na rantse da Allah ban da kwaxayin khilafa kuma ban da sha’awar shugabanci, amma ku kuka kira ni zuwa gare ta, kuka tilasta ni a kan ta.” To idan Allah ne ya naxa Ali ya shugabanci Musulmi kuma yana sane Annabi(SAW) ya yi wasiyya da haka, ta ya zai guji khilafa, ya qi karvar ta sai an tilasta masa?! Wani abu kuma da yake qara tabbatar da tufka da warwara a maganganun Rafilawa a kan dangantakar Ali da sauran Sahabbai shi ne yadda littafansu suke tabbatar da rawar da manyan Sahabbai suka taka wajen aurensa da Faxima. Babban malamin ‘yan Shi’a mashahuri, Ali binu Isa Al’arbali, da qasaitaccen malaminsu mai yawan rubuce-rubuce, Muhammad Baqir Almajalisi, sun rubuta qissar auren Ali da Faxima, Allah ya yarda da su, a cikin littafansu. Abinda suka ambata a taqaice shi ne cewa Abubakar da Umar da Sa’ad binu Mu’az Ba’ansare, Allah ya qara musu yarda, su ne suka baiwa Ali shawara da ya nemi auren Faxima a wajen mahaifinta Annabi(SAW). Kuma da Ali ya yi musu uzuri da qarancin abin hannu sun qarfafa masa guiwa kuma suka yi alqawarin taimaka masa. Waxannan malamai na Shi’a sun tabbatar da cewa, a lokacin da Annabi(SAW) ya amince ya aurawa Ali xiyatsa, Usman binu Affan ne ya biya sadakin auren kuma Abubakar ne ya sayi kayan xaki da aka kai amarya da su. Wannan qissa wacce manyan malaman Shi’a suka tabbatar da ita a cikin littafansu soyayya take nunawa da qauna tsakanin Ali da sauran Sahabbai amma ba qiyayya ba. Sai dai malaman Shi’a na wannan zamani suna voye irin wannan qissa domin mugun nufi da qoqarin vata sunan Sahabban Annabi da Ahalul Baiti baki xaya. Su kuwa ‘yan dagajin Shi’a na Nijeriya, irin su Zakzaki waxanda ba sa iya karanta littafin da ba shi da wasali, waxannan wataqila ko ganin qissar ma ba su tava yi ba. Daxa ballantana sauran mabiyansu, ‘yan Buraza, waxanda su da mai wasalin da mara wasalin duka xaya ne a wajensu. Ba abinda suke iya karantawa daga TRANSLATION sai TRANSLITERATION! Allah ya raba mu da fundum-fundum a kududdufin jahilci. Haqiqanin Alaqar Ahalul Baiti Da Sahabbai Abinda Ahalus Sunna suka sani, kuma suke quduri da shi, shi ne cewa babu abinda yake tsakanin Ahalul Baiti da Sahabbai sai soyayya da qauna da ban girma. Kuma wannan quduri na Ahalus Sunna shi ne yake dacewa da abinda Allah ya ba da labari da shi a cikin littafinsa mai tsarki da abinda yake cikin littafan Hadisi ingantattu da sauran littafan magabata na gari. Littafan Ahalus Sunna suna cike da bayanin girmamawar Abubakar da Umar, Allah ya yarda da su, ga Ali(RA), da ma sauran dangin Annabi Banu Hashim da Banul Muxxalib baki xaya, da yadda suka fifita shi, suka kwarzanta shi, suka sanya shi gaba da kowa a wajen martabawa da darajantawa. Kuma abu ne da ya tabbata a tarihi cewa Sarkin Musulmi Umar ya fifita Ahalul Baiti a tsarinsa na rabon ganima da dukiyar qasa ga al’umma. A lokacin da ya rattaba sunaye a Diwani don wannan manufa, ya gabatar da Banu Hashim, sa’an nan Banul Muxxalib. Ya gabatar da Abbas baffan Annabi, da Ali da Hassan da Hussaini, kuma ya ba su kaso sama da na kowa. Ya ma fifita Usama binu Zaid binu Harisa, wanda xa ne na bawan Annabi da ya ‘yanta, a bisa xansa Abdullahi. Wannan duka saboda girmamawa ga Annabi(SAW) da kiyaye haqqinsa. Haka nan Ahalus Sunna baki xayansu, tun daga zamanin Sahabbai har ya zuwa yau, babu mai qin Ali(RA) ko wani daga alayen Annabi(SAW). Maimakon haka, dukkaninsu suna qaunar su, suna daraja su, kuma suna bautawa Allah da son su. Idan mai karatu yana buqatar hujja a kan wannan, sai ya duba yadda sunayen Ali da Faxima da Hassan da Hussaini suka bazu a cikin al’ummarmu, ina nufin Musulmin Nijeriya. Har ma ya zama al’ada a wajen mu inda duk aka haifi tagwaye maza to ba wata magana sunansu Hassan da Hussaini. Kamar yadda Hausawa suka qware wajen nau’anta sunan Faxima saboda yawansa. Su ce Faxima, Fati, Binta, Batulu, Zahra ko Zahara’u, da sauransu. Babu wani suna da ya samu haka a tsakanin Musulmin Nijeriya Ahalus Sunna. Wannan kuma yana nuna qaryar ‘yan Shi’a, kuma ya isa ya sa su kunya in da suna da kunya. Kuma kamar yadda sauran Sahabbai suke son Ahalul Baiti, haka su ma Ahalul Baiti suke son Sahabbai baki xayansu kuma suke girmama su, musamman dai khalifofi guda uku, watau Abubakar da Umar da Usman, da kuma uwayen muminai, matan Manzon Allah(SAW), Allah ya yarda da su baki xaya. Ya tabbata cikin littafan Ahalus Sunna cewa Ali da ‘ya’yansa Hassan da Hussaini, Allah ya yarda da su, suna matuqar nuna so da qauna da girmamawa ga Abubakar da Umar da Usman, kuma daga alamun sonsu gare su duka sun sawa ‘ya’yansu sunayensu domin tunawa da su, kamar yadda za mu fayyace a nan gaba a cikin wannan littafi, in Allah ya yarda. Kamar yadda sonsu da qaunarsu ga uwayen muminai ya shahara kuma suka sanya sunayensu ga xiyansu mata. Mai son ya tabbatar da wannan sai ya koma ga littafan Ahalus Sunna ingatattu, kamar Sahihul Bukhari da Sahihu Muslim da Kitabus Sunnana Abdullahi binu Ahmad binu Hanbal da Kitabus Sunna na Khallal da Kitabus Sunna na Ibnu Baxxata da Kitabus Sunna na Ajuri da Kitabus Sunna na Lalika’i da Kitabul Asma’iwas Sifat na Baihaqi da KitabFada’ilis Sahabah na Imam Ahmad da Albidaya walNihaya na Ibnu Kathir da Minhajus Sunnah na Ibnu Taimiya, da gomomi da xaruruwan littafan Hadisi da Tafsiri da Sirah waxanda suke tabbatar da kyawawan halaye na Ahalul Baiti da Sahabbai da soyayya da qauna da rahama da jin qai da ban girma dake tsakaninsu wanda yake tabbatar da cewa lallai tabbas su almajiran mafificin annabawa ne waxanda suka tsarkaka da koyarwarsa. Amma masu sukan Manzon Allah(SAW) ta hanyar sifanta manyan almajiransa da mabiyansa da sifofin ‘yan daba masu qin juna da qeta ga juna da wulaqanta juna, to muna roqon Allah ya turmuza hancinsu a qasa, ya maida musu da mugun nufinsu a kansu. Babi Na Uku Dangantaka da Serekuta Tsakanin Sahabbai Da Ahalul Baiti Allah ya halicci jinsin mutane kuma ya sanya ‘yan uwantakar xabi’a tsakaninsu imma ta hanyar dangantaka ko serekuta. Ubangiji Maxaukaki ya ce, “Kuma shi ne ya halicci mutum daga ruwa, sai ya sanya shi nasaba da surukuta, kuma Ubangijinka ya kasance mai ikon yi.”(Suratul Furqan: 54). Sa’an nan ya raba wannan jinsi zuwa dangogi da qabilu domin su san juna. Allah Maxaukaki ya ce, “Ya ku mutane! Lalle mun halitta ku daga namiji da mace, kuma muka sanya ku dangogi da qabiloli, domin ku san juna.”(Suratul Hujurat: 13). Wannan sanin juna a kansa ake dasa itaciyar dangantaka kuma da shi ake tabbatar da ‘yan uwantaka da soyayya ta xabi’a. Haka nan, Allah ya zavi dangin Larabawa daga jinsin mutane kuma ya zavi qabilar Quraishawa a cikin wannan dangi. Kuma har yau, ya zavi gidan Hashim daga qabilar Quraishawa, sa’an nan ya zavi Annabi Muhammad(SAW) daga wannan gida. Manzo(SAW) ya ce, “Lallai Allah ya zavi Kinanatu daga xiyan Isma’ilu, kuma ya zavi Quraishawa daga (zuri’ar) Kinanatu, kuma ya zavi xiyan Hashim daga Quraishawa, kuma ya zave ni daga xiyan Hashim.” Sai Annabi(SAW) ya zama zavavve daga cikin Zavavvu. Kuma har ila yau, ya zavi Sahabbai daga sauran qabilun Larabawa da gidajensu, ya sanya ‘yan uwantaka tsakaninsu da Annabinsa imma ta hanyar dangantakar jini ko ta serekuta. “Wannan falalar Allah ce, yana bayar da ita ga wanda ya so.”(Suratul Hadid: 21). Kuma da yake rahamar Allah tana da yalwa, bai taqaice wannan falala a kan Larabawa ba kawai, amma ya game ta ga wasu dangogin mutane da qabilu, ciki har da baqar fata, waxanda suka xarshe ta ta hanyar serekuta. Bayanin wannan falala, da kuma dangantaka da serekuta tsakanin Annabi(SAW) da mutanen gidansa da Sahabbansa shi ne jigon wannan babi. Qabilar Quraishawa Malaman dake darasun dangogin mutane sun kasa Larabawa na farko, waxanda suka rayu tun asubahin fari ta tarihi, zuwa gida biyu: Larabawan da suka shuxe (Al’arabul Ba’ida) da Larabawan Asali (Al’arabul Ariba). Larabawan da suka shuxe, kamar Adawa da Samudawa da Amaliqawa, tuni sun qare, babu ragowarsu kuma ba su bar baya ba. Larabawan Asali su ne waxanda zuri’o’insu suka wanzu zuwa yau. Su ma malamai sun kasa su zuwa gida biyu: Larabawan Asali da Larabawan da suka larabce (Al’arabul Musta’araba). Larabawan Asali su ne qabilun Qahaxaniyyawa waxanda suka zauni kudancin qasar Larabawa, ko wurin da aka sani da sunan Yaman. Su kuwa Larabawan da suka larabce su ne qabilun Adananawa waxanda suka zauni arewacin qasar Larabawa, ko Hijaz. An ce musu waxanda suka larabce saboda kakansu na farko, Annabi Isma’ilu(AS) xan Annabi Ibrahim(AS), ba na qasar Larabawa ba ne asalinsa amma ya zo daga qasar Sham ne inda ya zauni garin Makka kuma ya auri mace daga Larabawan Asali ya fari tasa zuri’ar. Quraishwa na daga cikin Larabawan da suka larabce, watau zuri’ar Annabi Isma’ilu(AS). Zavin Allah ya faxa kan Quraishawa, waxanda suke ba daga Larabawan Asali ba, saboda zavin ba a kan Larabcin aka gina shi ba, amma an gina shi ne a kan tushen annabta, kasancewar kakansu Annabi Ibrahim shugaban masu Tauhidi. Abinda aka sani ne a Shari’a cewa zavi da falala ba’a gina su a kan jinsi, qabila ko gida, amma ana gina su a kan imani da kyakkyawan aiki. Allah Maxaukaki ya ce, “Lalle ne Allah ya zavi Adamu da Nuhu da Gidan Ibrahimu da Gidan Imrana a kan talikai.”(Suratu Ali Imrana: 33). Kuma da ya ambaci annabawa su goma sha takwas a cikin Suratul An’am, sai ya ce, “Kuma daga ubanninsu da zuriyarsu, da ‘yan uwansu, kuma muka zave su, kuma muka shiryar da su zuwa ga hanya madaidaiciya.”(Suratul An’am: 87). Watau falalarsu ta kasance sakamakon zavin Allah da shiryar da su da ya yi zuwa imani da aikin qwarai. Shi ya sa a cikin aya ta gaba ya ce, “Wancan ne shiryarwar Allah, yana shiryar da wanda yake so daga bayinsa. Kuma da sun yi shirki da, haqiqa, abinda suka kasance suna aikatawa ya lalace.”(Suratul An’am: 88). An kira Quraishawa da sunan ubansu na farko, watau Nadir xan Kinana wanda ake wa laqabi da Quraishu. Malaman nasaba suna kasa wannan qabila zuwa gidaje goma sha biyu: 1. Gidan Hashim (Banu Hashim). Hashim shi ne kakan Annabi(SAW) na biyu. Ya bar garinsu Makka ya tafi Yathriba (Madina) inda ya auri wata mace mai suna Sulma daga Banun Najjar, xaya daga gidajen qabilar Khazraj mazaunan Madina. Sulma ta haifa masa xa, Shaiba, wanda aka yiwa laqabi da Abdulmuxxalib. Wannan shi ne kakan Annabi(SAW) na farko, watau uban mahaifinsa Abdullahi. Kuma ta kansa nasabar Annabi ta haxu da mutanen Madina kawunnansa. Banu Hashim su ne dangin Annabi makusanta kuma su ne ainihin Ahalul Baiti. 2. Banul Muxxalib. Muxxalib da Hashim ‘yan uwan juna ne, ubansu xaya, shi ne Abdu Munaf (sunansa na yanka Mugira). Lokacin da Hashim ya rasu, Muxxalib, wanda shi ne babba, ya xauko xan qaninsa, Shaiba, daga wajen dangin uwarsa a Madina ya raine shi. Yayin da ya shiga da shi garin Makka, alhalin yana matashi, sai mutanen Makka suka zaci bawa ne ya sayo, sai suka riqa kiransa Abdulmuxxalib. Zuri’ar gidan Muxxalib su suka fi kowa kusanci da Banu Hashim don haka su ma ake lasafta su cikin Ahalul Baiti. 3. Banu Abdis Shams ( ko kuma Banu Umayya). Abdus Shams ma xan Abdu Munaf ne (shi da Hashim tagwaye ne), kuma shi ne uban Umayya, kakan Umawiyyawa wanda gidan ya fi shahara da sunansa. Wannan gida yana da yawan dangi kuma suna da xaukaka qwarai a cikin Quraishawa. Wanda ya fi shahara a gidan shi ne Usman binu Affan, khalifar Annabi na uku kuma surukinsa mijin xiyansa biyu, Ruqayya da Ummu Kulthum. Sai Mu’awiya binu Abi Sufyan, Sarkin Musulmi kuma kakan khalifofin Banu Umayya, da Abul Aas binu Rabi, wanda shi ma surukin Annabi ne mijin babbar xiyarsa, Zainab. Manzo(SAW) ya auri xiyar wannan gida ita ce Ummu Habiba xiyar Abu Sufyana, ‘yar uwar Mu’awiya. Zuri’ar wannan gida su suka fi kowa yawan ma’aikata ga Annabi(SAW), watau gwamnoni da hakimai da ya naxa a garuruwa da nahiyoyi dabam-daban. 4. Banu Abduddari. Abduddari da Abdu Munaf ubansu xaya, shi ne Qusayyu binu Kilab. Daga cikinsu mashahurin sahabin nan ya fito, watau Mus’ab binu Umair, wanda ya tafi Madina ya share fage kafin Annabi(SAW) ya yi hijira zuwa can. Banu Abduddari su ne masu riqe da maqullan Ka’aba. 5. Banu Asad. Shi Asad jikan Qusayyu ne daga xansa Abduluzza. Daga cikinsu Zubairu binul Awwam ya fito, xaya daga Sahabbai goma da Annabi(SAW) ya yi musu albishir da aljanna. Mahaifiyarsa ita ce Safiyya xiyar Abdulmuxxalib, kakan Manzon Allah(SAW). Watau uwarsa goggon Annabi ce ke nan. Har yau kuma, daga Banu Asad ne Khadija ta fito, Innar Muminai matar Annabi(SAW) ta farko kuma uwar xiyarsa Faxima. A nan muna iya yin tambaya: Ya Zubairu yake da Faxima? Kuma ya mijinta, Ali, wanda shi ma Safiyya goggonsa ce, yake da Zubairu? Mai karatu zai tuna Zubairu binul Awwam(RA) na cikin Sahabban da ‘yan Shi’a suke zagi, suna la’anta, suna xaukan sa a matsayin wanda ya yi ridda wai saboda ya goyi bayan Innar Muminai A’isha a kan Ali a yaqin Jamal. 6. Banu Zuhura. Shi Zuhura xan uwan Qusayyu ne ubansu xaya. Daga zuri’arsa mahaifiyar Manzon Allah(SAW) ta fito, watau Amina xiyar Wahab xan Abdu Munaf xan Zuhura. Haka nan, manyan Sahabban nan, Abdurrahman binu Auf da Sa’ad binu Abi Waqqas, waxanda Rafilawa suke zagi suna kafirtawa, su ma daga wannan gidan suka fito. Don haka su kawunnan Annabi ne. A nan sai mu tambayi ‘yan Shi’a, waxanda suka yi vatan vakatantan, don me kuke zagin kawunnan Annabi(SAW) alhali kuna da’awar qaunar mutanen gidansa? 7. Banu Makhzum. Daga wannan gida Faxima xiyar Amru ta fito wacce ta auri Abdulmuxxalib kuma ta haifa masa xansa Abdullahi. Watau ita ce kakar Annabi mahaifiyar ubansa. Har yau, daga wannan gida matar Annabi, Innar Muminai Ummu Salma, ta fito wacce sunanta na yanka Hindu xiyar Abu Umayya. Mashahurin Sahabin nan, Arqam binu Abil Arqam, shi ma zuri’ar gidan ne. Arqam shi ne wanda Annabi(SAW) ya riqa koyar da Sahabbai a gidansa a voye a lokacin da yake kira zuwa Musulunci a sirri. 8. Banu Taim. Taimu da Makhzum ubansu xaya, shi ne Murra xan Ka’ab. Wanda ya fi kowa shahara a wannan gida shi ne Abubakar Siddiq, Sahabin Manzon Allah kuma khalifarsa na farko. Har yau, daga wannan gida Xalha binu Ubaidillah ya fito, wanda yana cikin Sahabbai goma da Annabi(SAW) ya yi musu albishir da aljanna. 9. Banu Adiy. Shi Adiyyu xan uwan Murra ne, ubansu xaya. Zakara a wannan gida shi ne Umar binul Khattab, Sahabin Annabi kuma khalifarsa na biyu. Daga cikin mashahurai a wannan gida har yau, akwai Sa’id binu Zaid, xaya daga cikin goma, da Zaid binul Khaxxab, xan uwan Umar wanda ya yi shahada a yaqin Yamama a zamanin Sarkin Musulmi Abubakar. 10. Banu Amir. Mashahurai a wannan gida sun haxa da Abdullahi binu Makhruma, ya halarci Badar, da Haxib binu Amru, ya musulunta tun Annabi na shiga gidan Arqam, da Abdullahi binu Ummi Makhtum, ladanin Annabi(SAW). 11. Banu Harith. Wannan zuri’a suna cikin Quraishawa da suka zauni bayan garin Makka. Mafi shahara a cikinsu shi ne Abu Ubaida Amir binul Jarrah. Annabi(SAW) ya kira shi amintaccen wannan al’umma kuma yana cikin goma da aka yiwa albishir da aljanna. Shi ne wanda rava-dannin shugaban ‘yan Shi’a na Nijeriya, Ibrahim Alzakzaki, yake yiwa shakiyanci, yana kiransa sakataren al’umma. 12. Banu Muharib. Muharib xan uwan Harith ne, ubansu xaya, kuma shi ma zuri’arsa sun zauna a bayan garin Makka. Daga cikinsu Dahhak binu Qais da Habib binu Maslama suka fito. Sahabbai ne masu daraja. Waxannan su ne gidaje goma sha biyu na Quraishawa. Kuma mai karatu yana iya gani cewa xiyan waxan nan gidaje, waxanda ga asali duka ubansu guda ne, sun cuxu da juna ta hanyar dangantaka da auratayya a tsawon xaruruwan shekaru ta yadda ba wani gidan da ba shi da alaqa da wani. Banda kasancewarsu duka suna zaune a wuri xaya: Makka da kewayenta. Wannan ma dole ya qara danqon zumunta a tsakaninsu. Idan aka dubi yadda Larabawa suke kulawa da nasaba, suna haddace ta, saboda haka suna sane da cewa tushensu xaya ne, ba ta yiwuwa a ce gaba da qiyayya ta wanzu a tsakanin waxan nan gidaje, musamman bayan Musulunci ya qara danqon zumunta a tsakaninsu, kamar yadda ‘yan Shi’a ma’abota jahilci suke riyawa. Qabilu uku ne yawancin Sahabbai da Ahalul Baiti suka fito a cikinsu. Su ne Quraishawa na Makka, waxanda mai karatu ya ga dangantaka da danqon zumuncin dake tsakaninsu, sai kuma Ausu da Khazraj mazaunan Madina. Waxannan su ne a game ake cewa Muhajiruna da Ansar, waxanda su ne Musulmin farko. Dangane da Quraishawa, mai karatu ya ga matsayin Ahalul Baiti a cikinsu da yadda nasabarsu ta sarqe da juna. Dangane da Ausu da Khazraj kuwa, waxanda su ma ubansu guda ne, mai karatu ya ga yadda nasabar Annabi(SAW) ta haxu da tasu ta hanyar kakarsa Sulma, uwar Abdulmuxxalib, wacce ta fito daga Banun Najjar wanda gida ne na qabilar Khazraj. Saboda haka, ba wanda zai kitsa irin wannan qarya ta ‘yan Shi’a, ko ya yarda da ita, cewa wai gaba da qiyayya ta wanzu tsakanin waxan nan ‘yan uwa, musamman bayan hasken Musulunci ya shiga zukatansu kuma tarbiyyar Annabi(SAW) ta ratsa su, sai baqin jahili daqiqi ko munafuki (kafiri a zuci) wanda yake so ya soki Annabi(SAW) ta hanyar sukan manyan almajiransa. Nasaba Da Auratayyar Quraishawa Bayan bayani da muka gabatar a dunqule wanda yake tabbatar da dangantaka da auratayya a tsakanin Ahalul Baiti da Sahabbai, a yanzu za mu zavi wasu fitattu daga cikinsu, a matsayin misali, mu ba da tarihinsu a taqaice tare da bayanin nasaba da auratayyarsu domin fayyace abinda muka dunqule a sama. Amma bari mu fara da shugabansu, malaminsu, abin koyinsu, Annabi Muhammad, tsira da aminci su tabbata a gare shi. Nasaba Da Auratayyar Annabi(SAW) Shi ne shugaban halitta, cikamakin annabawa, wanda Allah ya aiko shi domin rahama ga talikai, Muhammad xan Abdullahi xan Abdulmuxxalib xan Hashim xan Abdu Munaf xan Qusayyu xan Kilab xan Murra xan Ka’ab xan Lu’ayyu xan Galib xan Fihiru xan Malik xan Nadir xan Kinana xan Khuzaima xan Mudurika xan Ilyas xan Mular xan Nizar xan Mu’addu xan Adananu. Wannan shi ne jerin kakannin Annabi(SAW) wanda malaman Hadisi da Tarihi suka haxu a kai. Amma abinda ya yi sama daga nan, to akwai savani a kansa tsakanin malamai. Sai dai duka sun haxu a kan cewa nasabarsa tana haxewa da Annabi Isma’il xan Annabi Ibrahimu Badaxayin Allah, tsira da aminci su tabbata a gare su. Game da dangantaka, babu wani Sahabi daga manyan Sahabbai Muhajiruna da Ansar wanda nasabarsa ba ta game da ta Annabi ba, daga kusa ko daga nesa. Amma idan muka koma ga serekuta, Annabi(SAW) ya auri mata masu yawa, kamar yadda aka sani, kuma ya aurar. Ya aurar da Zainab, babbar xiyarsa, ga Abul Aas binu Rabi daga Banu Umayya, kuma ta haifa masa xiya, Umamtu. (Abul Aas mahaifiyarsa, Halatu xiyar Khuwailid, ‘yar uwar Innar Muminai Khadija ce.) Sa’an nan ya aurar da Ruqayya ga Usman, shi ma daga Banu Umayya, ta haifa masa xa, Abdullahi, wanda ya rasu yana yaro. Sa’an nan da Ruqayya ta rasu a xakin Usman ya aura masa qanuwarta, Ummu Kulthum. Kamar yadda ya aurar da Faxima, ‘yar autar ‘ya’yansa mata, ga Ali binu Abi Xalib. Wannan yana nufin Annabi(SAW) ya aurar da xiyansa mata uku ga ‘ya’yan zuri’ar Banu Umayya, kuma ya aurar da guda kawai a cikin danginsa mafi kusa, Banu Hashim, Ahalul Baiti. Tare da wannan duka, ‘yan Shi’a ma’abota jahilci waxanda suka yi vatan vakatantan, suna matuqar gaba da ‘ya’yan gidan Banu Umayya, suna zagin su kuma suna kafirta su, duk da cewa Manzo(SAW) ya nuna musu qauna kuma ya girmama su ta hanyar yin serekuta da su. Idan muka koma ga matan da Annabi(SAW) ya aura, za mu ga cewa ya auri mata goma sha xaya kuma ya yi qwarqwara guda. A nan qasa mun shimfixa bayani a taqaice na matan nasa. 1. Khadija xiyar Khuwailid(RA) Innar Muminai Khadija xiyar Khuwailid xan Asad ita ce matar Annabi ta farko. Manzo(SAW) ya aure ta tana bazawara. Kafinsa, ta auri Abu Hala binu Nabash binu Zurara ta haifa masa ‘ya’ya biyu: Hala da Hindu. Sa’an nan ta auri Atiqu binu Aabid binu Amru binu Makhzum. Shi ma ta haifa masa xa guda. Khadija ta fito daga zuri’ar Banu Asad. Annabi(SAW) ya auri Khadija tana da shekaru arba’in a duniya, shi kuma yana da ishirin da biyar. Ta haifa masa ‘ya’yansa dukkaninsu in banda Ibrahim wanda Mariya ta haifa. ‘Ya’yan su ne: Alqasim, shi ne babban xan Annabi wanda ake masa alkunya da shi, sai Zainab, sai Ruqayya, sai Ummu Kulthum, sai Faxima wacce ita ce ‘yar auta a xiyansa mata. Duka waxan nan an haife su a Makka kafin Musulunci. Sai Abdullahi wanda aka haifa a Musulunci don haka ake masa laqabi da Axxahir Axxayyib. ‘Ya’yan Annabi(SAW) duka sun rasu a rayuwarsa, in banda Faxima wacce ta rasu kimanin wata shida bayan rasuwarsa. Alqasim shi ne ya fara rasuwa yana jariri. Zainab ta rasu bayan ta yi aure ta haihu. Ruqayya ma ta haihu kafin rasuwarta. Ummu Kulthum ta yi aure amma ba ta haihu ba. Khadija ta rasu a Makka shekaru huxu kafin hijirar Manzon Allah zuwa Madina. Annabi(SAW) ya kira shekarar rasuwarta Amal Huzni, watau shekarar baqin ciki. 2. Sauda xiyar Zam’a(RA) Matar Annabi(SAW) ta biyu, Sauda xiyar Zam’a xan Qais ta fito daga gidan Banu Amir. Ta musulunta da wuri, tare da mijinta na farko Sakaran binu Amru na gidan Banu Umayya. Sun yi hijira zuwa Habasha tare kuma bayan komowarsu sai mijin ya rasu. A wannan lokaci Sauda ta manyanta kuma babu mai riqe ta saboda Musulunci ya raba ta da yawancin danginta. Sai Manzon Allah(SAW) ya aure ta tana da shekaru hamsin da biyar a duniya. Bayan hijira zuwa Madina da aurarraki da Annabi ya yi, Sauda ta barwa A’isha kwananta don ra’in kanta, amma ta ci gaba da zama a matsayinta na Innar Muminai har zuwa qarshen rayuwarta. Ta rasu a zamanin Sarkin Musulmi Umar binul Khaxxabi(RA). 3. A’isha xiyar Abubakar(RA) Ita ce mace ta uku da Annabi(SAW) ya aura bayan Khadija da Sauda, kuma ita kaxai ce budurwa a cikin matan da Manzo ya aura a rayuwarsa. Ya aure ta a Makka tana da shekara shida kuma ya tare da ita a Madina tana da shekaru tara. Manzon Allah(SAW) ya so A’isha ainun saboda kusancinsa da ubanta. Kasancewarta tana qaramar yarinya a lokacin, wannan ya ba ta damar xaukar ilmi mai yawa daga Annabi, inda ta ruwaito hadisai masu yawa da gaske. Tana daga cikin Sahabbai biyar da suka fi yawan ruwaya. A’isha ta rasu a Madina, a cikin watan Ramadan, shekara ta 58 bayan hijira, tana ‘yar shekara sittin da shida. Abu Huraira ne ya sallace ta kuma an yi jana’izarta bayan sallar ashan. 4. Hafsa xiyar Umar(RA) An haifi Hafsa shekaru biyar kafin aiken Annabi(SAW). Mijinta na farko shi ne Khunaisu binu Huzafa binu Qais. Ta yi hijira tare da mijinta zuwa Madina amma sai ya rasu bayan yaqin Badar. Hafsa, kamar sauran matan Annabi, salihar mace ce mai yawan azumi da sallah. Yayin da Sarkin Musulmi Abubakar Siddiqu ya tattara Alqur’ani a karon farko, a farkon khilafarsa, an ajiye shi a wajenta har lokacin da Sarkin Musulmi Usman binu Affan ya karve shi ya yi kofe-kofe zuwa biranen Musulmi. Hafsatu ta rasu a cikin watan Sha’aban, shekara ta 45 bayan hijira, tana da shekaru sittin a duniya. 5. Zainab xiyar Khuzaima(RA) Zainab ta fito daga zuri’ar Banu Hilal, kuma ta kasance ana yi mata laqabi da Ummul Masakin (uwar miskinai) saboda taimakon musakai da take yi. Maza biyu sun aure ta kafin Annabi(SAW). Na farko shi ne Xufail binu Harith binu Muxxalib wanda ya sake ta. Bayan nan, xan uwan mijinta, Ubaida binu Harith, ya aure ta. Shi kuma ya yi shahada a Yaqin Badar. Sa’an nan, sai Annabi(SAW) ya aure ta a cikin watan Ramadan, shekara ta uku bayan hijira. Ta rayu tare da Annabi wata takwas kawai Allah ya yi mata rasuwa. Ita ce matar Annabi ta biyu, kuma ta qarshe, da ta mutu a zamanin rayuwarsa. Manzo ne ya sallace ta kuma aka bunne ta a maqabartar Baqi’a. Ta bar duniya tana da shekaru talatin. 6. Ummu Salma xiyar Abu Umayya(RA) Sunanta na yanka Hindu xiyar Abu Umayya xan Mugira na gidan Banu Makhzum. Mahaifiyarta ita ce Atika xiyar Abdulmuxxalib, goggon Annabi(SAW). Ta musulunta da wuri tare da mijinta na fari Abu Salma (sunansa Abdullahi) binu Abdil Asad na gidan Makhzum, kuma sun yi hijira zuwa Habasha tare. Ta haifa masa Zainab da Salma da Amru. Mijinta ya rasu sakamakon rauni da ya ji a yaqin Uhudu. Saboda haka sai Ma’aikin Allah(SAW) ya aure ta. Ta rasu a cikin watan Zul Qida, shekara ta 59 bayan hijira, tana da shekaru tamanin da huxu. Abu Huraira ne ya sallace ta, aka bunne ta a maqabartar Baqi’a. 7. Zainab xiyar Jahash(RA) Zainab xiyar Jahash xan Riyab daga Banu Asad binu Khuzaima, mahaifiyarta ita ce Umaima xiyar Abdulmuxxalib, goggon Annabi(SAW). Zaidu binu Haritha, bawan Annabi da ya ‘yanta, shi ya fara auren ta, sa’an nan ya sake ta. Ma’aiki(SAW) ya aure ta kuma da wannan aure Allah ya soke al’adar Jahiliyya ta hana auren matar da xan riqo ya aura ya saki, domin shi Zaidu bayan da Annabi ya ‘yan ta shi ya mayar da shi xan riqo (watau ya yi tabanni da shi) aka riqa kiran sa Zaidu binu Muhammad. Izuwa wannan ne Allah Maxaukaki ya ke nuni da faxinsa, “To a lokacin da Zaidu ya qare buqatarsa daga gare ta, mun aurar da kai ita, domin kada wani qunci ya kasance a kan muminai a cikin (auren matan) xiyan hankakarsu, idan sun qare buqata daga gare su.” (Suratul Ahzab: 37). Zaidu shi kaxai ne Sahabi da aka ambaci sunansa quru-quru a cikin Al’qur’ani. Shi ya sa Zainab xiyar Jahash ta zama tana alfahari ga matan Annabi(SAW), tana cewa, “Ku iyayenku suka aurar da ku, ni kuwa Allah ne ya aurar da ni daga kan saman bakwai.” Ta rasu tana da shekaru hamsin da uku a duniya, a shekarar hijira ta 20, zamanin Sarkin Musulmi Umar xan Khaxxabi, wanda shi ya sallace ta. 8. Juwairiyya xiyar Harith(RA) Juwairiyya xiyar Harith xan Abu Dirar xan Habib xan Juzaima ta fito daga Banul Musxaliq, wani reshe na Banu Khuza’a. Mahaifinta Harith da mijinta na farko Musafih binu Safwan shugabanni ne a cikin wannan qabilar. Qabilar tana da qarfi ainun kuma ta nuna matuqar adawa ga Musulunci. Lokacin da Allah ya ba Musulmi galaba a kanta, a yaqin da aka fi sani da Gazawatu Banil Musxaliq, an kashe mijin Juwairiyya da ubanta kuma aka kame da yawa daga cikin ‘yan qabilarta maza da mata a matsayin ganima, ciki har da ita kanta. Bayan da Ma’aiki(SAW) ya raba ganima, Juwairiyya ta faxa a rabon Thabit binu Qais wanda ya yi mata mukataba, watau ya ba ta dama ta fanshi kanta. Sai ta zo wurin Annabi(SAW) ta yi masa bayanin kanta da matsayinta a cikin mutanenta. Sai Manzo(SAW) ya biya fansarta, sa’an nan ya aure ta. Kuma wannan aure ya zama alheri ga Musulunci; domin lokacin da labarinsa ya watsu sai dukkanin Sahabbai suka ‘yanta waxanda suke hannunsu daga mutanenta. Suka ce ba za mu bautar da surukan Annabi ba. Wannan karamci da Ma’aiki ya nuna tare da Sahabbansa ya faranta ran ‘yan qabilar Banul Musxaliq, don haka sai suka shiga Musulunci baki xayansu, kuma gabar da take tsakaninsu da Musulmi ta juye ta zama ‘yan uwantaka da soyayya. Annabi(SAW) ya auri Juwairiyya a shekara ta biyar bayan hijira kuma ta rasu a shekara ta 56, tana da shekaru hamsin da shida a duniya. Marwan Binul Hakam, gwamnan Madina a zamanin Sarkin Musulmi Mu’awiyya, shi ya sallace ta. 9. Safiyya xiyar Huyayyu(RA) Safiyya xiyar Huyayyu xan Akhxab ta fito daga qabilun Yahudawan Madina. Lokacin da Annabi(SAW) ya yi hijira, akwai gidaje uku fitattu na Yahudawa a Madina. Su ne Banu Qainuqa’a da Banu Quraiza da Banu Nadir. Safiyya ta fito daga Banu Quraiza. Da isowar Ma’aikin Allah(SAW) Madina ya qulla yarjejeniyar zaman lafiya da waxannan Yahudawa, amma sai suka karya yarjejeniyar kuma suka sava alqawari. Don haka Annabi(SAW) ya fitar da su daga Madina, sai suka koma wajen ‘yan uwansu a Khaibar, inda suka ci gaba da qullawa Musulunci maqarqashiya da makirci. Wannan ya sa a shekara ta bakwai bayan hijira, Annabi(SAW) ya yaqe su kuma ya yi galaba a kansu a mashahuriyar gwabzawar da ake cewa Yaqin Khaibar. A wannan yaqin aka kashe mijin Safiyya kuma aka kame ta a matsayin ganima. Da aka raba ganima sai ta faxa a rabon Dahiyya binu Khalifa Alkalbi, amma kasancewarta xiyar shugaba ce kuma matar shugaba, sai Manzo(SAW) ya saye ta daga wajen Dahiyya, ya ‘yanta ta kuma ya aure ta a matsayin wata hikima ta siyasa domin ya jawo hankalin danginta su shiga Musulunci. Kafin Ma’aikin Allah, Safiyya ta auri mazaje biyu: Salam binu Mishkan Alkhuza’i, wanda ya sake ta, da Rabi’u binu Abil Haqiq Alnadiri wanda aka kashe shi yana tare da ita. Wannan aure ya haxa dangantaka tsakanin Annabi(SAW) da qabilun Yahudawa na qasar Larabawa kamar yadda ya rage kaifin qiyayya tsakanin Yahudu da Musulmi. Safiyya, Allah ya qara mata yarda, ta rasu a shekara ta 52 bayan hijira a Madina. 10.Ummu Habiba xiyar Abu Sufyan(RA) Sunanta Ramla xiyar Abu Sufyan xan Harbu xan Umayya na gidan Banu Umayya. Mahaifiyarta, Safiyya xiyar Abul As xan Umayya, goggon Sarkin Musulmi Usman binu Affan ce. Mijinta na fari shi ne Ubaidullahi binu Jahash, kuma ta haifa masa xiya, Habiba. Ubaidullahi ya musulunta tare da matarsa kuma ya yi hijira da ita zuwa Habasha. Amma a yayin da suke can, sai ya yi ridda ya shiga addinin Nasara, ita kuwa Ummu Habiba ta tabbata a kan Musuluncinta. Wannan dalili ya raba su aure. Lokacin da Annabi(SAW) ya ji labari, sai ya aike wajen Sarkin Habasha, Najashi, ya umarce shi da ya aura masa ita. Najashi ya xaura auren, ya ba Ummu Habiba sadaki dinare xari huxu. Mai karatu zai tuna cewa Najashi ya musulunta kuma shi ne a lokacin da ya rasu, Annabi(SAW) ya yi masa sallah daga nesa (salatul ga’ib) a Madina. A lokacin da Ma’aiki(SAW) ya auri Ummu Habiba, ubanta Abu Sufyan shi ne yake jagorantar mushirikan Makka a yaqinsu da Musulunci. Uban nata ya zo Madina a wani yunquri na neman sulhu jim kaxan kafin Annabi(SAW) ya ci Makka, kuma ya shiga wajen xiyarsa don ya gaisa da ita. Lokacin da ya so ya zauna kan shimfixar Annabi(SAW), Ummu Habiba ta yi wuf ta janye shimfixar, ta faxa masa cewa shi mushiriki ne don haka bai kamata ya zauna bisa shimfixar Annabi. Ummu Habiba, Allah ya qara mata yarda, ta rasu a shekara ta 44 bayan hijira, a zamanin khilafar Mu’awiyya xan uwanta. 11. Maimuna xiyar Harith(RA) Maimuna xiyar Harith ‘yar dangi ce daga gidan Banu Hilal. ‘Yar uwa ce ga Ummul Falali Lubabatu xiyar Harith matar Abbas xan Adbulmuxxalib, baffan Annabi(SAW), da Asma’u xiyar Umais (wacce suka haxa uwa) matar Ja’afar binu Abi Xalib, xan uwan Ali binu Abi Xalib, Allah ya yarda da su baki xaya. (Bayan rasuwar Ja’afar, Asma’u ta auri Abubakar Siddiq kuma bayan rasuwarsa ta auri Ali, kuma duka ta haifa musu ‘ya’ya, kamar yadda za mu gani.) Maimuna ta auri maza biyu kafin Annabi(SAW). Ta auri Mas’ud binu Amru binu Umair Althaqafi a zamanin Jahiliyya, ya rabu da ita. Sai ta auri Abu Ruhum binu Abdil Uzza wanda ya rasu ta yi masa takaba. Lokacin da Ma’aiki(SAW) ya zo Makka domin yin umrar ramuwa bayan Sulhun Hudaibiyya, a shekara ta bakwai bayan hijira, ya iske Maimuna, wacce tana cikin waxanda suka musulunta da wuri, a cikin halin rashin miji kuma ga gallazawar ‘yan uwa saboda musuluncinta. Don haka sai Annabin Rahama(SAW) ya aure ta, domin gata da rufin asiri a gareta. Wannan auren ya ceci wannan baiwar Allah kuma ya faranta ran danginta waxanda suka ga karamcin Annabi(SAW) a fili. Maimuna ita ce mace ta qarshe da Annabi(SAW) ya aura. Ta rasu a shekara ta 61 bayan hijira, a kan hanyarta ta komowa daga Hajji, kuma xan ‘yar uwarta ne da yake rakiyarta, Abdullahi binu Abbas, ya sallace ta. Banda waxan nan mata goma sha xaya na aure, Ma’aiki(SAW) ya yi sa-xaka da mace guda ita ce Mariya Alqibxiyya, wacce ta haifa masa xansa Ibrahim wanda ya rasu yana qarami. Kuma da wannan qwarqwara ne falalar dangantaka da Annabi(SAW) ta hanyar serekuta ta yi naso zuwa ga al’ummar baqar fatar duniya. Domin Mariya Alqibxiyya, kamar yadda sunanta yake nunawa, baqibxiya ce ta fito daga qabilar Qibxawa baqar fata mazaunan qasar Misira na asali. Sarkin Misira, Muqauqis, ne ya baiwa Annabi kyautarta tare da ‘yar uwarta Sabrina, bayan da Manzo(SAW) ya aike masa da takarda yana kiran sa zuwa Musulunci. Sai Annabi(SAW) ya yi sa-xaka da ita kuma ya bayar da ‘yar uwarta ga Hassaan binu Thabit. A sakamakon wannan dangantaka Manzon Allah(SAW) ya yi wasiyya da mutanen Misira. Ummu Salma(RA) ta ruwaito cewa, Annabi(SAW) ya yi wasiyya ga al’umma a lokacin rasuwarsa, ya ce, “Ina gam muku da Allah dangane da Qibxawan Misira. Lallai ku da sannu za ku yi rinjaye a kansu, kuma za su zame muku tattali da taimako wajen xaukaka addinin Allah.” A wani hadisin kuma ya ce, “Lallai ku za ku buxe Misira (watau za ku ci ta da yaqi), kuma ita qasa ce da ake ambaton qiraxi a cikinta. Idan kuka buxe ta, to ku kyautata wa mutanenta domin lallai su suna da alqawari da zumunta.” Ko kuma cewa ya yi, “alqawari da serekuta.” Malamai suka ce zumunta saboda Hajaru uwar Annabi Isma’il(AS) daga cikinsu take, serekuta kuma saboda Mariya Alqibxiyya. Koda yake dangantakar baqaqen fata da Annabi(SAW) da Musulunci ba ta tsaya a kan Hajaru da Mariya ba kawai. Akwai Ummu Aiman (sunanta Baraka), baiwa ce ta mahaifin Annabi, Abdullahi, Manzon Allah(SAW) ya gaje ta daga mahaifinsa kuma ita ce ta yi rainon sa. Daga bisani, Ma’aiki(SAW) ya ‘yanta ta kuma ‘yantaccen bawansa, Zaidu binu Haritha, ya aure ta, ta haifa masa xansa Usama. Ummu Aiman an sifanta ta da cewa baqa ce qirin, kuma Manzo(SAW) ya kasance yana kiran ta da Ummata, kamar yadda ya yi mata albishir da aljanna. Har yau kuma, akwai Bilal binu Rabah, ladanin Annabi(SAW). Shi ma baqi ne bahabashe, ya musulunta da wuri a Makka kuma ya jure baqar azaba a kan Musuluncinsa. Abubakar(RA) ne ya saye shi ya ‘yanta shi, kuma Annabi(SAW) ya yi masa albishir da aljanna. Haka nan, akwai Najashi, sarkin Habasha, wanda ya karvi baquncin manya-manyan Sahabbai na farko masu gudun hijira a qasarsa har sau biyu. Shi ma baqi ne, ya musulunta, kuma a lokacin da ya rasu Annabi(SAW) ya yi masa sallah daga nesa (salatul ga’ib) a Madina. Wannan duka yana nuna matsayin mu, mu jinsin baqar fata, a Musulunci, cewa ba shigege muka yi ba, amma da mu aka fara. Kuma wannan ita ce baqar fatar da ya kamata a yi alfahari da ita, ba baqar fatar Afirka ta Kudu ba ko Jameka. Abin nufi a nan shi ne bayanin yadda dangantaka da auratayya ta sarqe tsakanin shugaban Ahalul Baiti shi da kansa, watau Annabi(SAW), da mutanen gidansa da kuma sauran Sahabbai na qabilu da hauloli dabam-daban na Larabawa har da wasunsu. Nasaba Da Auratayyar Abubakar Siddiq(RA) Shi ne Abubakar (sunansa na yanka Abdullahi) xan Abu Quhafa (sunansa Usman) xan Amir xan Amru xan Ka’ab xan Sa’ad xan Taimu xan Murra xan Ka’ab xan Lu’ayyu xan Galib xan Fihiru. Ya fito daga gidan Banu Taim. Nasabarsa tana haxewa da Annabi(SAW) a kan kakansa na shida, Murra xan Ka’ab. Abubakar shi ne farkon wanda ya musulunta a cikin mazaje (manya) kamar yadda Khadija ita ce farkon Musulma mace, Ali binu Abi Xalib kuma shi ne farkon wanda ya musulunta a yara. Abubakar shi ne mafi girma a cikin Sahabban Annabi(SAW) kuma mafi soyuwa gare shi. Ya lizimci Manzo a tsawon rayuwarsa, ya halarci dukkan yaqoqa tare da Annabi(SAW) kuma ya ciyar da dukiyarsa wajen yaxa Musulunci. Ya aurawa Annabi(SAW) xiyarsa A’isha(RA) kuma ya zama khalifarsa na farko. A zamanin khalifancinsa, ya yi maganin ‘yan ridda, inda ya yaqe su har sai da ya mayar da qasar Larabawa duka qarqashin hukuncin Musulunci kamar yadda Annabi(SAW) ya bar ta, kuma ya fara cin wasu sabbin qasashe. Abubakar ya rasu a shekara ta 13 bayan hijira, yana xan shekara sittin da uku a duniya, kuma an bunne shi kusa da Annabi(SAW) a xakin xiyarsa A’isha. Abubakar(RA) ya auri mata da dama. Waxanda suka shahara a cikinsu sun haxa da: 1. Ummu Ruman xiyar Amir wacce ta haifa masa A’isha Innar Muminai matar Manzo(SAW) da Abdurrahman. 2. Asma’u xiyar Umais xan Ma’ad xan Taim wacce ta haifa masa xansa Muhammad wanda Ali binu Abi Xalib ya raine shi. Asma’u xiyar Umais ta auri manyan Sahabbai uku, biyu daga cikinsu Ahalul Baiti, kuma duka ta haifa musu ‘ya’ya. Da farko ta auri Ja’afar binu Abi Xalib, xan uwan Ali, ta haifa masa Aunu da Muhammad da Abdullahi. Bayan Ja’afar ya yi shahada a yaqin Mu’uta a zamanin rayuwar Annabi(SAW), sai ta auri Abubakar ta haifa masa xa wanda ya kira shi Muhammad. Bayan rasuwar Abubakar kuma, Asma’u ta auri Ali binu Abi Xalib ta haifa masa ‘ya’ya biyu: Yahaya da Aunu. Ta je gidan Ali da Muhammad binu Abubakar a matsayin agola kuma Ali ya raine shi. Muhammad ya zauna a gidan Ali har lokacin da ya zama khalifa. Ya goyi bayan Ali a rikicinsa da Mu’awiyya, haka nan a yaqin Jamal tsakaninsa da Xalha da Zubairu. Don haka Ali(RA) ya naxa shi a matsayin gwamnansa na Misira. A nan sai mu tambayi maqaryata, ma’abota jahilci, masu cewa akwai gaba da qiyayya a tsakanin Abubakar da Ali: Ya za su yi da wannan haqiqa ta tarihi? Ga Ali ya auri matar Abubakar, wacce a da ta auri xan uwansa Ja’afar, kuma ya raini xansa Muhammad wanda ya ci gaba da zama tare da shi har girmansa, kuma ya zama amintaccensa, mai goyon bayansa, har ya naxa shi gwamna a zananin khalifancinsa. Babu shakka wannan yana rushe qaryar ‘yan Shi’a, yana tona asirin jahilcinsu ko mummunar manufarsu, kuma ya isa ya sa su kunya in da suna da kunya. Bugu da qari, Muhammad xan Abubakar shi ya haifi Qasim wanda ya haifi Ummu Farwa mahaifiyar Ja’afar Sadiq, imamin Shi’a na shida, kamar yadda za mu gani a nan gaba in Allah ya yarda. Banda waxannan mata biyu, Abubakar ya auri Habiba xiyar Harija binu Yazid Ba’ansare da Futailatu ta Banu Amir. Nasaba Da Serekutar Umar binul Khaxxab(RA) Shi ne Umar xan Khaxxabi xan Nufail xan Abdul Uzza xan Rayah xan Abdullahi xan Qurxi xan Razahi xan Adiyyu xan Ka’abu xan Luayyu xan Galib xan Fihiru. Ya fito daga gidan Banu Adiyy. Nasabarsa na haxewa da Annabi(SAW) a kan kakansa na bakwai, Adiyyu xan Ka’abu. Umar yana cikin Musulmin farko; ya musulunta a lokacin da Annabi(SAW) yake gidan Arqam. Allah ya xaukaka addini da musuluntarsa, a yayinda Musulmi suka numfasa kuma suka fito fili suka nuna addininsu a Makka. Ya lizimci Annabi(SAW) a tsawon rayuwarsa, ya halarci dukkan yaqoqa tare da shi kuma ya sadaukar da rayuwarsa da duk abinda ya mallaka wajen yaxa addinin Musulunci. Ya aurawa Annabi(SAW) xiyarsa Hafsa(RA) kuma ya zama khalifansa na biyu bayan Abubakar. Sarkin Musulmi Umar gwarzon namiji ne wanda ya jagoranci rundunonin Musulunci wajen rusa daulolin Farisa da Rum. Ya cinye qasashen Iraqi da Farisa da Sham da Misira da wasunsu. Ya kafa durakun daular Musulunci, ya assasa tsare-tsaren mulki masu qaye kuma ya shimfixa adalci. Umar ya yi shahada a shekara ta 24 bayan hijira, yana da shekaru sittin a duniya. Abu Lu’uluatal Majusi, wanda bamajusen Farisa ne aka kamo shi a yaqi yake zaman bauta a Madina, shi ne ya kashe shi domin xaukar fansar rushe daular Majusawan Farisa da Khalifan ya yi. Wannan bamajuse a yau yana da hubbare a qasar Iran wacce ‘yan Shi’a daga ko ina a duniya suke ziyarta domin girmamawa. Umar ya auri mata da dama. Sun haxa da: 1. Zainab xiyar Maz’un xan Habib, ‘yar uwar mashahurin Sahabin nan Usmanu binu Maz’un, ta haifa masa Hafsa Innar Muminai matar Manzon Allah(SAW), da Abdullahi. Waxannan su suka fi shahara cikin xiyan Umar. 2. Ummu Kulthum xiyar Ali da Faxima, ta haifa masa Zaid da Ruqayya. Watau Umar ya aurawa Annabi(SAW) xiya kuma ya auri jikanyar Manzon Allah(SAW). Wannan auratayya da ta je ta zo tsakanin Umar da Ma’aiki, tana nuna dangantaka tsakanin Banu Adiyy, dangin Umar, da Ahalul Baiti. Kuma koda yake ma’abota jahilci, masu vatan vakatantan, suna cewa qwatar Ummu Kulthum Umar ya yi, amma duk mai hankali da addini ya san Sahabin Annabi bai qwatar mace ya zauna da ita ta haifa masa ‘ya’ya, koda yana iya yin hakan, kamar yadda ya san cewa ba’a iya qwatar xiyar Ali(RA) koda qwacen ya zama al’ada a tsakaninsu. Saboda haka, Ali(RA) ya aurawa Umar(RA) xiyarsa Ummu Kulthum a kan yardarsa da son ransa, saboda soyayya da qauna da ban girma dake tsakaninsu. Kuma mene ne abin mamaki idan Ali ya aurawa Umar xiyarsa? Shin Annabi(SAW) bai auri xiyar Umar ba? Bayan rasuwar Umar, Ummu Kulthum ta auri Aunu xan Ja’afar binu Abi Xalib, ya rasu ta yi masa takaba. Bayan rasuwarsa, ta auri xan uwansa, Muhammad xan Ja’afar binu Abi Xalib, shi ma ya rasu ta yi masa takaba. Sa’an nan ta auri xan uwansa har yau Abdullahi xan Ja’afar binu Abi Xalib wanda ta rasu a gidansa. Banda waxan nan mata biyu, Umar ya auri wasu mata da dama, kamar Ummu Hakim xiyar Harith ta Banu Makhzum da Jamila xiyar Thabit Ba’ansariya da Atika xiyar Zaid. Nasaba Da Serekutar Usman binu Affan(RA) Shi ne Usmanu xan Affan xan Abul Aas xan Umayya xan Abdu Shams xan Abdu Munaf xan Qusayyu. Ya fito daga gidan Banu Umayya kuma nasabarsa na haxewa da Annabi(SAW) a kan kakansa na huxu. A cikin khalifofi huxu, banda Ali, Usmanu ya fi kusa da Annabi(SAW). Mahaifiyarsa, Arwa xiyar Ummu Hakim ce xiyar Abdulmuxxalib. Watau kakarsa ta wajen uwa goggon Annabi ce, ita da mahaifin Annabi, Abdullahi, ba wai kawai shaqiqai suke ba, a’a tagwaye ne kuma. Don haka mahaifiyarsa imma ya ce ko qanuwa ga Annabi(SAW); shi kuma xa ne a wajen Annabi(SAW). Usmanu na daga cikin waxanda Abubakar ya kira zuwa Musulunci, kuma ya musulunta da wuri tun kafin Manzo(SAW) ya shiga gidan Arqam. Usmanu xan dangi ne kuma babban attajiri wanda ya shahara da kyawawan halaye kamar kunya da kamun kai da yawan kyauta. Ya lizimci Annabi(SAW) a tsawon rayuwarsa kuma ya halarci yaqoqa duka tare da Annabi banda Badar; bai je ba saboda yana jiyar matarsa Ruqayya da umarnin Annabi(SAW). Don haka, Manzo(SAW) ya raba ganimar yaqin da shi. Ya ciyar da dukiya mai yawa wajen xaukaka addinin Allah. Usmanu binu Affan(RA) ya auri xiyan Annabi(SAW) guda biyu: ya auri Ruqayya wacce ta haifa masa Abdullahi, kuma bayan ta rasu ya auri qanuwarta Ummu Kulthum. Don haka ake masa laqabi da Zul Nuraini, mai haske biyu. Wannan falala a duniya ba’a tava samun mai irinta ba sai Usmanu. Sarkin Musulmi Usmanu ya zama khalifa na uku bayan Umar, kuma a zamaninsa Allah ya yi buxin arziqi ga al’ummar Musulmi wanda ya raba shi da adalci. Usmanu ya ci gaba da buxe qasashe wanda Umar ya fara, kuma a qarqashin mulkinsa Musulunci ya dangana da Indiya, qasar Sin da Ifriqiyya. Usmanu(RA) ya yi shahada a gidansa a Madina, a shekara ta 35 bayan hijira, a lokacin ya haura shekara tamanin a duniya. Ya mutu a hannun ‘yan tawaye waxanda Adbullahi binu Saba’i bayahude yake jagoranta. Binu Saba’i shi ne uban ‘yan Shi’a wanda ya fara kira zuwa ga aqidojin qungiyar kuma shi ya fara kafa durakunta. Usmanu binu Affan ya auri mata da dama a rayuwarsa. Sun haxa da: 1. Ruqayya xiyar Manzon Allah(SAW), ta haifa masa Abdullahi wanda ya rasu a Madina yana qaramin yaro. Ruqayya(RA) ta yi hijira tare da mijinta zuwa Habasha kuma bayan komowarsu, sun yi qaura zuwa Madina. Ta rasu a shekara ta biyu bayan hijira, a dai-dai lokacin da Musulmi suke komowa daga yaqin Badar. 2. Ummu Kulthum xiyar Ma’aiki(SAW). Annabi ya aura masa ita bayan rasuwar Ruqayya. Ummu Kulthum(RA) ta zauna da Usmanu shekara bakwai, to amma Allah bai ba su haihuwa ba. Ta rasu a shekara ta tara bayan hijira. A lokacin da ta rasu, Annabi(SAW) ya ce da Usmanu: “Da muna da wata ‘ya da mun ba ka.” Banda waxannan biyun, Usmanu ya auri wasu mata kamar Faxima xiyar Walid ta Banu Makhzum, da Ramla xiyar Shaiba ta Banu Umayya, da Na’ila xiyar Farafisa wacce ta kare Usmanu daga harin ‘yan tawaye har aka raunata ta. Nasaba Da Serekutar Ali binu Abi Xalib(RA) Shi ne Ali xan Abu Xalib xan Abdulmuxxalib xan Hashim xan Abdu Munaf xan Qusayyu. Ya fito daga gidan Banu Hashim, gidan su Manzo(SAW). Shi ne shugaban Ahalul Baiti bayan Annabi(SAW). Xan baffan Annabi kuma mijin xiyarsa Faxima. Na farkon wanda ya musulunta a cikin yara; a lokacin da ya musulunta bai kai shekara goma ba. Annabi ne ya raine shi, ya taso a gidan annabta, kuma ta kansa ne zuri’ar Annabi(SAW) ta yaxu ta hanyar ‘ya’yansa Hassan da Hussaini. Ali(RA) yana da baiwa mai yawa da falala mai girma. Jarumi ne sadauki, mai ilmi da yawan sani, kuma ga fasaha da zalaqa ta harshe. Ya lizimci Annabi(SAW) a tsawon rayuwarsa, kuma ya halarci yaqoqa duka tare da Annabi(SAW) banda Tabuka; bai je ba saboda Ma’aiki(SAW) ya umarce shi da ya yi gadin iyalinsa a Madina. Ya auri xiyar Manzo(SAW) Faxima da jikarsa Umamatu xiyar Abul Aas wacce Zainab xiyar Annabi ce ta haife ta. Sarkin Musulmi Ali binu Abi Xalib(RA) ya zama khalifa na huxu bayan Usmanu(RA). Sai dai a lokacin khilafarsa fitina wacce ta faro da kisan Usmanu ta shagaltar da shi don haka ba’a samu buxe qasashe ba a zamaninsa. Maimakon haka, an samu yaqoqa a tsakanin Musulmi a junansu kuma ‘yan tawaye waxanda suka kashe Usmanu su ne suka haddasa su. Yaqin Jamal ya auku tsakanin Ali da magoya bayansa a hannu guda , da kuma Xalha da Zubairu da Innar Muminai A’isha waxanda suka fito da niyar yin sulhu tsakanin Ali da Mu’awiya. Haka nan, yaqin Siffain ya auku tsakanin Ali da Mu’awiya, kamar yadda yaqin Nahrawan ya auku tsakanin Ali da Khawarijawa waxanda suka fice daga rundunar Ali, suka yi masa tawaye bayan yaqin Siffai. Ali(RA) ya yi shahada a birnin Kufa, hedukwatar khilafarsa. Wani xan Khawarijawa mai suna Abdurrahman binu Muljam ne ya kashe shi a daren sha bakwai ga watan Ramalan, shekara ta 40 bayan hijira, yana da shekaru sittin da xaya a duniya. Ali binu Abi Xalib ya auri mata da yawa. Waxanda suka fi shahara a cikinsu su ne: 1. Faxima xiyar Manzon Allah(SAW). Ita ce matarsa ta farko. Ya aure ta a shekara ta biyu bayan hijira kuma ta haifa masa Hassan da Hussaini da Ruqayya da Ummu Kulthum wacce Umar binul Khaxxabi ya aura, ta haifa masa Zaidu da Ruqayya. 2. Asma’u xiyar Umais. Ya aure ta bayan rasuwar mijinta na biyu Abubakar Siddiq, kuma ta zo gidansa da xan Abubakar mai suna Muhammad a matsayin agola wanda Ali ya raine shi har girmansa, kamar yadda muka gabatar da bayani. Asma’u ta haifawa Ali ‘ya’ya biyu: Aunu da Yahaya. 3. Umamatu xiyar Abul Aas binu Rabi ta gidan Banu Umayya. Jikar Manzon Allah ce ta wajen babbar xiyarsa Zainab. Ali ya aure ta bayan rasuwar qanuwar uwarta Faxima, kuma ba’a samu haihuwa ba a tsakaninsu. Umamatu ta yiwa Ali takaba, kuma a bayansa ta auri Mugira xan Naufal binul Harith binu Abdulmuxxalib. Bayan waxannan, Ali binu Abi Xalib(RA) ya auri mata masu yawa kamar Laila ta gidan Banu Tamim da Ummul Banina ta Banu Kilab da sauransu. Nasaba Da Serekutar Xalha binu Ubaidillah(RA) Shi ne Xalha xan Ubaidullahi xan Usmanu xan Amru xan Ka’abu xan Sa’ad xan Tamim xan Murra. Ya fito daga gidan Banu Taim, dangin Abubakar Siddiq(RA). Nasabarsa tana haxewa da Annabi(SAW) a kan kakansa na shida, Murra. Xalha ya musulunta a hannun Abubakar tun kafin Manzo(SAW) ya shiga gidan Arqam, kuma yana cikin goma da aka yiwa albishir da aljanna. Ya halarci yaqoqa duka tare da Annabi(SAW) banda yaqin Badar; bai je ba saboda Ma’aiki ya tura shi aikin leqen asiri tare da Sa’id binu Zaid. Koda suka komo, Annabi(SAW) ya riga ya dawo daga yaqin Badar, amma ya raba ganima da su domin su ma aikin yaqi suka je. A yaqin Uhudu, Xalha ya yiwa Annabi(SAW) garkuwa da jikinsa a yayin da kafirai suka tausa kora suna nufin kashe Manzo(SAW). A sakamakon haka, ya samu raunuka ishirin da huxu a jikinsa tsakanin sara da takobi da suka da mashi da harbi da kibiya. Wannan ya sa a duk lokacin da Abubakar ya tuna yaqin Uhudu sai ya kan ce, “Wannan rana ce ta Xalha.” Xalha binu Ubaidillah(RA) ya yi shahada a yaqin Jamal, a shekara ta 36 bayan hijira, yana da shekaru sittin da huxu a duniya. Sarkin Musulmi Ali binu Abi Xalib(RA) ya ji takaicin mutuwarsa kamar yadda ya yi baqin cikin mutuwar duk waxanda suka rasa rayukansu a wannan yaqi. Daga baya, ya tara ‘ya’yansa ya yi musu ta’aziyya, ya ce: “Lallai ina sa tsammani ni da ubanku mu zama daga cikin waxanda Allah ya ke cewa dangane da su: ‘Kuma muka xebe abinda ke a cikin zukatansu na daga qullin zuci, suna zama ‘yan uwa a kan gadaje, suna masu fuskantar juna (a aljanna).’”(Suratul Hijr: 47). Xalha(RA) ya auri mata da dama kuma ya haifi ‘ya’ya maza da mata masu yawa. Matansa sun haxa da: 1. Ummu Kulthum xiyar Abubakar Siddiq, ta haifa masa Zakariya da Yusuf da A’isha. 2. Ummul Harith xiyar Qassama, ta haifa masa Ummu Ishaq. Wannan xiya, Ummu Ishaq, Hassan xan Ali binu Abi Xalib ya aure ta, ta haifa masa Faxima. Kuma bayan rasuwarsa, qaninsa Hussaini xan Ali binu Abi Xalib ya aure ta, ta haifa masa xa ya sa masa suna Xalha. Wannan serekuta mai danqo (wa ya aura, qani ya aura) tsakanin gidan Ali(RA) da gidan Xalha(RA) tana nuna yadda ba su xauki yaqin Jamal a matsayin gaba da qiyayya ba, amma wani abu ne da Allah ya qaddare shi kuma ya faru ba bisa son ransu ba, kamar yadda maganar Ali da muka ruwaito a sama ta nuna. Allah ya xaukaki darajojinsu a aljanna baki xaya. Banda waxannan mata biyu, Xalha ya auri Hamnatu xiyar Jahash, shaqiqiyar Zainab xiyar Jahash Innar Muminai matar Manzon Allah(SAW), uwarsu Umaima xiyar Abdulmuxxalib, goggon Annabi(SAW). Nasaba Da Serekutar Zubairu binul Awwam(RA) Shi ne Zubairu xan Awwam xan Khuwailid xan Asad xan Abdul Uzza xan Qusayyu. Ya fito daga gidan Banu Asad, dangin Innar Muminai Khadija matar Annabi(SAW). Mahaifiyarsa ita ce Safiyya xiyar Abdulmuxxalib, kuma Khadija(RA) goggonsa ce. Zubairu ya musulunta bayan Abubakar; shi ne namiji na huxu ko na biyar da ya shiga Musulunci. Ya yi hijira biyu: Habasha da Madina, kuma yana cikin goma ‘yan aljanna. Ya halarci yaqoqa duka tare da Annabi(SAW). Shi ma ya yi shahada a yaqin Jamal. Ali(RA) ya yi matuqar baqin cikin mutuwarsa. Ya ce, “Ku yi albishir da wuta ga makashin xan Safiyya.” Ya rasu yana da shekaru sittin da huxu a duniya. Zubairu binul Awwam ya auri: 1. Asma’u xiyar Abubakar Siddiq, ta haifa masa Abdullahi da Asim. Abdullahi xan Zubairu ya shiga rikicin siyasa da Yazid xan Muawiya kuma ya rasa ransa a sanadiyar wannan rikicin kamar yadda Hussaini xan Ali ya shiga rikici da Yazid shi ma ya rasa ransa. 2. Rabab xiyar Anif, ta haifa masa Ubaidu da Umar. Shi Ubaidu shi ne ya haifi Munzir wanda ya auri Faxima xiyar Ali binu Abi Xalib(RA) wacce mahaifiyarta sa-xaka ce. Faxima ta haifa masa xa wanda ya sawa suna Usmanu. Banda waxannan mata guda biyu, Zubairu binul Awwam(RA) ya auri wasu matan masu yawa. Nasaba Da Serekutar Abdurrahman binu Auf(RA) Shi ne Abdurrahman xan Auf xan Abdu xan Harith xan Zuhra xan Kilab. Ya fito daga gidan Banu Zuhura dangin mahaifiyar Annabi(SAW). Ya musulunta da wuri kuma yana cikin goma ‘yan aljanna. Shi ne mutum na biyu da aka san Annabi(SAW) ya yi sallah a bayansa; na xayan shi ne Abubakar Siddiq. Ya rasu a shekara ta 32 bayn hijira. Abdurrahman binu Auf ya auri mata da dama, kamar Sahalatu xiyar Asim binu Adiyyu Ba’ansare da Ummu Kulthum xiyar Uquba binu Abi Mu’aixin (‘yar uwar Usmanu binu Affan da suka haxa uwa). Ummu Kulthum xiyar Uquba, kamar Asma’u xiyar Umais, ta auri manyan Sahabbai guda huxu. Da farko ta auri Zaidu binu Haritha ta haifa masa Ruqayya. Bayan Zaidu ya yi shahada a yaqin Mu’uta, ta auri Zubairu binul Awwam ta haifa masa Zainab. Bayan Zubairu, ta auri Abdurrahman binu Auf ta haifa masa Ibrahim da Hamidu. Bayan rasuwar Abdurrahman ta auri Amru binul Aas wanda ta rasu a xakinsa. Mai karatu zai lura cewa wannan babbar Sahabiya wacce ta fito daga gidan Banu Umayya da farko ta auri ‘yantaccen bawa wanda ba baquraishe ba ne sam. Sa’an nan ta komo cikin danginta Quraishawa ta auri xan gidan Banu Asad, sa’an nan ta auri xan gidan Banu Zuhura, sa’an nan daga qarshe ta auri xan gidan Banu Saham. Wannan misali ne na yadda ‘yan uwantakar Musulunci ta karfafi dangantakar nasaba, sa’an nan kuma serekuta ta qara xinke tsakanin waxannan tsarkakan tsara waxanda tarihi bai ga irinsu ba. Abdurrahman(RA) ya haifi ‘ya’ya masu yawa. Sun haxa da Urwa da Abdullahi da Salim da Ibrahim da Muhammad da Usman. Nasaba Da Serekutar Sa’ad binu Abi Waqqas(RA) Shi ne Sa’ad xan Abu Waqqas (sunansa Malik) xan Wuhaibu xan Abdu Munaf xan Zuhura. Shi ma ya fito daga Banu Zuhura kuma yana da kusanci ainun da mahaifiyar Annabi(SAW). Shi ya sa Manzo(SAW) wani lokaci yake kiran sa kawu. Wata rana Manzo(SAW) ya yi barkwanci. Da ya hangi Sa’ad yana tafe, sai ya dubi Sahabban dake zaune tare da shi ya ce, “Ga kawuna nan, mutum ya nuna min kawunsa!” Ya musulunta yana matashi xan shekara goma sha bakwai, kuma shi ne farkon wanda ya yi jifa da mashi don xaukaka addini. Ya halarci yaqoqa duka tare da Annabi(SAW) kuma Manzo(SAW) ya yi masa albishir da aljanna. Yana cikin kwamitin shura na mutum shida da Umar binul Khaxxab(RA) ya naxa waxanda suka zavi Usmanu khalifa. Shi ne kwamandan da ya ci qasar Iraqi a zamanin khalifa Umar(RA); kuma shi ne ya gina birnin Kufa. Bayan kisan Usmanu da hudowar fitina a tsakanin Musulmi, Sa’ad ya qauracewa mutane ya koma bayan garin Madina a wani wuri da ake kira Aqiq. A nan ya zauna har rasuwarsa a shekara ta 55 bayan hijira. An xauko shi zuwa Madina inda aka bunne shi a maqabartar Baqi’a. Sa’ad binu Abi Waqqas(RA) ya auri Ummu Harun xiyar Abdullahi xan Hunain (daga Banu Hashim Ahalul Baiti), ta haifa masa Harun da Bujad. Wannan yana nufin bayan dangantaka ta haxa shi da Ahalul Baiti ta wajen dangin Amina mahaifiyar Annabi(SAW), har yau kuma serekuta ta haxa shi da wannan babban gida ta kan wannan mata tasa Ummu Harun. Nasaba Da Serekutar Sa’id binu Zaid(RA) Shi ne Sa’id xan Zaid xan Amru xan Nufail xan Abdul Uzza xan Rayah. Ya fito daga gidan Banu Adiy dangin Umar binul Khaxxab(RA). Sa’id ya musulunta gabanin Annabi(SAW) ya shiga gidan Arqam kuma yana cikin goma ‘yan aljanna. Ya halarci yaqoqa duka tare da Annabi(SAW) banda yaqin Badar; bai je ba saboda Manzo(SAW) ya tura shi aikin leqen asiri tare da Xalha. Annabi(SAW) ya raba ganimar Badar da shi. Shi da matarsa, Faxima xiyar Khaxxab ‘yar uwar Umar, suka yi sanadin shiga Musuluncin Umar(RA) a lokacin da ya je gidansu ya ji suna karatun Alqur’ani. Sa’id binu Zaid(RA) ya rasu a shekarar hijira ta 51, yana xan shekara saba’in da ‘yan kai, kuma an bunne shi a maqabartar Baqi’a. Sa’id ya auri Faxima xiyar Khaxxab, ‘yar uwar Umar binul Khaxxab, ta haifa masa ‘ya’ya da yawa. Daga cikin xiyansa akwai Muhammad da Ibrahim da A’isha da Hafsa. Nasaba Da Serekutar Abu Ubaida(RA) Shi ne Abu Ubaida (sunansa Amir) xan Abdullahi xan Jarrah xan Hilal xan Uhaibu xan Lubba xan Harith xan Fihiru xan Malik. Ya fito daga gidan Banu Harith. Abu Ubaida ya musulunta da wuri, tun Musulmi a duniya duka ba su kai goma ba. Ya yi hijirar Habasha kafin Madina, kuma Manzo(SAW) ya yi masa albishir da aljanna. Ya halarci yaqoqa duka tare da Annabi(SAW) kuma a zamanin Sarkin Musulmi Abubakar yana cikin manyan kwamandojinsa. Shi ne ya buxe Dimashqa da Ba’alabakka da Anxakiya. Abu Ubaida(RA) mutum ne mai gaba-gaxi, wanda bai san wasa ba. A yaqin Uhudu, ya yi fito-na-fito da mahaifinsa ya kashe shi. A dalilinsa ne, kuma a dalilin wannan aiki nasa da yake nuna zurfin imani, Allah Maxaukaki ya saukar da wannan aya: “Ba za ka samu mutane masu yin imani da Allah da ranar Lahira suna soyayya da wanda ya savawa Allah da Manzonsa ba, ko da sun kasance ubanninsu ne, ko xiyansu ko ‘yan uwansu, ko danginsu. Waxannan Allah ya rubuta imani a cikin zukatansu, kuma ya qarfafa su da wani ruhi daga gare shi, kuma zai shigar da su a gidajen aljanna, qoramu na gudana qarqashinsu, suna masu dawwama a cikinsu. Allah ya yarda da su, kuma sun yarda da shi. Waxannan qungiyar Allah ne. To, lalle qungiyar Allah su ne masu babban rabo.”(Suratul Mujadala: 22). Abu Ubaida ya rasu a sakamakon wata annoba da ta watsu a garin Amwas na qasar Sham inda yake jihadi tare da rundunarsa. Wannan mummunar annoba ta yi sanadin mutuwar kimanin Musulmi dubu talatin, ciki har da manyan Sahabbai, a shekara ta 18 bayan hijira. Abu Ubaida Amir binul Jarrah(RA) ya auri mace xaya rak a rayuwarsa, ita ce Hindu xiyar Jabir binu Wahab binu Amir binu Lu’ayyu, ta haifa masa ‘ya’ya biyu: Yazid da Umar, waxanda duka suka mutu suna qanana. Don haka, Abu Ubaida bai bar baya ba amma ya bar tarihi mai cike da manya-manyan ayyuka na jihadi. Yana cikin Sahabbai qalilan da aka san sun auri mace xaya a rayuwarsu. Wani da aka san ya auri mace xaya kuma shi ne Usmanu binu Maz’un(RA). Abu Ubaida jihadi ne ya shagaltar da shi ga barin aure, shi kuwa Usmanu ya shagala da yawan ibada ne. Allah ya xaukaki darajojinsu a aljanna baki xaya. Nasaba Da Serekutar Mu’awiya binu Abi Sufyan(RA) Shi ne Mu’awiya xan Abu Sufyan (sunansa Sakhar) xan Harb xan Umayya. Ya fito daga gidan Banu Umayya, dangin Sarkin Musulmi Usmanu(RA). Ubansa Abu Sufyan ya jagoranci mushirikan Makka a cikin adawarsu ga Musulunci da yaqoqansu ga Annabi(SAW). Ya musulunta shi da ubansa bayan buxe Makka kuma ya halarci yaqin Hunain tare da Annabi(SAW). Ya kasance daga cikin marubutan Annabi(SAW) kuma Manzo(SAW) ya auri ‘yar uwarsa Ummu Habiba Ramla xiyar Abu Sufyan, Allah ya yarda da ita. Mu’awiya(RA) mutum ne da ya laqanci qulle-qullen siyasa da janhurunta. Umar binul Khaxxab ya naxa shi a kan wani vangare na qasar Sham kuma Usmanu binu Affan ya game masa mulkin Sham baki xaya. Mu’awiya ya ja da Sarkin Musulmi Ali(RA) a lokacin da ya qi ya yi mubaya’a sai har Ali ya zaqulo waxanda suka kashe Usmanu daga cikin rundunarsa ya hukunta su. A sakamakon haka, yaqin Siffain ya auku tsakanin Ali da Mu’awiya. Bayan da aka samu qiqi-qaqa a qarshen wannan yaqin, Mu’awiya ya yi amfani da iya janhurunsa na siyasa ya yi qarfi, a yayin da Ali ya yi rauni, kuma rundunarsa ta wargaje a sakamakon ficewar Khawarijawa daga cikinta. Ali(RA) ya shagala da yaqar Khawarijawa, abinda ya qara masa rauni, a lokacin da shi kuma Mu’awiya ya qara qarfi da kama qasa a cikin lamarinsa. Ana cikin haka ne Khawarijawa suka shirya maqarqashiyar kashe Ali da Mu’awiya, Allah ya yarda da su, wai domin su haxe kan Musulmi kuma su yi maganin fitina. Amma Mu’awiya ya tsallake wannan maqarqashiya da qaddarar Allah; shi kuwa Ali da aka qaddara masa qarar kwana ya yi shahada. Bayan rasuwar Sarkin Musulmi Ali(RA), magoya bayansa sun yi mubaya’a ga xansa Hassan(RA) wanda ya zama khalifa na tsawon wata shida. Hassan binu Ali(RA) ya yi tunanin ya kai qarshen jayayya da Mu’awiya wacce ya gada daga ubansa. Don haka ya xauki matakin yin sulhu da Mu’awiya kuma ya sakar masa lamarin shugabancin al’umma domin tsai da zubar da jinin Musulmi a junansu. Da wannan ne Mu’awiya ya zama Sarkin Musulmi kuma dukkan vangarori suka shiga qarqashin xa’arsa, in banda Khawarijawa waxanda suka ci gaba da yaqar sa. Kuma da wannan sulhu ne aka kai qarshen zamanin Khulafa’ur Rashidun kuma aka fara zamanin khalifofin Banu Umayya. Wannan ya faru a shekara ta 40 bayan hijira, shekarar da akewa laqabi da Amal Jama’a, watau shekarar haxin kai, saboda haxuwar al’umma a kan Mu’awiya(RA). Mu’awiya binu Abi Sufyan ya yi shekara ishirin yana gwamnan Sham, kuma ya shekara ishirin yana khalifa. Ya rasu a shekara ta 60 bayan hijira, yana da shekaru saba’in da takwas a duniya. Sarkin Musulmi Mu’awiya ya auri Fakhitatu xiyar Qurza, ta haifa masa Abdurrahman da Abdullahi. Haka nan, ya auri Maisun xiyar Badajal wacce ta haifa masa xansa Yazid wanda ya gaje shi a matsayin khalifa. Mun gabatar da bayani cewa gidan su Mu’awiya, Banu Umayya, surukan Annabi(SAW) ne. Ya aurar da xiyansa mata uku ga ‘ya’yan wannan gida. Su ne Zainab ya aurar da ita ga Abul Aas binu Rabi da kuma Ruqayya da Ummu Kulthum ya aurar da su ga Usmanu binu Affan. Kamar yadda shi kuma ya auri ‘yar uwar Mu’awiya, watau Ramla wacce akewa alkunya da Ummu Habiba, Allah ya yarda da su baki xaya. Serekuta Tsakanin ‘Ya’yan Sahabbai Da Ahalul Baiti Kamar yadda dangantaka da serekuta ta haxa tsakanin Sahabbai da Ahalul Baiti, haka abin ya ci gaba a tsakanin ‘ya’yan Sahabbai da zuri’ar Ahalul Baiti maza da mata, inda suka ci gaba da qulla danqon zumunta ta hanyar auratayya da serekuta da qara cuxanyar nasabarsu da junansu. Daga cikin irin wannan auratayya mai albarka, za mu ba da misali qanqane da yake tabbatar da yadda soyayya da qauna da ban girma suka doge a tsakanin zuri’ar Sahabbai da Ahalul Baiti, savanin abinda ma’abota jahilci da masu mugunyar manufa suke yaxawa na vata sunan waxannan zavavvun tsara domin kawo fitina da raba kan Musulmi. 1. Atika xiyar Zaid ‘yar uwar Sa’id binu Zaid kuma ‘yar baffan Umar binul Khaxxab (daga Banu Adiy). Ana yi mata laqabi da matar shahidai saboda ta auri maza biyar waxanda duka suka yi shahada. Da farko ta auri Abdullahi xan Abubakar Siddiq (daga Banu Taim), ya yi shahada a yaqin Xa’if a zamanin Manzon Allah(SAW). Sa’an nan, ta auri Umar binul Khaxxab (daga Banu Adiy), ya yi shahada. Bayansa ta auri Zubairu binul Awwam (daga Banu Taim), ya yi shahada a yaqin Jamal. Sai ta auri Muhammad xan Abubakar Siddiq, agolan Ali binu Abi Xalib kuma xan uwan mijinta na farko (daga Banu Taim), ya yi shahada a Misira yana gwamnan Ali binu Abi Xalib. Sa’an nan, daga bisani ta auri Hussain xan Ali binu Abi Xalib (daga Ahalul Baiti), shi ma ya yi shahada a Karbala. 2. Faxima xiyar Ali binu Abi Xalib(RA), mahaifiyarta qwarqwara ce. Ta auri Muhammad xan Abu Sa’id xan Aqilu binu Abu Xalib (daga Ahalul Baiti), ta haifa masa Hamida. Bayansa, ta auri Sa’id xan Aswad binu Abil Buhuturi (daga Banu Asad), ta haifa masa Barazatu da Khalid. Sa’an nan, ta auri Munzir xan Ubaidatu binu Zubairu binul Awwam (daga Banu Taim), ta haifa masa Usmanu. 3. Ramla xiyar Ali binu Abi Xalib(RA). Ta auri Abdullahi xan Abu Sufyan binul Harith binu Abdulmuxxalib (daga Ahalul Baiti). Sa’an nan ta auri Mu’awiya xan Marwan binul Hakam (daga Banu Umayya). Marwan binul Hakam shi ne kakan yawancin khalifofin Banu Umayya, ciki har da Umar binu Abdil Aziz, khalifa mai adalci. ‘Yan Shi’a ma’abota jahilci, masu vatan vakatantan, suna la’antar wannan bawan Allah wai da hujjar yana gaba da Ahalul Baiti, koda yake xiyar Ali ta cikinsa ba ta ga laifi ta auri xansa na cikinsa ba. 4. Sakina xiyar Hussain xan Ali binu Abi Xalib(RA), mahaifiyarta ita ce Rababu xiyar Imru’ul Qais (daga Banu Kilab). Ta auri Mus’abu xan Zubairu binul Awwam (daga Banu Taim) ta haifa masa Faxima. Bayan rasuwarsa, ta auri Zaid xan Umar binu Usman binu Affan (daga Banu Umayya). Sa’an nan, bayan rasuwar Zaid ta auri Ibrahim xan Abdurrahman binu Auf (daga Banu Zuhura). 5. Faxima xiyar Hussaini xan Ali binu Abi Xalib(RA), mahaifiyarta Ummu Ishaq xiyar Xalha binu Ubaidillah (daga Banu Taim). Ta auri Hassan xan Hassan binu Ali binu Abi Xalib (wanda ake wa laqabi da Hassanul Muthanna, daga Ahalul Baiti), ta haifa masa Abdullahi da Ibrahim da Zainab. Bayan rasuwarsa, ta auri Abdullahi xan Amru binu Usman binu Affan (daga Banu Umayya), ta haifa masa Qasim da Muhammad. 6. Ummu Kulthum xiyar Abdullahi xan Ja’afar binu Abi Xalib (daga Ahalul Baiti). Ta auri Abanu xan Usman binu Affan (daga Banu Umayya). 7. Ummu Ishaq xiyar Xalha binu Ubaidillah (daga Banu Taim). Ta auri Hassan xan Ali binu Abi Xalib (daga Ahalul Baiti), ta haifa masa Faxima. Bayan rasuwarsa, ta auri qaninsa Hussain binu Ali, ta haifa masa xa wanda ya sa masa sunan ubanta Xalha. Xalha binu Ubaidillah shi ma ‘yan Shi’a ma’abota jahilci, masu vatan vakatantan, suna la’antar sa wai a dalilin ya yaqi Ali binu Abi Xalib(RA), ko da yake Hassan da Hussaini ba su ga laifi ba su auri xiyarsa, xaya bayan xaya, saboda qauna da sada zumunci, kuma har ma Hussaini ya haihu da wannan xiya ya sawa xan sunan ubanta. Saboda haka a nan sai ‘yan Shi’a iyayen jahilci, manya masu TRANSLATION da TRANSLITERATION, suka nuna halin irin mutanen nan da ake cewa masu fushi da fushin wani. Su har ma sun fi wanin fushi! Allah ya raba mu da yin addini da ka. Serekuta Tsakanin Jikokin Sahabbai Da Ahalul Baiti Auratayya da serekuta ba ta tsaya a tsakanin ‘ya’yan Sahabbai da ‘ya’yan Ahalul Baiti ba kawai; a’a wannan zumunci da ‘yan uwantaka da soyayya da qauna da ban girma sun ci gaba har a tsakanin jikokinsu da ‘ya’yan jikokinsu. A wannan ajin za mu ba da misali xaya kawai saboda muhimmancinsa, domin wannan misali yana qara tabbatar da qaryar ‘yan Shi’a da duk wani zindiqi mai son ya vata sunan Sahabbai da Ahalul Baiti domin ya yi amfani da wannan dama ya soki shugabansu kuma abin koyinsu, Manzon Allah(SAW). Misalin shi ne na nasabar Ja’afar Sadiq, imamin Shi’a na shida. Ta wajen uwa, Ja’afar jikan Abubakar Siddiq ne ninki biyu. Mahaifiyarsa, Ummu Farwa, kakanta na wajen uwa da kakanta na wajen uba duka ‘ya’yan Siddiqu ne na cikinsa. Kakanta na wajen uwa shi ne Abdurrahman xan Abubakar Siddiq, shaqiqin A’isha Innar Muminai, wanda ya haifi mahaifiyarta Asma’u. Kakanta na wajen uba shi ne Muhammad xan Abubakar Siddiq (agolan Ali binu Abi Xalib) wanda ya haifi mahaifinta Qasim. Wannan ya sa Ja’afar Sadiq yake cewa, “Abubakar ya haife ni sau biyu.” Ta wajen uba kuwa, Ja’afar xan Muhammad Baqir ne, xan Ali Zainul Abidin xan Hussain binu Ali binu Abi Xalib, Allah ya yarda da su baki xaya. Wannan nasaba ta zinare babu shakka wata mahangurva ce a fuskar ma’abota jahilci da zindiqai masu son su vata kyawun Musulunci ta hanyar sifanta shugabannin addini na farko da sifar ‘yan daba musu gaba da qiyayya da hancini a kan abin duniya. Muna roqon Allah ya qara turmuza hancinsu a qasa. Babi Na Huxu Suna Linzami Turawa suna da wani karin magana inda suke tambaya: “What is in a name?” Ga wanda ya sani, amsa sahihiya ita ce, “Plenty.” Larabawa kuma suka ce: Minismika a’arifu abaka. Ma’ana, “Daga sunanka ake sanin ubanka.” Watau daga sunan mutum ake sanin mahaifinsa Musulmi ne ko kafiri; jahili ne ko malami; mai bin Sunna ne ko xan bidi’a; wayayye ne ko bagidaje. Su kuwa Hausawa suka ce, “Suna linzami.” Wannan yana nufin banda tasirin suna ga mutum, har yau suna qawa ne idan muka dubi ma’anar kwaxo da linzami. Duka wannan yana nuna muhimmancin suna a wajen al’ummai dabam-daban da addinai dabam-daban. Suna yana da muhimmanci a addini da rayuwa. A rayuwa dai, suna da shi ake sanin mutum, a san iyayensa da ‘ya’yansa, kana suna yana raka mutum a tsawon rayuwarsa kuma ya ci gaba da zama a bayan mutuwarsa. A addini kuwa, Musulunci ya kwaxaitar da zavawa ‘ya’ya, maza da mata, kyawawan sunaye kuma ya isa dalilin muhimmancin haka a Shari’a yadda Annabi(SAW) ya sauyawa mutane da dama, maza da mata, sunayensu don su dace da kyawawan sunaye. Wataqila mai karatu ya lura a babin da ya gabata yadda da dama daga cikin Ahalul Baiti suka sawa ‘ya’yansu sunayen manyan Sahabbai, maza da mata, musamman sunayen Abubakar da Umar da Usman da Abdurrahman da A’isha da Hafsa, da sauransu. Wannan wani qarin hujja ne mai qarfi da yake nuna soyayya da qauna da ban girma dake tsakanin Ahalul Baiti da Sahabbai, kamar yadda yake fallasa qaryar ‘yan Shi’a waxanda suke yaxa cewa gaba da qiyayya sun kasance a tsakaninsu kuma wai suna ganin kafircin juna. Wannan ya sa muka ga ya dace mu kawo ‘yan misalai kaxan domin amfanin masu karatu. ‘Ya’Yan Ali Masu Sunayen Sahabbai Bayan rasuwar Faxima(RA), Ali binu Abi Xalib ya auri mata da yawa kuma ya yi sa-xaka da qwarqwarori masu yawa. Haka nan, banda ‘ya’yan da Faxima ta haifa masa, Allah ya arzuta shi da wasu ‘ya’yan masu yawa daga sauran matansa da qwarqwarorinsa. A taqaice dai a lokacin da ya yi shahada, Ali(RA) ya bar matan aure huxu, qwarqwarori goma sha shida da ‘ya’ya maza da mata kimanin arba’in. A nan, za mu ambaci ‘ya’yansa masu sunayen Sahabbai ne kawai tare da uwayensu, kuma za mu kawo waxannan bayanai daga littafan malaman Shi’a waxanda suka yarda da su. 1. Abbas da Abdullahi da Ja’afar da Usman. Mahaifiyarsu ita ce Ummul Banina xiyar Hazam binu Daram. 2. Ubaidullahi da Abubakar. Uwarsu ita ce Laila xiyar Mas’ud Addaramiyya. 3. Ruqayya da Umar Babba. Uwarsu ita ce Ummu Habib xiyar Rabi’a. 4. Umar Qarami. Mahaifiyarsa ita ce Assahba Altaglubiyya. Mai karatu zai lura da cewa Ali binu Abi Xalib(RA) ya sawa ‘ya’yansa sunayen Sahabbai Abubakar da Umar da Usman. Umar ma har biyu gare shi, Umar Babba da Umar Qarami, kamar yadda yake da Muhammad Babba da Muhammad Qarami. Kuma wannan bayani mun naqalto shi daga littafan Rafilawa waxanda manyan malamansu suka wallafa. To idan da gaskiya ne Ali binu Abi Xalib yana qin Abubakar da Umar, ko kuma yana qudure cewa su kafirai ne sun yi ridda, kamar yadda ‘yan Shi’a suke yaxawa, ya zai sanya wa ‘ya’yansa sunayensu? Sanya sunayen Sahabbai ga ‘ya’yan Ahalul Baiti bai tsaya a kan Sarkin Musulmi Ali ba kawai, a’a abu ne wanda ya zama al’ada a cikin ‘ya’ya da jikoki, kai har ma da jikokin jikoki na Ahalul Baiti. A nan za mu ba da misali qanqane, tare da naqaltowa daga littafan malaman Rafilawa su da kansu. 1. Hassan binu Ali binu Abi Xalib(RA), ya sa wa ‘ya’yansa sunan Abubakar da Umar. 2. Hussain binu Ali binu Abi Xalib(RA), shi ma a cikin ‘ya’yansa akwai Abubakar da Umar. 3. Ali binul Hussain binu Ali binu Abi Xalib(RA), yana da xa mai suna Umar. 4. Musa binu Ja’afar binu Muhammad binu Ali binu Hussain binu Ali binu Abi Xalib, wanda aka fi sani da Musa Alkazim, imamin Shi’a na bakwai, ya sawa xiyarsa suna A’isha. 5. Ali binu Musa (imamin Shi’a na takwas) wanda sukewa laqabi da Alrida, yana da xiya mai suna A’isha. Wannan misali ne kawai muka bayar na yadda Ahalul Baiti a tsawon shekaru suka mayar da sawa ‘ya’yansu sunayen Sahabbai al’ada. Littafan malaman Shi’a waxanda suka rubuta da hannayensu cike suke da wannan al’ada wacce take nuna qaunar Ahalul Baiti da girmamawarsu ga Sahabbai. Wanda yake son qarin bayani na irin waxannan misalai sai ya duba waxannan littafai na malaman Shi’a: Maqatilux Xalibiyyin na Abul Faraj Al’asbahani xan Shi’a, da Tarikhul Ya’aqubi na Ya’aqubi xan Shi’a, da Altanbihuwal Ishraf na Mas’udi xan Shi’a, da Mu’ujamu RijalilHadith na Khu’i xan Shi’a, da wasu da yawa banda waxannan. Ha’incin Malaman Shi’a Mai karatu yana iya yin tambaya a nan: idan gaskiya ne littafan malaman Shi’a suna cike da irin waxannan misalai kamar yadda aka ambata a sama, to me ya sa alal aqalli su ‘yan Shi’a ba su san da haka ba? Me ya sa, ga misali, ba su san cewa Ali da Hassan da Hussaini, Allah ya qara musu yarda, duka suna da ‘ya’ya masu suna Abubakar da Umar ba? To amsa ita ce, yawancin ‘yan Shi’a dai jahilai ne, kuma malamansu suna amfani da wannan jahilci nasu su voye masu abubuwa waxanda ga su rubuce a cikin littafansu amma ba su iya gani. Wannan abu haka yake a dukkan qasashen da ‘yan Shi’a suke, amma a nan Nijeriya ya fi tsanani. A nan qasar, manyan malaman Shi’a, ciki har da madugunsu Ibrahim Alzakzaki, ba su iya karanta littafan Larabci in ba su da wasali! To a nan mai karatu yana iya ganin cewa babu shakka akwai matsala. Ko da mutum ya ga littafai a wurinsu tuli, to kwalliya ce kawai da burga suke yi amma ba karatu ba. Idan kuma har sun karanta to ba su gane kome sai abinda ba’a rasa ba. Su kuwa mabiya ba batunsu ake ba. Yawancinsu ba abinda suka sani daga TRANSLATION sai TRANSLITERATION. To babu shakka kuwa ba’a karatun Musulunci da waxannan. Saboda haka sai abin ya zama duhu yana dukan duhu. Wannan ya sa malaman Shi’a suke voye abinda suka ga dama su bayyana abinda suka ga dama, tunda dama mai ido xaya ne yake jan makafi. Bari mu ba da misali wanda zai qara fito da wannan lamari fili. Qissar Karbala da yadda Hussaini(RA) ya yi shahada a can, wataqila malaman Shi’a ba su da wani karatu da suke koyawa mabiyansu wanda ya fi wannan qissa. Kullum suna maimaita ta a makarantunsu da kan mimbari wajen huxuba da kuma gidajen talabijin masu watsa shirye-shiryensu ta hanyar tauraron xan Adam. Amma idan mutum ya dubi yadda suke ba da qissar sai ya ga ha’inci da cin amanar ilmi a fili. Ga misali, kowa ya san cewa Hussaini(RA) ya zo Karbala tare da iyalinsa da ‘yan uwansa na kusa, kuma yawancinsu sun yi shahada tare da shi a wannan wuri. Amma idan malaman Shi’a suka zo ba da labarin abinda ya faru sai su yi xungushe. Suna ambaton musibar da Hussaini ya gamu da ita a Karbala da qishirwar da ya yi fama da ita da fafatawa da ya yi da abokan gaba da kuma yadda daga qarshe ya yi shahada. Amma sai su qi ambaton sunayen ‘yan uwansa, Abubakar binu Ali da Umar binu Ali da Usman binu Ali, waxanda su ma suna tare da shi a wannan yaqi, sun gamu da musiba irin wacce ya gamu da ita, sun yi fama da qishirwa yadda ya yi fama da ita, sun fafata da abokan gaba kamar yadda ya fafata da su, kuma daga qarshe sun yi shahada tare da shi kamar yadda ya yi shahada. Haka nan, suna ambaton yadda ‘ya’yan Hussaini, Ali Babba da Abdullahi, suka yi shahada a Karbala, amma su qi ambaton xan uwansu, Umar binu Hussain, wanda shi ma ya yi shahada tare da su. Haka nan, suna ambaton ‘ya’yan Hassan(RA), Abdullahi da Qasim, waxanda suka yi shahada a Karbala, amma su voye sunayen ‘yan uwansu, Abubakar binul Hassan da Umar binul Hassan, waxanda su ma sun yi shahada tare da su. Haka nan, suna ambaton ‘ya’yan Aqilu binu Abi Xalib(RA), Ja’afar da Abdullahi, waxanda suka yi shahada a Karbala, amma su sakaya sunan xan uwansu, Abdurrahman binu Aqil, wanda shi ma ya yi shahada tare da su. Wannan shi ne yadda malaman Shi’a suke ha’intar mabiyansu, su ci amanar ilmi, su qeqashe qasa, ba kunya ba tsoron Allah, su ambata sunayen da suke so a cikin qissar Karbala, su voye waxanda suke so, tare da cewa duka ga su rubuce a cikin littafansu. Wataqila wannan ya ba wani mamaki, amma wanda ya san haqiqanin addinin Shi’a ya san cewa hakan kaxan da aikinsu ne. Faxakrwa Dangane Da Sunaye Musulmin Nijeriya Allah ya yi mana baiwa da al’adar sanya sunayen Musulunci tsintsa. Har ana iya cewa, a duniya duka ba wata qasar Musulmi da ta wuce mu a wannan fage. Mai biye mana a baya ita ce qasar Sudan. Wannan muhimmin abu ne da ya jawo kulawar duniya har malamai da dama waxanda ba na qasar nan ba suka yi rubutu a kai. Wanda nake iya tunawa daga cikinsu a yanzu shi ne Abdurrahman Doi, wanda yake Musulmi ne Ba’indiye da ya yi aiki a Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria. Babu shakka wannan abu ne muhimmi da ya kamata mu gode Allah a kansa, mu yi alfahari da shi, kuma mu tabbatar ya xore a cikin ‘ya’yanmu da jikokinmu. Sai dai abin takaici shi ne, a ‘yan shekarun nan wannan abu ya fara ja da baya, inda sunaye marasa asali marasa ma’ana suka fara yaxuwa a tsakaninmu. Kuma abin ya fi yawa a sunayen mata, inda za ka iske iyaye suna sanyawa xiyansu sunaye kawai saboda suna da zaqin faxi a baka. Misalin sunaye kamar Amira, Farida, Samira, da sauransu. Wasu ma su kan fi waxannan muni da rashin ma’ana, kamar Shamsiyya, Fauziyya, Qamariyya, Quluziyya, Zillaziyya, da sunaye masu kama da haka. Wani da ba na tuhuma da qarya ya ba ni labari a garin Kaduna cewa ya tava jin wata yarinya da suna Mal’una (watau La’ananniya!). Wannan duka yana nuna yadda jahilcinmu ya zama ninki biyu: ba’a sani ba kuma ba’a san cewa ba’a sani ba! Hakan ya sa ya zama wajibi a yi faxakarwa, kuma na mai da hankali a misalaina ga sunayen mata saboda a nan ne wannan matsala ta fi yawa. Shari’a ba ta bar lamarin sunaye haka sakaka ba. Sunnar Manzo(SAW) ta nuna kyawawan sunaye da fifikonsu. 1. Na farko su ne sunaye masu haxe da Abdu. Waxanda suka fi a cikin waxannan su ne Abdullahi da Abdurrahman. Sai kuma sauran sunaye duka dake haxe da Abdu, kamar Abdul’aziz, Abdulwahhab, Abdulmalik, da sauransu. A wannan aji dole a nesanci sunayen da ma’abota jahilci suka qaga kamar Abdulhussaini, Abdul’amir, Abdunnabi, Abdurrasul, da sunaye masu kama da su. ‘Yan Shi’ar qasashen Iraqi da Iran suke sa irin waxannan sunaye. 2. Waxanda ke biye su ne sunayen annabawa. Na farkonsu Annabinmu Muhammad, sa’an nan sai sauran annabawa da manzanni waxanda ambatonsu ya zo imma a cikin Alqur’ani mai girma ko a cikin hadisai ingatattu. Kamar yadda aka sani, babu mace a cikin annabawa, to amma akwai siddiqai mata wanda shi ne matsayi na biyu bayan annabta. Misalin manyan mata a cikin al’umman da suka gabata akwai Maryamu mahaifiyar Annabi Isa(AS) da mahaifiyarta Hannatu matar Imrana. A cikin wannan al’umma kuma akwai Khadija da A’isha da Faxima. Banda waxan nan, akwai wasu manyan mata, kamar Asiya (Hasiya) matar Fir’auna da Saratu da Hajaru matan Annabi Ibrahim(AS). 3. Daga waxannan sai sunayen Sahabban Annabi(SAW) da mutanen gidansa, maza da mata. Waxannan akwai dubunnai shahararru da masu qarancin shuhura. 4. Akwai kuma wasu da yake can asali ba sunaye ba ne, amma alkunya ne ko nasaba ko laqabi. Ana sa waxannan sunaye domin tunawa da masu su na farko da neman albarkarsu da fatan koyi da ayyukansu masu nagarta. Misali kamar Buhari, Shafi’i, Suyuxi, Hanbali, Gazali, Fodiyo, da sauransu. Irin waxannan sunaye na tarihi ba laifi Musulmi ya kira xiyansa da su, to sai dai dole ne a guji sa sunan ‘yan bidi’a, kamar Tijjani,Inyasi, Harazumi, Barhama, da masu kama da su. 5. Babu laifi a yi amfani da sunaye ko laqabai na gida masu kyakkyawar ma’ana ko don tunawa da wasu mutane na gari, kamar Balarabe/Bala, Bawa (idan ana nufin bawan Allah), Inuwa, Bello, da masu kama da su. Sunayen Mata Masu Kyawu A nan qasa, za mu ba da jerin wasu daga sunayen mata masu kyawu, tare da ambaton asalin sunayen, domin kwaikwayawa: A’isha/Shatu/A’i: Xiyar Abubakar Siddiq. Innar Muminai, matar Annabi(SAW). Amina/Maidare: Mahaifiyar Manzon Allah(SAW). Asma’u/Ma’u: Xiyar Abubakar Siddiq, matar Zubairu binul Awwam. Sahabiya ce. Asiya/Hasiya: Matar Fir’auna. Xaya daga cikin mata qalilan da suka samu kammala a tarihin Bil Adama baki xaya. Ta riqe Musuluncinta duk da cewa mijinta babban kafiri ne, sai ta cancanci girma a wajen Allah da bayinsa salihai. Atika: Xiyar Abdulmuxxalib. Goggon Annabi ce kuma uwar matarsa, Innar Muminai Ummu Salma. Sahabiya ce. Bara’atu Baraka: Baiwar Annabi ce da ya gada daga mahaifinsa, Abdullahi. Ta raini Manzo(SAW), kuma ya ‘yanta ta, ya aurar da ita ga ‘yantaccen bawansa Zaidu binu Haritha. Ta haifawa Zaidu xansa Usama. Barira: Baiwar Innar Muminai A’isha ce. Bilkisu: Mai gadon zinare. Sarauniyar daular Saba ta zamanin Annabi Sulaiman(AS). Ta musulunta. Xaharatu/Xahare Faxima/Fati/Zahara’u/Binta/Batulu: Xiyar Manzo(SAW), matar Ali kuma uwar ‘ya’yansa, Hassan da Hussaini. Habiba/ Biba/ Bibalo: Xiyar Kharija. Matar Abubakar Siddiq. Ba’ansariya ce. Hafsa/Tasidi/Ta’annabi: Xiyar Umar binul Khaxxabi. Innar Muminai, matar Annabi(SAW). Hajara: Matar Annabi Ibrahim(AS), uwar xansa Annabi Isma’il(AS). Halima/Sa’adiya/Dubu: Ta shayar da Annabi(SAW). Hanafiyya: Sunanta Khaulatu. Qwarqwarar Ali binu Abi Xalib. Abubakar ya ba shi ita, ta haifa masa Muhammad binul Hanafiyya. Hannatu/Hanne: Matar Imrana, mahaifiyar Maryamu uwar Annabi Isa(AS). Tana cikin matan da suka samu kammala, kamar yadda ya zo a hadisi. Hassana Hauwa’u/Kulu/Maijidda: Matar Annabi Adam(AS). Kakar talikai. Hindu: Shi ne sunan yanka na Innar Muminai Ummu Salma. Hussaina Izzatu: Xiyar Abu Lahabi. Sahabiya ce. Jamila: Xiyar Thabit. Matar Umar binul Khaxxabi. Ba’ansariya ce. Jumana: Daga cikin xiyan Ali binu Abi Xalib(RA). Juwairiyya/Zuwaira/Zuwaire: Innar Muminai, matar Annabi(SAW). Khadija/Hadiza/Dije/Kubura: Innar Muminai, matar Manzo(SAW). Khalida: Xiyar Abu Lahabi. Sahabiya ce. Khaula/Haule: Sahabiya ce. Qarina: Matar Abdurrahman binu Abubakar Siddiq. Laila: Umar binul Khaxxabi yana da jikanya mai wannan sunan. Ita ce xiyar xansa Asim wacce ta auri Abdul’aziz xan Marwan binul Hakam, ta Haifa masa Umar binu Abdil’aziz, khalifan Banu Umayya mai adalci. Lubabatu/Luba: ‘Yar uwar Innar Muminai Maimuna xiyar Harith ce, kuma mata ga baffan Annabi(SAW) Abbas binu Abdilmuxxalib. Ita ce ta shayar da Hussaini binu Ali. Har yau, Ali yana da xiya mai sunan. Maimuna/Munari: Innar Muminai, matar Annabi(SAW). Mariya/Mari: Innar Muminai, qwarqwarar Manzo(SAW). Maryam/Mero: Mahaifiyar Annabi Isa(AS). Siddiqa ce. Nafisa/Nafi: Daga cikin xiyan Ali binu Abi Xalib. Na’ima Na’ila: Matar Usman binu Affan. Jaruma ce; ta kare mijinta a gaban masu tawaye har aka yi mata rauni. Nusaiba: Sahabiya ce, Ansariya. Rabi’a/Rabi/Adabiyya: Baiwar Allah ce wacce ta shahara da ibada. Rahamatu/Ramatu Ramla: Innar Muminai, matar Annabi(SAW). Ruqayya: Xiyar Manzo(SAW). Matar Usman binu Affan(RA). Sa’adatu/Sa’a/Sa’ade Safiyya: Xiyar Abdulmuxxalib. Goggon Annabi ce, kuma mahaifiyar Zubairu binul Awwam. Sahabiya ce. Akwai Safiyya xiyar Khaxxabi, ‘yar uwar Umar. Salamatu Saratu/Sarai: Matar Annabi Ibrahim(AS), mahaifiyar xansa Annabi Ishaq(AS). Sauda/Saude: Xiyar Zam’a. Innar Muminai, matar Annabi(SAW). Sukaina/Sakina: Daga cikin xiyan Hussaini binu Ali. Sumayyatu/Sumayya: Sahabiya ce. Mutum na farko da ta yi shahada a Musulunci. Suwaiba: Baiwar baffan Annabi Abu Lahabi. Ta shayar da Manzo(SAW) kafin Halima ta xauke shi. Shaima’u/Shema’u Shifa’u/Shafa: Mahaifiyar Abdurrahman binu Auf. Itace ungozoma da ta karvi haihuwar Annabi(SAW). Umamatu: Jikanyar Annabi(SAW), xiyar ‘yarsa Zainab. Hamza baffan Annabi ma yana da xiya mai sunan. Umaimatu: Xiyar Abdulmuxxalib. Goggon Annabi ce kuma uwar matarsa, Zainab xiyar Jahash. Sahabiya ce. Akwai Umaimatu xiyar Khaxxabi, ‘yar uwar Umar. Ummu Aiman: Itace Baraka. Ummu Hani: Xiyar Abu Xalib, ‘yar uwar Ali. Sahabiya ce. Ummul Khair/Umma Ummu Kulthum: Xiyar Annabi(SAW), matar Usmanu binu Affan(RA). Wasila Zainab/Abu: Annabi(SAW) ya auri mata biyu masu wannan suna, Zainab xiyar Khuzaima da Zainab xiyar Jahash. Kuma sunan babbar xiyarsa ne. Zaliha/Zulai: An ce it ace matar nan ta cikin qissar Annabi Yusuf(AS). Ta musulunta. Zubaida: Matar khalifan daular Abbasiyya, Harun Arrashid. Ta shahara da taimakon Addini da talakawa. Rufewa Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da aminci su tabbata ga Annabinmu Muhammad da Alayensa da Sahabbansa da waxanda suka bi tafarkinsu da kyautatawa. Bayan haka, daga karatun abinda ya gabata a wannan littafi abu guda ya bayyana a fili, shi ne cewa yawancin ‘yan Shi’a suna bin tafarkin Rafilanci a bisa rashin sani kuma hakan ya sa suna gaskata duk abinda malamansu suka faxa musu ba tare da wani tararrabi ba. Wannan shi ne jahilcinsu da muka yi ta maimaitawa a cikin dukkanin babukan littafin. Ga misali, idan mutum ya san cewa Hassan binu Ali binu Abi Xalib ya auri xiyar Xalha binu Ubaidillah kuma a bayan rasuwarsa qaninsa Hussaini ya auri ita wannan mata kuma ta haihu ya sawa xan sunan ubanta, ta ya zai yarda cewa akwai gaba da qiyayya mai tsanani a tsakanin Xalha da Ali? Shi mai gaskata wannan qaryar idan aka tambaye shi: Shin zai auri ‘yar maqiyin ubansa, ko kuma shi idan xan maqiyin ubansa ya nemi xiyarsa da aure zai ba shi? Babu shakka dole amsarsa ta zama a’a, sai fa idan yana da tavin hankali ko kuma wata xabi’a dabam gare shi ba ta bil Adama ba. Ko kuma, ta qaqa mutum mai hankali zai yarda cewa Ali binu Abi Xalib yana xaukar Umar binul Khaxxabi a matsayin kafiri wanda ya yi ridda, kuma shi Umar xin ya ci mutuncin matarsa Faxima a kan titi, a bainar jama’a, ya yi mata xan karen duka har ya karya mata qashin haqarqari, kuma sa’an nan Ali ya yi masa tukuici da xiyarsa Ummu Kulthum, xiyar wannan mata tasa da ta sha kashi, ya ba shi auren ta? Babu shakka wanda ya yarda da wannan qarya shi ne ainihin wanda ya ci mutuncin Ali; domin ba mu san yadda ya xauke shi ba a zuciyarsa. Mahaukaci? Matsoraci? Makwaxaici? Wulaqantacce koma bayan mazaje? To sai dai rashin sani, wanda aka ce ya fi dare duhu, ba abinda ba ya jawo wa mai shi. Mu, a matsayinmu na al’umma, rashin sani ya jawo mana tasku. Shekaru talatin da suka wuce (1980-2010), babu xan Shi’a ko xaya a Nijeriya, sai ko wanda ya zo ci-rani ko kaxar rava. Amma a yau, akwai dubunnai waxanda suke a shirye suke da su kashe ko a kashe su a kan Shi’anci. Kuma ba wannan ne kawai musibar ba; babbar musibar ita ce har yau ba’a faxaka ba. Har yau, ga alama, Musulmin qasar nan ba su fahimci haxarin yaxuwar Shi’a yadda ya kamata ba. Har yau ba mu ankara ba da cewa, tun da Shaihu Xanfodiyo ya kafa wannan al’umma shekaru xari biyu da suka wuce, babu wata musiba da ta afka mana kamar zuwan Shi’a. Da yinwa (irin su ‘yar Gusau da ake cewa), da fatara da mayata, da kwalara da yaqin basasa, kai har da mulkin mallaka kansa, idan aka mulmule su wuri guda, ba su kai musibar yaxuwar Shi’a ba. Na ce mulkin mallaka shi da kansa; domin tun wucewar Xanfodiyo babu wata musiba da ta same mu, a matsayinmu na al’umma, kamar sa. Kuma gaskiya ne mulkin mallaka ya rusa ginin al’ummarmu, ya haxa mu da yajuju da majuju(haxi na rashin adalci tun da ya xora su a kanmu), ya soke Shari’a, ya mayar da a’izzata ahliha azilla, (kuma yaxuwar jahilci ma xa ne daga cikin ‘ya’yan itaciyar mulkin mallaka waxanda suka nuna suka zama Shi’a), amma duk da haka ya bar mu muna Musulmi. Rafilanci kuwa ma’anarsa juyawa a kan dugadugai, da tuve rigar Musulunci xungurum, da komawa gidan jiya, watau Maguzanci. Yaxuwar Shi’anci warwara ce ga tufkar Musulunci ta sama da shekaru dubu a qasar nan. Wannan ita ce fahimta sahihiya ta yaxuwar Shi’anci a Nijeriya, kuma matuqar ba mu samu irin wannan fahimtar ba to da sauran aiki. Don haka a nan muke fuskantar da kira da babbar murya ga dukkan wani Musulmin da yake qasar nan, ko mece ce aqidarsa, da ya mai da hankali ga darasun Shi’a da fahimtar mene ne haqiqaninta, kuma ya xauka cewa wannan wajibinsa ne tsakaninsa da Ubangijinsa, tsakaninsa da al’ummarsa, tsakaninsa da gobe ta ‘ya’yansa da jikokinsa. Kuma mu sani, wallahi, yin burus da al’amarin yaxuwar Shi’a a qasar nan, ko nuna halin ko-in-kula, ko kuma haxa kai da qungiyar Rafilawa don huce fushi da rama gayya, kamar yadda wasu suke yi, cin amanar Allah ne da wannan al’umma da kuma yin kantafi da makomar ‘ya’yanmu da jikokinmu. Muna roqon Allah Maxaukaki da ya tsare wannan al’umma, ya yi mata gamon katari, kuma ya fisshe ta fargar jaji. “Ya Ubangijinmu, ka yi gafara gare mu, kuma ga ‘yan uwanmu waxanda suka riga mu yin imani, kada ka sanya qulli a cikin zukatanmu ga waxanda suka yi imani. Ya Ubangijinmu, lalle kai mai tausayi ne, mai jinqai.”(Suratul Hashri: 10). Manazarta