Wednesday 28 September 2016

TABARGAZAR YAKUBU YAHYA KTN BAYAN DAWOWARSA DAGA IRAN

KUSKUREN MALAM

KASET NE WANDA SHUGABAN YAN SHI'AR KATSINA MAL YAKUBU YAHYA YAYI BAYAN DAWOWARSA DAGA IRAN INDA YA BAYYANA HAKIKANIN ABUBUWAN DA YA GANO WANDA DA HAR YA TUBA AMMAN TALLALABIYA TA JA SHI YA KOMA

RUBUTAWA: Hasan Kabir Yar'adua

Sunday 25 September 2016

NURUN ALA NUR " BAN SAKI AHLUL BAITI BA NA KAMA SAHABBAI" (01)

*NURUN ALA NUR "BAN SAKI AHLULBAITI BA NA KAMA SAHABBAI"*

*Fitowa Ta [01]*

Daga: *_Dr Mansur Ibrahim Sokoto_*

Labarin Sheikh Ali Dan Muhammad Al-Kadhibi - Wani malami dan kasar Bahrain da Allah ya ganar da shi gaskiya ya dawo daga rakiyar Shi'a.

GABATARWA;
“Godiya ta tabbata ga Allah, godiya mai yawa, mai tsarki, mai albarka wadda ta cike sammai da qasa da duk abin da Allah ya so bayan su. Tsira da amincin Allah su tabbata ga zababben bawansa, cikamakin manzanninsa; annabi Muhammad da iyalansa da sahabbansa da duk wadanda suka bi su da kyautatawa har rana ta qarshe. Bayan haka:
Na yi wannan dan rubutu ne don in zayyana ma mai karatu wasu ‘yan nazarce-nazarce da wasu ‘yan tambayoyi da na yi ma kaina har suka ja ni zuwa ga gaskiya wacce ban taba tunanin - a can baya – zan iya janyuwa zuwa gare ta ba.
Rikici ne ba na wasa ba, kuma aiki ne ja; mutum ya bar abinda ya saba da shi kuma ya gaje shi daga iyaye da kakanni idan ya gane cewa gaskiya ita ce sabaninsa. Ba ni kadai abin ya shafa ba, da yawa wadanda suka qarar da rayuwarsu a wajen kare wata manufa ko tabbatar da wata aqida, kwatsam! Sai Allah ya ganar da su cewa ba a kan daidai suke ba. A nan ne mutum zai yi ta fama da rikici a tsakanin sa da zuciyarsa amma idan ya daure sai Allah ya yi ma sa gamon katar. A nan ne mutum zai gane cewa, riqo da rubabbiyar aqida don kawai son zama tare da ‘yan uwa da dangi bai kamata ba. Idan mutum ya yi haka to, ya yi cinikin duna wanda ba shi da riba sai hasara. A maimakon haka kamata ya yi mutum ya yi riqo da gaskiya a lokacin da ta bayyana gare shi."
Baban Khalifi
Muhammad Al-Qadhibi

TUNA BAYA;
Tun da farko na tashi a gidanmu na tarar da iyayena masu tsananin kula da riqo da addinin Shi’a. Ban yi wayon sanin mahaifina ba sai dai kawuna wanda ya riqe ni tsakani da Allah bayan mutuwar mahaifin nawa. Kawuna yana cikin shehunai masu rawani, kuma ya yi karatu a Hauza ta yankin Jadd Hafs a qasar Bahrain, bayan nan kuma ya samu qarin ilimi a babban birnin Qum na qasar Iran.
Ba zan manta yadda kawuna yake kula da mu yana ba mu tarbiyya ba, yana hana mu cudanya da bata gari don kada su gurnata mu. A ranar da ya ji ina cewa zan karanci ilimin kida a jami’a idan na gama makarantar sakandare bata ransa ya yi, sannan ya kira ni cikin lumana ya lurar da ni, ya ce, ka ga ni, sa’ad da nake yaro irinka ban samu mai dora ni a kan hanya ba. Ya rinqa rarrashi na har ya canja min ra’ayi. Wataqila da yanzu ni wani shahararren makadi ne.

Mahaifiyata ita kuma ba ta da aiki sai jiran lokutan bukukuwa wadanda ake yi akai-akai don raya addinin Shi’a. Tana bugun gaba da shiga a cikin su tana ganin – ta haka – za ta samu falalar hidimar sayyidi Husaini. Sau da yawa takan je bukukuwan ko ba ta da lafiya. In aka yi ma ta magana sai ta ce, ai shiga wannan sha’ani shi ne maganin ciwonta. Mahaifinta kuwa sana’arsa ita ce yin ganguma da ake kida da su a bukukuwan Ashura da sauran bukukuwa da makokai da ake yi a koda yaushe. Wani abin da mai karatu zai so ya sani shi ne cewa, dukkan mu muna bin tafarkin shehun malami ayatullahi.

Tunatarwa ga Jami'an tsaro Mal Baban Hamdan

Sabon saqon Boko Haram: tunatarwa ga jami'an tsaron Nigeria.

Tun ba a yi nisa ba, Marigayi Shaikh Ja'afar Mahmud Adam ya bayyanawa duniya, ya sirrintawa mahakunta hatsarin Da'awar Boko Haram, qarshe Allah Ya rubuta masa shahada a hannun miyagu yana sallar asuba daren juma'a, Allah Ya masa Rahama Ya kyautata makwanci.

A wani wa'azin Izala da aka yi a garin Maiduguri, ana tsakiyar Boko Haram, Shaikh Sani Yahya Jingir Allah Ya qara lafiya Ya kare shi,  ya hau minbari ya bayyanawa duniya Boko Haram ba musulunci bane, kuma ya shawarci mahakunta su tsananta sa ido da tsaurara matakan daqile tunani da ta'addanci irin na Boko Haram. Sakamakon haka 'yan ta'adda suka kai masa hari da boma-bomai da bindigogi yana tafsirin al-Qur'ani, Allah Ya tserar da shi, amma an rasa rayuka, ciki har da dan Shaikh Muhammad Nasir AbdulMuhyi.

Shaikh Albani Allah Ya ji qansa shi cewa ma ya yi idan dan Boko Haram ya shigo masallacin sa, za su yi dauki-ba-dadi, sabo da yadda kowa ya fada musu a kan halaka su ke amma sun qi ji, a lokacin kuma suna nema su gagari jami'an tsaro, qarshe Allah Ya masa shahada a hannun 'yan ta'adda.

Malaman sunnah da suka rasa rayukansu a kan fada da Boko Haram ba za su lisaafu ba amma hakan bai hana su ci gaba da fafatawa ba. An ga yadda Shaikh Isa Ali Pantami da Mal Idris AbdulAziz suka yi muqabala a bainar jama'a suka bayyanawa 'yan Boko Haram kuskuren fahimtar su ga addini, tun ma Muhammad Yusuf na da rai, tun Boko Haram bata fada hannun 'yan sari irin yanzu ba.

To Malaman Sunnah ba su yi qasa a gwiwa ba, amma maganar ita ce, an san tushen aqidar Boko Haram jagoran 'yan shi'a ne, Zazzaki, wanda yanzu haka yake hannu, ya kawo ta Nigeria. An sani sarai, Zakzakiy ne ya fara cewa Boko Haram ne a wajajen 80s, ya sa mutane suka fice daga makarantu, wasu ma sun gama suka riqa yayyaga takardun su. Sannan an ruwaito shi kansa Muhammad Yusuf tsohon almajirinsa ne, daga bisani ya tuba, tuban muzuru. A bakin Zakzakiy kalmar 'bara'a' ta bayyana a tsakanin matasa, wanda har yanzu 'yan shi'a suna qudurce da ita, har da wani Chemist na gargajiya wai shi 'Bara'a Chemist'.

Ma'anar bara'a ita ce abin da Boko Haram suka yi, wato raba gari da duk wani tsarin gwamnatin Nigeria sabo da ba tsarin Allah bane, ba tare da la'akari da halin da aka sami kai a ciki na zamantakewa tsakanin Musulmi da wadanda ba Musulmi a qasa daya ba. Qarqashin wannan ne za a ji suna cewa 'ba hukuma sai ta Allah' ma'ana ba su yarda da gwamnatin Nigeria ba sai ta Zakzakiy da ta Iran kamar dai yadda Boko Haram ba su yarda da ita ba sai ta Shekau da ISIS.

Wannan ita ce Aqidar 'yan shi'a kuma ba sa musu a kan haka.

Duk wanda ya bibiyi maganganun Zakzakiy a kan Boko Haram, ya san aqidar Zakzakiy ita ce 'ba Boko Haram, gwamnati ce Boko Haram'. Mutane da yawa, la'alla har wasu cikin jami'an tsaro, basu fahimci me Zakzakiy yake nufi ba. Da yawa suna fahimtar yana nufin babu wasu mutane 'yan Boko Haram masu aqidar Boko Haram, amma ba haka bane. Zakzakiy ya san awai su, amma yana nufin su 'yan Boko Haram su ne suka fi kusa da gaskiya, ita gwamnati ita ce Boko Haram, 'yarta'adda.

Don haka Zakzakiy yana ganin za su iya haduwa da Boko Haram don a hambarar da gwamnatin Nigeria daga baya sa daidaita tsakanin su, amma ba za su iya haduwa da gwamanti su ga bayan Boko Haram ba in yaso sa sasanta tsakanin su daga bisani.

Kamar yadda zai wa gwamnati wahala ta samo kan Boko Haram cikin laluma sabo da alaqar da Boko Haram din ta qulla da ISIS, haka ma 'yan Shi'a, domin su kuma daga Iran ne kawai za a basu umarni su karba. Ita kuma Iran ba za ta bada wani umarnin gaske wanda ba na tada hankali da yi wa hukumomi bore da gwagwarmayar juyin-juya-hali ba.  Za a iya ganin haka, a yayin da mahakuntan Saudi Arabia ke hado hancin qasashen musulmi don yaqar munanan aqidu irin na ISIS da Boko Haram da Hizbolla da sauransu, ita Iran baza mugga-muggan makamai take yi a qasashe, hatta nan Nigeria an kama jirgin ruwa maqare da makamai daga qasar Iran, da kuma wasu dandazon wasu makaman a Kano a hannun 'yan shi'a.

Alhamdu lillah, malaman sunnah sun yi aiki tuquru wajen tsare tunani da aqidar jama'a, kuma ba fargabar ko wace irin matsala, amma babbar matsar da dole za ta kasance in ba a yi wa tufkar hanci mai qarfin gaske tun qafin ta fara bajewa ba ita ce ta shi'a.

Insha Allah za mu ci gaba da bayyana hatsarin 'yan shi'a a qasa da yadda za su zo su fi Boko Haram barna idan ba a dauki qwararan matakai tun yanzu ba.

Allah Ya tsare mu da tsarewarsa Ya bamu zaman lafiya a qasarmu Nigeria.

HANA KARUWANCI DA FATAUCIN MIYAGUN KWAYOYI A Karamar Hukumar Kafur

HANA KARUWANCI DA FATAUCIN MIYAGUN KWAYOYI  A Karamar Hukumar Kafur

Daga Hassan Kabir Yar'adua

HARAMTA KARUWANCI DA KULLE GIDAJEN GIYA/KAYAN MAYE

A wata zantawa da nayi ta wayar tarho da kantoman riko na karamar Hukumar Kafur a jahar Katsina Alh Hamza Umar Nasarawa (Mai Garin Sabuwar Kasa) ya bayyana cewa sakamakon zaman da kwamitin tsaro na hukumar tayi kan korafi da aka yi game da lalacewar tarbiyyar matasa wanda karuwanci da gidajen giya/kayan maye ke haifarwa hakan yasa mu ka ga babu mafita illa muyi abunda Allah ya umarce mu (masu madafun iko) muyi na hana karuwancin da fataucin miyagun kwayoyin.
Shugaban karamar hukumar ya bayyana cewa sun sanya dokar kulle gidajen karuwanci da sha da fataucin kwayoyi a gaba dayan yankin na Kafur, duk wanda aka samu yana saidawa ko sha ko zuwa gidajen karuwancin to Doka za ta hau kanshi. Daga karshe ya bayyana cewa an rufe gidajen nan da ake masha’a.
Wannan alkairin na da nasaba da canjin aiki da aikawa wani malamin addinin musulunci daga karamar hukumar Katsina zuwa Karamar hukumar Kafur, wanda ya bada gudumuwa kwaran gaske wurin tabbatar da wannan aikin alkhairin. Malamin yanzun haka yana ta kokarin sanya al’ummar yanki bisa koyarwar addinin musulunci ta hanyar gabatar masu da majalisai na karatu da kuma kokarin tabbatar da da’ar ma’aikatan yankin.
Muna fatan sauran kananan hukumomi da jahohi su ma su yi koyi da wannan karamar hukumar domin dorewar rayuwa ingantaciyya ta musulunci.

Thursday 22 September 2016

TAMBAYOYI 70 GA YAN SHI'A

AQIDAR SHI'A AKAN IMAMA Mal Salihu Baban Takko

AIKIN HAJJI A WAJAN SHI'A Daga Majalisin Mal Baban Hamdan

TARIHIN SHEIKUL ISLAM IBN TAIMIYYAH

TARIHIN SHEHIN MUSULUNCI IBN TAIMIYYA

QISSAR FARKE/TAUNA HANTAR HAMZA R.A Daga Mal Salihu Baban Takko

QISSAR FARKE CIKI/CIREWA DA TAUNA HANTAR HAMZA BN ABDULMUTALLAB BN HASHIM (RA).

BY: SALIHU B. TAKKO

SUNA : HAMZA BN ABDULMUTALLAB BN HASHIM.

MATSAYI : SAHABI/BAFFAN MANZON ALLAH (SAW), KUMA 'DAN UWANSA NA SHAYARWA.

FALALA : SHUGABAN SHAHIDAI/TAMBAYO AUREN KHADIJAH BINT KHUWAILID (RA) WA ANNABI (SAW).

SHEKARAR MUSULUNTA : SHEKARA TA BIYU (2) HIJRIYYAH.

'DAN UWAN HADI A MUSULUNCI : ZAID BN AL-HARITH (RA).

SUNAR WANDA YA KASHE SHI : WAHSHIYYU BN AL-HARB
WURI DA SHEKARAR MUTUWA : UHUD/SHEKARA TA 3 HIJRIYYAH/YANA DA SHEKARU 57

(SABABI)

MASU TARIHI SUN AMBACI SABABBUN KASHE SHI (RA) BISA SABANIN MAGANGANU GUDA BIYU, WASU SUNCE :

1). A RANAR YAQIN BADR SHI YA KASHE TU'AIMAH BN ADIY AN-NUFALIY, MUTUMIN DA KE BAFFA WA JUBAIR BN MUT'IM, WANDA HAKAN YA SANYA SHI ALWASHIN DAUKAN FANSA.
WASU KUMA SUKA CE : 2). A RANAR YAQIN BADR YA KASHE UTBAH BN RABI'AH DA 'DANSA, UTBAH SHINE MAHAIFIN MATAR ABU SUFYAN (RA), HINDU BINT UTBAH (RA). A WANNAN LOKACIN BA TA MUSULUNTA BA, ITA MA HAKAN YA SANYATA ALWASHIN DAUKAN FANSA, TA KIRA WAHSHIY TAYI MASA ALKAWARIN LADAR KUDI IDAN HAR YA KASHE HAMZA (RA).

AMMA MAGANA MAFI RINJAYE DA SHAHARA ITA CE NA FARKO, KAMAR YADDA ZAMU GANI DAGA BAKIN WANDA YAYI WANNAN KISAR DA TA BATA RAN MA'AIKI (SAW) DA SAURAN MUMINAI.

(QISSA)

MANZON ALLAH (SAW) YA TAMBAYE SHI YADDA YAYI WANNAN KISA, SAI YACE :

كنت ﻏﻼﻣﺎ لجبير بن مطعم وكان عمه ﻃﻌﻴﻤﺔ بن عدي قد أصيب يوم بدر، فلما سارت قريش إلى أحد قال لي جبير : إن قتلت حمزة عم محمد بعمي ﻓﺄﻧﺖ عتيق. قال : فخرجت مع الناس وكنت رﺟﻼ ﺣﺒﺸﻲا أقذف بالحربة قذف الحبشة قل ما ﺃﺧﻄﻰء بها ﺷﻴﺌﺎ... قال : وهززت ﺣﺮﺑﺘﻲ حتى إذا رضيت منها دفعتها عليه، فوقعت فى ثنته حتى خرجت من بين رجليه وذهب لينوء نحوى فغلب ﻭﺗﺮﻛﺘﻪ وإياه حتى مات، ثم أتيته فأخذت حربتي، ثم رجعت إلى العسكر وقعدت فيه ولم ﻳﻜﻦ لي بغيره حاجة ﺇﻧﻤﺎ قتلته لأعتق، ﻓﻠﻤﺎ قدمت مكة عتقت."

راجع : البداية ﻭﺍﻟﻨﻬﺎﻳﺔ لإبن كثير : 4/18

"NA KASANCE BAWA GA JUBAIR BN MUT'IM, ALHALI BAFFANSA TU'AIMAH IBN ADIY AN KASHE SHI A YAQIN BADR, YAYIN DA QURAISHAWA SUKA TASAMMA ZUWA UHUD, SAI JUBAIR YACE MUN : IDAN HAR KA KASHE HAMZA, BAFFAN MANZON ALLAH RAMAKON BAFFA NA, KAI 'ENTACCE NE. YACE : SAI NA FITA TARE DA MUTANE, NA KASANCE MUTUM BAHABASHE, NA KWARE WURIN JIFA DA MASHI, JIFAR HABASHAWA KUWA QALILAN TAKE FADUWA KASA BANZA ..... YACE : (yayin da) NA DAIDAITA SAITI HAR NA AMINTA TA DAIDAIDONSA (akan sa), SAI NA SAKE MAKAMIN AKAN SA, YA SAME SHI A CIBAYA HAR SAI DA YA FITO TA TSAKANIN KAFOFINSA BIYU, YAYI YUNKURIN RUNGUMATA, AMMA SAI MAKAMIN YAYI GALABA AKANSA, NI KUWA NA BARSHI DA SHI (ban cire masa ba) HAR YA FADI YA MUTU. BAYAN WANI LOKACI SAI NA ZO KANSA NA CIRE MASHI NA, SANNAN NA KOMA CIKIN RUNDUNA NAYI ZAMA TA, DA MA BANI DA BUKATAR KOWA SAI SHI, KAWAI NA KASHE SHI NE DON IN 'ENTU, YAYIN DA NA KOMA MAKKAH SAI AKA 'ENTA NI."
WANNAN RUWAYA ITA CE INGANTACCIYA.

(YADDA ISNADIN MAGANAR TAUNA HANTA TAKE A RUWAYA)

قال الإمام أحمد : حدثنا ﻋﻔﺎﻥ، حدثنا حماد، ﺣﺪﺛﻨﺎ عطاء بن السائب، عن الشعبي، عن ابن مسعود قال : .... فنظروا فإذا حمرة قد بقر ﺑﻄﻨﻪ، وأخذت هند كبده فلاكتها، فلم تستطع أن تأكلها، فقال رسول الله ص : أأكلت شيئا؟ قالوا لا، قال : ما كان الله ليدخل شيئا من حمزة فى النار..."
ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺃﺣﻤﺪ ﻓﻰ ﻣﺴﻨﺪﻩ، ﺑﺮﻗﻢ 4414

"IBN MAS'UD YACE : .... DA SUKA DUBA SAI GA HAMZA AN FARKE CIKINSA, HINDU TA CIRI HANTARSA TA TAUNA, AMMA BA TA IYA TA CI BA, SAI MANZON ALLAH (SAW) YACE : SHIN TA TAUNA WANI ABU DAGA JIKIN HANTAR? SAI SUKA CE, A'A! SAI YACE : ALLAH BAI KASANCE ZAI SHIGAR DA WANI ABU DAGA JIKIN HAMZA CIKIN WUTA BA..."

WANNAN RUWAYA BA TA INGANTA BA, DOGARO DA DALILAI KAMAR HAKA :

1). AL-HAFIZ IBN KATHIR BAYAN YA KAWO WANNAN QISSAR, SAI YACE :

تفرد به أحمد، ﻭﻫﺬﺍ إسناد فيه ضعف أيضا، من جهة عطاء بن السائب، والله أعلم." البداية ﻭﺍﻟﻨﻬﺎﻳﺔ : 4/39

"AHMAD YA KADAITA DA WANNAN RUWAYA, HAR WA YAU WANNAN ISNADI NE MAI RAUNI DAGA BANGAREN ATA'U BN SA'IB. WALLAHU A'ALAM."

2). BABBAN MALAMIN SANIN MAZAJEN HADISI, KUMA 'DAN BIJIMIN MASANIN ILMIN HADISI DA MAZAJENSA, ABU MUHAMMAD, ABDURRAHMAN IBN ABIY HATIM, BAYAN YA AMBATO WANNAN RUWAYAR SHA'ABIY DAGA IBN MAS'UD, SAI YACE :

ﻫﺬﻩ ﺍﻟﺮﻭﺍﻳﺔ ﻟﻢ ﺗﺼﺢ، ﻷﻥ ﺍﻟﺸﻌﺒﻲ ﻭﻫﻮ ﻋﺎﻣﺮ ﺑﻦ ﺷﺮﺍﺣﻴﻞ ﻟﻢ ﻳﺴﻤﻊ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻣﺴﻌﻮﺩ. ﻭﻗﺎﻝ : سمعت ﺃﺑﻲ يقول : لم يسمع ﺍﻟﺸﻌﺒﻲ عبدالله بن ﻣﺴﻌﻮﺩ."

المراسيل : ص160
"WANNAN RUWAYAR BATA INGANTA BA, DOMIN SHA'ABIY, WATAU AAMIR BN SHARAHIL BAI JI WANI ABU BA DAGA ABDULLAHI BN MAS'UD. KUMA YACE : NA JI BABA NA YANA CEWA : SHA'ABIY BAI JI DAGA ABDULLAHI BN MAS'UD BA."

(SAKAMAKO)

QISSAR TAUNA = DA'IF

GWARGWADON HUKUNCIN MASANAN DA DUNIYAR MUSULUNCI TAFI AMINTA DA SU, KUMA TA SALLAMA MASU AKAN SUNE MASANA RUWAYA, WANNAN QISSAR TAUNA HANTA DAI TA NA DA RAUNI (la'ifiya ce), BABU WATA QURA AKAN HAKAN.

(NASIHA)

WANNAN QISSAR DAI BA TA TABBATA BA. MU KUWA MUN KAWO TA NE DON NASIHA GA MAI NEMAN SHIRIYA DA RABAUTA. DON A RASHIN SA'A AKE SAMUN WASU DAGA CIKIN MUTANE DA KE DANGANTA KANSU DA MUSULUNCI, DOGARO DA WANNAN LABARI MARAR NAGARTA SUKE JIFA DA FADIN MUNANAN KALAMAI AKAN SURKUWAN MA'AIKI (SAW), WANDA SAHABIYA CE, MATAR SAHABI, MAHAIFIYAR SAHABBAI, MAHAIFIN MARUBUCIN WAHAYI DA WASIKUN MA'AIKI (SAW), KUMA KAMAMMIYAR MACE.

DON HAKA MAI RABO SAI YA FADAKU, DON YA KUBUTAR DA ADDININSA DA DAUKAN ALHAKIN NAGARTATTUN MUTANE, KUMA DON RABAUTAR LAHIRARSA.
ALLAH SHI KARA SHIRYAS DA MU GA ABUN DA YA YARDA DA SHI DA KARA MANA SON MUSULUNCI DA AIKI DA SHI.

Tuesday 20 September 2016

Ghadir Khum Daga Shehin Malamai Dr. Muhd Sani R/Lemu

CIKAKKEN BAYANI AKAN GHADIR KUM

Daga Bakin: Dr. Muhammad Sani Umar R/Lemu

Dama haka abin yake, lallai Allah ya taimake ni da na saurari wannan tattaunawa ta Dr Muhammad Sani Umar R/Lemu, tabbas Dr ya tabbata bijimin Malami mai ilimi da kuma adalci. An kusa a ruftani amma Allah ya taimake ni gaskiya tayi halinta. Kai Alhamdulillah!!! A’ah kai Jama’a!!!

• Wai kasan mai ake kira da GHADIR KUM?
• Mai ya faru ne a wannan waje?
• Da gaske ne Annabi yayi Huduba ko kuma dai kawai shifcin gizo ne?
• Idan yayi Huduba to mai yace?
• Anya ba’ayi karin gishiri a Hudubar ba idan ma har ya tabbata yayi Hudubar?
• Kai jama’a!!! Karba fa nima na zama cikin Jahilai wanda ake wasa da hankalinsu!
• Bazan taba yadda wannan al’amari ya wuce ni ba, sai naji yaya abin yake!

Don jin cikakken abin da wannan bayani ya kunsa kai tsaye kayi downloading ta wannan link dake kasa. Ayi sauraro lafiya……………………….

http://www.dandalinsunnah.com/multimedia/amb/others/Lecture/DrSani/Ghadir%20Kum.mp3

Idan wannan bai yiba a wayar ka, za ka iya downloading ta wannan link din na kasa.

http://files.mboxdrive.com/1470856927/Ghadir%20Kum.mp3

saboda samun karin bayani adai kan shi wannan batu kar a rifta da kai, ga rubutattun makala da Shehin Malami Salihu Baban Takko ya rubuta ta waddannan links dake kasa

darasi na farko: https://m.facebook.com/photo.php?fbid=4848453588006&id=1796968402&set=a.1724436649535.69364.1796968402&refid=17

Darasi na biyu: https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=4852911379448&id=1796968402&refid=17

Allah ya kara nuna mana gaskiya gaskiya ce ya bamu ikon binta, ya nuna mana karya karya ce ya bamu ikon guje mata.

Monday 19 September 2016

GHADIR KUM: KALUBALE GA YAN SHI'A {D r. Mansur Sokoto}

-GHADIR: KALUBALE GA ‘YAN SHI’A(Dr. Mansur Sokoto)

INGANTACCEN LABARIN GHADIR:
Kalmar Ghadir a larabce, tana nufin wurin da ya tara ruwa da ciyawa.
“Ghadir Khum” sunan wani tafki ne da yake a yankin Juhfa, kilomita 15 daga Rabigh. Nisan sa daga Makka kilomita 160 ne.
Labarin Ghadir:

Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallam ya aiki Khalid dan Walid a matsayin kwamandan rundunar da za ta yi yaki a kasar Yaman daf da fara aikin Hajjin shekara ta 10H, hajjin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam da kansa ya jagoranta.
Bayan da rundunar musulmi ta ci nasara sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam ya aika Sayyidi Ali don ya kula da sha’anin Ganimar da aka samu.
Ali Radhiyallahu Anhu ya raba Ganima, kuma ya cire hakkin Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam na Khumusi kamar yadda Alkur’ani ya zayyana. Daga ciki kuma ya cire ma kansa wata kuyanga da ta ba shi shawa.
Sayyidi Ali bai bata lokaci ba ya zarce zuwa Makka don ya riski maigidansa Sallallahu Alaihi wa Sallam a wurin aikin Hajji. Ya kuma wakilta wani daga cikin sojoji akan sauran aikin da ya rage.
Domin ya dadada ran sojojin, wakilin Sayyidi Ali ya raba ma su tufafi kyawawa daga cikin abin da aka ganimanto. Ya kuma yi ma su izini kowa ya hau rakumin da yake so daga cikin kayan Ganima. Kafin haka, sojoji sun gabatar da bukatar haka ga Sayyidi Ali amma bai amince ba. Sai ya ce ma su, rabonku sai an je Madina.
Sojojin wannan runduna sun hadu da Sayyidi Ali tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam a kan hanyar su ta dawowa bayan gama aikin Hajji. Sayyidi Ali ya nuna rashin jin dadinsa a kan wannan rabo da aka yi kafin lokacin yinsa. Nan take ya yi umurni duk su sauka daga rakuman, suka kuma mayar da tufafin da aka raba masu. Rayukansu sun baci matuka a kan haka kuma sun kai karar sa ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam suna zargin sa da cewa ya kuntata masu.
Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam ya iso Ghadir Khum, kuma ya lura da fushi a fuskar wadannan sojoji. Ya yi huduba yana tambayar su
(!ألستُ أولى بالمؤمنين من أنفسهم؟)
“Ashe ban fi muminai cancanta da kawunansu ba?” Suka ce masa, haka ne. Sai ya ce,
(فمن كنت مولاه، فعلي مولاه)
“To, duk wanda nake majibincinsa Ali ma majibincinsa ne”. Ma’ana, bai dace ku bata ranku a kan hukuncin da ya yi ba.
Da wannan babban jagora ya kwantar da wannan rikici da rashin fahimta, ya kuma nuna wajabcin a yi ma jagora da’a, sa’annan ya bayyana matsayin dan uwansa Sayyidi Ali a wurin muminai. Sojojin suka ba shi hakuri, suka gane matsayinsa, suka wuce Madina tare da sauran ayarin mahajjata da suke tare da shi.
Wannan shi ne abin da ya faru. Illa iyaka.

TATSUNIYAR GHADIR
‘Yan Shi’a sun ribaci wannan abin da ya faru kuma ya zo ya wuce kamar sauran ire-irensa. Suka fankama shi, suka fadada shi, suka mayar da shi wani gagarumin bukin nadin sarauta. Suka kuma jefi duk Sahabban Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam da kin Allah da kauce ma gaskiya, da jayayya da wannan nadi da suka ce an yi.
Wannan akidar ta Ghadir a matsayin ranar buki ba a san ta a cikin tarihi ba sai bayan sama da shekaru 340 gwamnatin Shi’a ta Buwaihawa ta kago wannan bidi’a a kasar Iraqi. Suka mayar da ranar 18 ga watan Dhul Hajji a matsayin ranar wannan buki ta kowace shekara. Sukan taru a wurin kaburburan manyansu suna ta kururuwa suna la’antar masoyan Allah wadanda suka ce sun kauce ma umurni Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam da ya bayar na mika mulki ga maigida Sayyidi Ali.
Sun kago ruwayoyi barkatai a kan falalar wannan rana, cikin su har da cewa wai, Imam Ar-Ridha ya ce, da mutane sun san matsayi da falalar wannan rana da Mala’iku sun rinka musafaha da su har sau goma a kowace rana.
Haka kuma sun kitsa tatsuniyoyi masu nuna wai, manyan Sahabbai sun yi ma Ali mubaya’a amma a munafurce, sannan suka shirya makarkashiyar kashe Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam. A cikin su kuma wai har da duk sauran tara daga cikin mutane goma da Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam ya yi ma su bushara da aljanna.

KALUBALE GA ‘YAN SHI’A
Muna kalubalantar ‘yan Shi’a a kan wannan batu da wadannan tambayoyi:
1. Idan wannan magana ta Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam cewa “Duk wanda nake majibincinsa Ali ma majibincinsa ne” tana nuna wajabcin shugabantar da shi, to me za ku ce game da fadar Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam “Ko wace al’umma tana da amintacce, mu kuma amintaccenmu a cikin wannan al’umma shi ne Abu Ubaida”? Wa ya fi cancanta a cikin su kenan?
2. Idan har gaskiya ne an yi wannan nadin kamar yadda kuke cewa, me ya sa ba a umurci Sayyidi Ali da ya ci gaba da ba da Sallah ba musamman bayan da ciwon ajali ya kama Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam?
3. Me ya sa ba ayi wannan bukin a zamanin da Sayyidi Ali yake Khalifa ba ko Sayyidi Al-Hasan ko a zamanin duk Imamanku goma sha daya da suka rayu kafin Malam Na-boye (Mahadinku) ya zo duniya? Me ya sa sai lokacin da Buwaihi Bafarise mai kamun kifi ya kafa gwamnati sannan aka fara wannan buki a shekarar 352H?
4. Idan hudubar Ghadir tana nufin nadin sarauta ne, me ya sa ba ayi ta a Makka ba in da duk alhazan duniya suka taru su sama da mahajjata dubu dari?
5. Ashe Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam bai yi hudubobi a can Makka da Minna da Arafat ba? Me ya sa bai ware huduba ta musamman a kan wannan babbar maganar ta halifancin Sayyidi Ali ba?
6. Ashe Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam bai yi huduba a kan jinainai da dukiyoyi a ranar babbar sallah ba? Ashe bai yi ma al’umma wasici da muhimman abubuwan da suke bukatar sani ba? Ita wannan maganar ba ta kai muhimmancinsu ba ne ya manta da ita? Me ya sa sai da aka watse, kowa ya bi hanyar garinsu saura mutanen Madina kawai suka rage sannan ya yi wannan magana a cikin sunkurmin daji a tafkin Ghadir?
7. Ya ya aka yi Sahabbai suka riwaito wannan hudubar ta Ghadir alhalin kun ce sun boye kaso biyu cikin uku na Alkur’ani masu bayyana falalar Ahlulbaiti?
8. Kun ce duk rikicin da musulmi suka shiga a tsawon tarihi dalilin kauce ma wannan umurni na ranar Ghadir ne da sahabbai suka yi. Me ya sa Alkur’ani ya yi biris da labarin Ghadir?
9. Allah Tabaraka wa Ta’ala ya saukar da sura ta musamman a cikin Alkur’ani kan maganar Hudaibiya da mubaya’ar da sahabbai suka yi ma Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam da har wuri da bishiyar da suka yi mubaya’a a karkashinta, kuma ya ce ya yarda da su a kan haka bisa ga abin da ke cikin zukatansu na imani da ikhlasi. Kuma ya ce, a lokacin da suke yi ma Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam mubaya’a hannun Allah yana saman nasu. Me ya sa idan har an yi wannan mubaya’a Allah bai kawo ta ba a cikin Alkur’ani?
10. Mubaya’ar da mata suka yi ma Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam ita ma Allah ya kawo labarinta cikin Suratul Mumtahana. Shin ita wannan mubaya’ar ta Ghadir ba ta da muhimmanci ne irin wannan mubaya’ar mata ko kuwa?
‘Yan Shi’a ku ji tsoron Allah! Malamanku suna zargin Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam da boye wannan bayani wai a cikin Makka har suna cewa a kan wannan boyewar da ya yi sai da Allah ya saukar da ayar ”Ya kai wannan manzo ka isar da sakon da aka saukar ma ka daga wurin Ubangijinka. Idan kuwa har ba ka yi ba to, ba ka isar da sakonsa ba. Kuma Allah zai kare ka daga mutane”. To, sannan wai, ya tsaya a Ghadir Khum ya isar da wannan sako. Ku ji tsoron Allah! Ku darajanta manzonsa, ku koma ga gaskiya.
Wallahi, Sayyidi Abubakar da Sayyidi Umar da Sayyidi Usmanu da ma duk sauran sahabbai almajiran Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam ba su jiye ma Sayyidi Ali da kome. Kuma ba su da wani kwadayi ga duniya balle su nemi shugabanci. Allah Ta’ala da kansa cewa ya yi a kan su:
(للفقراء المهاجرين الذين أُخرجوا من ديارهم وأموالهم يبتغون فضلا من الله ورضوانا وينصرون الله ورسوله أولئك هم الصادقون)
“-A bayar da Fai’i- ga talakawa Muhajirai wadanda aka fitar da su daga gidajensu da dukiyoyinsu suna neman falala daga Allah da yarda, kuma suna taimakon Allah da manzonsa. Wadancan su ne masu gaskiya”
To, ka ji. An kore su daga garuruwansu, aka kwace dukiyarsu kuma a cikin zukatansu ba zaman gida ko mallakar dukiya ne a gabansu ba. Babban gurinsu shi ne taimakon Allah da manzonsa. Ka kuma ji Allah ya ce ma su masu gaskiya. Don Allah ta ina wadannan za su yi kwacen mulki kuma har su shirya ma Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam makarkashiyar kisan sa?!
Ya Allah! Ka shiryar da bayinka, ka ceto su daga muguwar akidar da Farisawa ‘yan bautar wuta suka kago suka lullube ta da rigar musulunci don su halaka su. Allahumma Ameen

LALACIN GABOBI DA LALACIN KWAKWALWA! Daga Sheik Aliyu Said Gamawa

LALACIN GABOBI DA LALACIN KWAKWALWA!

Wannar Muhimmiyyar Lacca ce wacce Sheikh  Aliyu Said Gamawa (Sarkin Malaman Gamawa) Ya gabatar.  Kuma tana kunshe da Nasihu Masu Tsada da Muhimmanci ga Al'umman Musulmi Musamman Matasa  a wannan Zamani da muke ciki.

Kana iya sauraron Cikakkiyar Laccar ta wannan Link dake Kasa:

http://www.dandalinsunnah.com/multimedia/amb/muhadara/1437/LalacinGabobi_da_LalacinKwakwalwa_By_ShAliyu_Sa'id_Gamawa.mp3

MINBARIN SUNNAH
Facebook : @ http://www.fb.com/minbarinsunnah

WHATSAPP : @ +2347066677977

Sunday 18 September 2016

Matar Babban Malamin Hadisin duk duniya ta karba kiran ubangiji

Abdulmuttalib Abdullahi
INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR
RAJI'UN:
ALLAH YAYIWA UMMUL FADHIL
YUSRA ABIDEEN RASUWA A
SAFIYAR YAU LAHADI, MATAR
BABBAN MALAMIN HADISI
MASANIN ALLAH DA SUNNAH
SHAIKH NASIRUD DEEN ALBANY
RASUWA,TANA YER SHEKARU
86.
ALLAH YASA ALJANNAH CE
MAKOMARTA.

Saturday 17 September 2016

Mal Baban Hamdan
Sanarwar gaggawa.
A FADA A CIKA SAI SAUDIYYA: A wani zama da aka yi da babban limamin Haramin Makkah ga babban Malamin mu, Shaikh Dr Mansur Ibrahim Sokoto, Shaikh Professor Abdurrahman Sudais yake sanar da cewa akwai wata jami'a ta musamman da Qasa mai Tsarki za ta bude don horas da masu sha'awar karatun Shari'a ko Ilimin Al-Qur'ani, qafin a shiga sabuwar Shekarar 1438.
Har na cika da mamakin ga shi yau ana 14/12/1437 (saura sati biyu shekara ta qare) amma ba mu sami labarin an bude wannan jami'a mai albarka ba ballantana a fara daukar dalibai, kwatsam sai ga sanarwa ashe an bude wannan jami'a har an fara daukar dalibai kamar yadda Shaikh Sudais ya tabbatarwa su Mallam tun 20/11/1437 kuma za a ci gaba da dauka har 20/12/1437 a kuma fara karatu 1/1/1438 insha Allah.
Don haka a madadin Mallam ina shelanta sanarwar daukar dalibai maza da mata, a matakin karatun Diploma (shekara 1) ko Degree (shekara 4).
Za a iya yin karatu a can garin Makkah ga maza, maza da mata kowa zai iya yin rajistar karatun distance learning.
Ba a biyan kudin makaranta, karatun kyauta ne, kuma ba qa'idar shekarun dalibi. Admission nan take ne ga wanda zai yi karatun distance learning, wanda kuma zai je can Makkah za a ba shi admission nan take amma za a qara tantance shi.
Matan aure da ma'aikata da zaunannu wannan babbar dama ce da za a yi karatu daga gida, a sami ilimi mai nagarta ga kuma gangariyar takardar shaidar kammala degree ta Jami'ar Ummul Qura, karbabbiya a duk fadin duniya; masu sha'awar zuwa can Saudia kuwa sun fi kowa morewa.
Sunan makarantar 'Jami'atu Imam al-Da'wah' shugabanta Professor Shaikh Abdurrahman Sudais, babban limamin Haramin Makkah, ga kuma link din cike form. Da fatan za a cike kuma a yada wannan sanarwa ta shiga lungu da saqo domin yau saura kwana 6 kacal a rufe.
Allah Ya sa mu dace.
Arabic: http://mojamah.com/register.php
English: http://mojamah.com/register-en.php

Ghadeer Khum 2

BIKIN IDIN GHADIR KHUM KO GHADAR KHUM (Ranar bikin Idin Yaudara/Ranar bikin Idin sanar da kafuwar Addinin Zagin Sahabbai) 18th/DHUL HIJJAH (2) Bismillahi, wassalatu wassalamu ala Rasulillah, wa ala Alihi wa Ashabihi Ajma'een. A shari'ar da Manzon Allah (saw) yazo da shi daga wurin Allah Ta'alah, akwai kebantattun ranakun bukukuwan Idi guda uku (3) wadanda bassu da na hudu. Wadannan shar'antattun idi na Musulunci sune : 1. IDIN BABBAN SALLAH (sallahr lahiya) 2. IDIN KARAMAR SALLAH (karamar sallah) 3. IDIN SATI (ranar Jumu'a) Iyakan bukukuwan IDI kenan da Addinin Musulunci ya sani, basu da na hudunsa. Saboda haka, duk wani IDI bayan wadannan ukun, toh lallai bakon haure ne ba Idin Addinin Musulunci bane, don haka zaka ga duk cikin littafan fiqhun Addinin Musulunci sune ake kawo su da hukunce hukuncensu kamar ; wajibcinsu, mustahabbansu, ladubbansu, dss. Sabanin wadannan zaka babu shi ballantana hukunce hukuncen da ya kebantau da su. Shar'antuwar wadannan idi guda uku sunzo da nassoshi kamar haka : (1-2). BABBA DA KARAMAR SALLAH (Sallahr Lahiya) : ﻋﻦ ﺃﻧﺲ ﺽ ﻗﺎﻝ : ﻗﺪﻡ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺹ ﻭﻷﻫﻞ ﺍﻟﻤﺪﻳﻨﺔ ﻳﻮﻣﺎﻥ ﻳﻠﻌﺒﻮﻥ ﻓﻴﻬﻤﺎ ﻓﻰ ﺍﻟﺠﺎﻫﻠﻴﺔ، ﻓﻘﺎﻝ : ﻗﺪﻣﺖ ﻋﻠﻴﻜﻢ ﻭﻟﻜﻢ ﻳﻮﻣﺎﻥ ﺗﻠﻌﺒﻮﻥ ﻓﺒﻬﻤﺎ ﻓﻰ ﺍﻟﺠﺎﻫﻠﻴﺔ، ﻭﻗﺪ ﺃﺑﺪﻟﻜﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻬﻤﺎ ﺧﻴﺮﺍ ﻣﻨﻬﻤﺎ : ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻨﺤﺮ ﻭﻳﻮﻡ ﺍﻟﻔﻄﺮ . " ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ )١١٣٤ ) "Daga Anas bn Malik r.a yace : Annabi s.a.w ya taho (madina) alhali mutanen Madina suna da wasu ranaku biyu a jahiliyya da suke wasanni a cikinsu, sai Yace : Na taho gareku kuna da ranaku biyu da kuke wasanni cikinsu a jahiliyya, hakika Allah ya musanya muku su da wasu biyun mafiya alheri da su : ranar idin yanka da ranar idin karamar sallah." (3). IDIN SATI (Ranar Jumu'a) : Daga Anas bn Malik (raa) yace, Annabi (saw) yace : ﺃﺗﺎﻧﻲ ﺟﺒﺮﻳﻞ ﺑﻤﺜﻞ ﺍﻟﻤﺮﺁﺓ ﺍﻟﺒﻴﻀﺎﺀ، ﻓﻴﻬﺎ ﻧﻜﺘﺔ ﺳﻮﺩﺍﺀ، ﻗﻠﺖ : ﻳﺎ ﺟﺒﺮﻳﻞ، ﻣﺎ ﻫﺬﻩ؟ ﻗﺎﻝ : ﻫﺬﻩ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ، ﺟﻌﻠﻬﺎ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻴﺪﺍ ﻟﻚ ﻭﻷﻣﺘﻚ ..... ﺍﻟﺦ ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺑﻮ ﻳﻌﻠﻰ ) ٤٢١٣( ﻭﻏﻴﺮﻩ ﺑﺴﻨﺪ ﺣﺴﻦ . "Annabi s.a.w yace : Jibrilu yazo min da kwatankwacin gilashi fari, a cikinsa akwai digo baqi, sai Nace : Ya Jibrilu, mecece wannan? Yace : wannan itace Jumu'a, Allah ya sanyata IDI gareka da al'ummarka ...." Wadannan sune kadai ranakun Idi na Musulunci, duk wani abu koma bayan wannan ba shi asali a karantarwan Manzon Allah (saw), don haka ne yayin da wani bayahude yazo wurin Khalifa Umar 'Dan Khattab (ra) yake kokarin ya kwadaitar da Musulmai su riki ranar da Ayahr "Alyauma akmalTu lakuum dinaakum..." wacce ta sauka a filin Arfah a matsayin ranar Idi, sai Umar r.a ya nuna masa sun san wuri da ranar da Ayahr ta sauka, amma musulmai bassu yin hakan. ﻋﻦ ﻃﺎﺭﻕ ﺑﻦ ﺷﻬﺎﺏ ﻗﺎﻝ : ﺟﺎﺀ ﺭﺟﻞ ﻣﻦ ﺍﻟﻴﻬﻮﺩ ﺇﻟﻰ ﻋﻤﺮ ﺑﻦ ﺍﻟﺨﻄﺎﺏ ﻓﻘﺎﻝ ﻟﻪ : ﻳﺎ ﺃﻣﻴﺮ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ، ﺁﻳﺔ ﻓﻰ ﻛﺘﺎﺑﻜﻢ ﺗﻘﺮﺀﻭﻧﻬﺎ، ﻟﻮ ﻋﻠﻴﻨﺎ ﻣﻌﺸﺮ ﺍﻟﻴﻬﻮﺩ ﻧﺰﻟﺖ ﻻﺗﺨﺬﻧﺎ ﺫﻟﻚ ﺍﻟﻴﻮﻡ ﻋﻴﺪﺍ، ﻓﻘﺎﻝ : ﺃﻱ ﺁﻳﺔ؟ ﻗﺎﻝ : >> ﺍﻟﻴﻮﻡ ﺃﻛﻤﻠﺖ ﻟﻜﻢ ﺩﻳﻨﻜﻢ ﻭﺃﺗﻤﻤﺖ ﻋﻠﻴﻜﻢ ﻧﻌﻤﺘﻲ ﻭﺭﺿﻴﺖ ﻟﻜﻢ ﺍﻹﺳﻼﻡ ﺩﻳﻨﺎ

Ghadeer Khum 1

BIKIN IDIN GHADIR KHUM KO IDIN GHADAR KHUM (1) DARUSSA DAKE CIKIN HAJJIN BAN KWANA DA HUDUBAR GHADIR KHUM (Farfajiyar GHADIR KHUM kenan maikaratu ke gani a cikin wannan hoto) HAJJIN BAN KWANA : Shine aikin hajji da Annabi (saw) da cuncurundon SahabbanSa (raa) daga ko ina suka halarta a shekara ta goma (10) bayan hijira. KHUM : Sunar wani mutum mairine ne da ake kiran wani kwari dake tsakanin Makkah da Madina da shi, wanan wuri yana da tazarar mil uku (3km) daga Juhfa (muhallin daukar miqatin mutanen sham). GHADIR : Ana nufi wurin dake da idanun ruwan da bishiyoyi suka kewaye mabubugan ruwan. Akan haka ake hade sunayen biyu a kira wurin da sunar GHADIR KHUM. A wannan wuri ne Annabi (saw) da SahabbanSa (raa) da wadanda hanyar garuruwansu take ta kan wannan hanya, suka yada zango bayan da suka gama aikin hajjin ban kwana suke komawa izuwa gida. Anan ne yayi shaharrariyar hudubar dake a dunkule take wanke ciki da wajen Imam Aliy bn Abiy Talib (ra) da bisa yawan maganganu da koke da suka samo asali daga mutanen da yake shugabanta daga Yeman, bayan da wasu abubuwa suka faru tsakaninsa da su akan : 1. Daukarsa (zaben) wata kyakkyawan kuyanga daga cikin ribatattu. 2. Hana su amfani da kayan ado da yayi, bayan na'ibinsa ya basu dama. 3. Abinda wasunsu suka kira da kaushin hali ko tsanani daga bangarensa gare su. Akan wadannan abubuwa ne maganganu suka yi ta kai komo a tsakanin mutanen Yeman a lokacin aikin hajjin ban kwana, har ta kai ga matsayin wasu daga cikin Sahabbai (raa) da suke karkashins suka kai kokensa wurin Annabi (saw). Kasantuwar hajjin ban kwana shine mafi girma da taron jama'ar musulmi daga dukkan garuruwan musulmi da Annabi (saw) ya taba shaidawa, wadanda basu taba ganinSa ba (saw) suka ganshi, anan ne yayi hudubarSa mafi tara mutane, inda a cikinta yayi wasici da kyautata wa mata da wadanda hannuwan dama suka mallaka, kuma ya kafawa mutane hujja akan shaidar ya isar ma 'ya'yan Adamu sakon Allah Ta'alah, kuma a wannan mauqifi na Arfah ne Ayahr cikon addini : "اليم أكملت لكم دينكم وأتممت عليكم نعمتي ورضيت لكم الإسلام دينا" ta sauka gare Shi (saw). Kasantuwar wannan kadiyyar (koke da nuna kiyayya ga Imam Aliy) bata shafi dukkan Sahabbai ba, sai Annabi (saw) baiyi huduba akanta ba a cikin kwanakin aikin hajji, ta inda sakonta (abinda mabarnata ke riya cewa NADIN KHALIFANCI ne) zai isar da ita wa gaba-dayan dukkan Sahabbai, kamar yadda yayi wancan hudubar a filin Arfah, inda a wurin ya ambaci maganar kyautata wa mata da sauransu da maimaita tambaya wa Sahabbai : shin Na isar da sakon Allah? Sahabbai (raa) suka amsa da cewa : Tabbas Ka isar. Duk wannan ya faru ne akan idanu da shaidar dukkan Sahabbai da suke halarce a wurin, amma fangane da koken mutanen Yeman sai Ya jinkirta bada jawabi akai, sai a hanyar komawarsu gida bayan da ya yada zango a wannan kwari na GHADIR KHUM, inda anan ne a ranar 18th/12/10 AH yayi hudubar da sababinta shine wancan koke, kuma domin Ya bada amsa wa masu koke akan Aliy bn Abiy Talib (ra), inda a cikin hudubar yace : " من كنت مولاه فهذا علي مولاه اﻟﻠﻬﻢ ﻭﺍﻝ ﻣﻦ ﻭﺍﻻﻩ، ﻭﻋﺎﺩ ﻣﻦ ﻋﺎﺩﺍﻩ، ﻭﺍﻧﺼﺮ ﻣﻦ ﻧﺼﺮﻩ، ﻭﺍﺧﺬﻝ ﻣﻦ ﺧﺬﻟﻪ " "Duk wanda Na kasance majibincinsa, toh wannan Aliyu majibincinsa ne, Ya Allah, Ka jibinci duk wanda ya jibince shi, Kayi adawa da duk wanda yayi adawa da shi, Ka taimaki duk wanda ya taimake shi, kuma tabar da duk wanda ya tabar da shi." (bangaren wannan hadisi da tsawonsa haka yana tangardan rashin inganci, amma zamu kaddara ma gaba-dayansa ya inganta). Wannan huduba ita ce wasu Maluman musulunci suke kiranta da sunar HADISIN GHADIR KHUM, wassu kuma ke kiranta HADISIN WILAYA, a yayin da bakin haure wa Musulunci ke kiranta HADISIN DASA KHALIFA. Ga Musulmai ma'anar wannan hadisi shine qara fitar da falalar Aliy (ra), wurin nuna tsarkin ciki (zuciyarsa) da wajensa (zahirinsa) da jibintarsa ta hanyar kaunarsa da yi masa biyayya da barrantar da shi daga hikidu ko son zuciya ko kin muminai, amma sam basu fahimci ma'anarta shine NADA SARAUTAR KHALIFA bayan Annabi (saw) ba. Wannan itace tabbatacciyar fassara a janibin masu bin Musulunci sau da kafa da tsarkakakken zuciya, ba tare da NIFAQA ba. Amma akasi itace fassarar wannan huduba a janibin masu ciwon zandaqah a cikin zuci, kuma masu adawa da karantarwan Annabi (saw), wanda idan muka kaddara daukan fassararsu ga hadisin tana nufin wasici ne ga NADA SHI SHUGABA A BAYAN ANNABI (SAW) kamar haka : ١. من كنت مولاه فهذا علي مولاه "Duk wanda na kasance SHUGABANSA, toh Aliyu wannan SHUGABANSA ne" MAS'ALOLIN DA SUKE CIKIN IRIN WANNAN FASSARA : 1. Babu abinda ke nuni da hana wani ma ya zamanto shugaba a bayansa. Sannan matsayin Imam Aliy (ra) a wurin Musulmai shine yana daga cikin Shuwagabanninsu. 2. Kenan wannan fassara tana nufin Sahabbai kamar Ansar (raa) bassu fahimtar harshen larabci, domin sune yayin sallama khalifanci wa Abubakar (raa) suka ce : منا أمير ومنكم أمير "Cikinmu akwai shugaba, kuma cikinku akwai shugaba" 3. Ina laifin Sahabbai (raa) akan abinda Imam Aliy (ra) yayi shiru akai ranar da aka mika bai'a ga Abubakar (raa) bai tashi ya tunashe su wannan nadi nasa ba? 4. Wannan magana jingina wa Imam Aliy (ra) rashin sanin wannan kalma مولاه tana nada shi khalifa ne, domin kamar yadda tazo a cikin littafin (Nahjul Balagha, 1/191) ranar da mutane suka yi cuncurundo yi masa mubaya'a, sai yake ce musu : " ﺩﻋﻮﻧﻲ ﻭﺍﻟﺘﻤﺴﻮﺍ ﻏﻴﺮﻱ " "ku fita sha'ani na ku nemi wani na" Kaga da yasan wancan kalmar nada shi khalifa Annabi (saw) yayi, da sam ba zaice musu su nemi waninsa ba. 5. Ina hikimar dake cikin murtaddai (kamar yadda suka ce sahabbai sunyi ridda akan wannan kadiyyar) zasu zo gaban Imam Aliy (ra) yi masa bai'a, amma sai bai nemi su jadda kalmar shahada ba don su dawo Musulunci kafin ya karbi bai'arsu, ko karbar bai'ar kafiri ya halasta ne? 6. Ko akwai ingataccen ruwayar da ke nuna Fatima Albatula (raa) ta na sane da wannan nadin, har ta shahara da neman a zartas da shi kan Mijinta, sabanin Fadak? ٢. اﻟﻠﻬﻢ ﻭﺍﻝ ﻣﻦ ﻭﺍﻻﻩ "Ya Allah, Ka jibinci duk wanda ya jibince shi" MAS'ALA : 1. Wannan addu'a ce da Annabi (saw) yayi ga wadanda suka shugabantar da Imam Aliy (ra) a bayansa. Abinda masu irin wannan fassara suke nufi, shine wannan addu'ar da Annabi (saw) yayi bata yi aiki akan Aliy (ra) ba sai akan Abubakar Siddiq (raa). Tunda suna nufin akasin fassarar musulmai shine daidai, sai a tambaye su : ya aka yi Allah ya jibinci wadanda suka jibinci Abubakar ta hanyar shugabantar musu da wanda suka shugabantar? ٣. ﻭﻋﺎﺩ ﻣﻦ ﻋﺎﺩﺍﻩ "Ya Allah Ka yi adawa da duk wanda ke adawa da shi" MAS'ALOLI : 1. Tabbatattun tarihin musulunci sun tabbatar ba asan wani sahabi guda daya ba da ya shafe rayuwarsa bayan wafatin Ma'aiki (saw) yana adawa da Abubakar (ra) ba. 2. Tarihi ya tabbatar Abubakar da Umar da Usman (raa) basu yi adawa da Aliy (ra) ba, kenan wannan yana daga cikin hikimar kasantuwar suka yi khalifanci gabaninsa. ٤. ﻭﺍﻧﺼﺮ ﻣﻦ ﻧﺼﺮﻩ "Ya Allah, Ka taimaki duk wanda ya taimake shi" MAS'ALOLI : 1. Da irin fassarar masu fassarar wannan hadisi da nada khalifa, sai muce kenan kuna nufin wannan addu'ar ma akan Abubakar (raa) tayi aiki, domin a bayyane shine Allah ya bada nasara ga wadanda suka sallama masa khalifanci, banda akasin hakan? 2. Allah ya karfafi Abubakar da Umar da Usman (raa) saboda sun karfafi Aliy a duk inda ya kamata su karfafe shi, kamar wurin : sadar masa zumuncin kasantuwarsa jinin Manzon Allah (saw), ba shi kaso a cikin abinda aka rabauta, sanya shi a cikin majalisar koli na shawari da sauransu. ٥. ﻭﺍﺧﺬﻝ ﻣﻦ ﺧﺬﻟﻪ "Ya Allah, Ka tabar da duk wanda ya tabar da shi" MAS'ALA : 1. Allah bai tabar da Abubakar ko Umar ko Usman (raa) ba, domin babban abinda zai fitar mana da hakan fili, shine kasantuwar a tsakanin sahabbai sune Musulmai suka fi sanya sunayensu wa 'ya'yayensu, kuma sune Musulmi ke kidanya su a matsayin khalifofin farko, wanda da Allah ya tabar da su da tunin an manta da tarihinsu ko an daina ambatonsu da alheri. BABBAN ABIN TAMBAYA : IDAN WANCAN HADISI NADA KHALIFA KE TABBATARWA, SHIN DUK WADANCAN ADDU'OIN DA ANNABI (SAW) YAYI WA IMAM ALIY (RA) KUNA NUFIN KUCE ALLAH BAI KARBESU BA KENAN? Daga 'Dan Almajiri : Salihu Baban Takko 17th/12/1434 AH - 22th/10/

Kirsimetin Shi'ah Daga Malam Baban Hamdan

KIRSIMETIN ADDININ SHI'A. 'YANUWANTAKAR ADDININ SHI'A DA NA KIRISTA QALQASHIN IBADA GUDA BA SABON LABARI BANE KAMAR YADDA KOWA YA JI KUMA YA GA LOKUTAN DA MADUGUN MABIYA ADDININ SHI'A IBRAHIM ZAKZAKIY DA SHUGABANNIN KIRISTOCI A NIGERIA SUKA SHA JAGORANTAR TARUKAN 'MU-TARU-MU-YI-BAUTA'. MAI HANKALI ZAI FAHIMCI MABIYA ADDININ SHI'A SUNA DA RUWA DA TSAKI A KIRSIMETIN ADDININ KIRISTA, MUSAMMAN IDAN AKA YI KARATUN-TA-NUTSU GA AMSAR DA AYATULLAHI SISTANIY YA BAYAR DA AKA TAMBAYE SHI HAKUMCIN TARAYYA DA ARNA A BUKUKUWAN SU? إذا كان فيه ترويج للمسيحية أو للفساد فلا يجوز "IN DAI BASA TALLATA ADDININ KIRISTANCI KO BARNA TO YA HALATTA" MU KALLI WANNAN DA KYAU, CEWA AKA YI "BIKIN ADDININ KIRISTA", AMMA SAI DA YAYI JIRWAYE YA HALATTA SHI, GAMA BATUN ACE IN BA A TALLATA ADDININ KIRISTA A CIKIN SA ZANCEN BANZA NE DON GABA DAYAN SA MA AI TALLATA ADDININ NE. KUMA MA AI MUN GANI, DUK DA KUROS-KUROS A WUYAYEN SU KUMA SUN RIQO WASU A HANNAYEN SU, SUKA RIQA ZUWA BUKUKUWAN ADDININ SHI'A, SAI DA NASU YAZO ZA AYI TUNANIN ZASU CIRE KUROS-KUROS DIN?! AYATULLAHI YAYI HAKA NE DON KAR YA TAFI KAI TSAYE MUTANE SU FAHIMCI ALAQAR DAKE AKWAI TSAKANIN ADDINAN BIYU. AMMA QARYA FURE TAKE BATA 'YA-'YA, GAMA DUK WANDA YA KALLI ADDINAN BIYU YA SAN KUMAINIY NE DA KAMNA'IY; ABIN DA YAYI WANNAN SHINE YAYI WANCAN. ASHE BA SU IBRAHIM ZAKZAKIY BANE SUKA BULLO DA MAULIDIN ANNABI ISA A NAN QASAR BA?! ASHE BA KIRISTOCI NE KE RAYA BIKIN KIRSIMETI SABO DA WAI A CEWAR SU, YESU YA SADAUKAR DA RAYUWAR SA DON YA CECE SU BA?! MA'ANA DUK ZUNUBAN DA MABIYA ZASU TAFKA, YESU YA WANKE SU, ALLAH BA ZAI MUSU AZABA BA! TO AI NAN MA HAKA MABIYA ADDININ SHI'A SUKA FADA, KAMAR YADDA KULAINIY YA RUWAITO DAGA QUMMIY CIKIN KAFIY 1/260 WAI MUSAL KAZIM A.S. YA CE: إن الله عز وجل غضب على الشيعة فخيرني نفسي أوهم، فوقيتهم والله بنفسي "ALLAH YAYI FUSHI DA 'YAN SHI'A (KUN SAN SU SUKA KASHE HUSAIN JIKAN ANNABI S.A.W.) SAI YA BANI ZABI 'KO DAI NI KO SU ('YAN SHI'A)' WALLAHI SAI NA FANSHE SU DA KAINA" WANNAN ITA CE DORON AQIDAR MABIYA ADDININ KIRISTA, KUMA ITA CE DORON AQIDAR ADDININ SHI'A. 'YAN SHI'A A KAN WANNAN NE SUKE DA AQIDAR DUK ZUNUBIN DA BARAFILE ZAIYI TAFKA ALLAH BA ZAI QONA SHI BA, SABO DA ALLAH YANA SON SU, KAMAR YADDA SUMA KIRISTOCIN SUKE FADA. BUGA KA QARA, KAMAR YADDA KIRISTOCI SUKA RIQI ANNABI ISA A.S. A MATSAYIN UBANGIJI, HAKA MABIYA ADDININ SHI'A SUN RIQI ALIY R.A. A MATSAYIN ABIN BAUTA. MISALIN WANNAN YANA NAN A TAFSIRIN AYYASHIY 2/353 QALQASHIN FADIN ALLAH S.W.T. ولا يشرك بعبادة ربه أحدا DON YA TABBATAR MUKU LALLAI ALLAH AKE NUFI KUMA ALIY SHINE ALLAN, SAI DA AYYASHIY YA KORO RUWAYA DAGA ABU ABDILLAHI: قال الله تبارك وتعالى أنا خير شريك، من أشرك بي في عمله لن اقبله "ALLAH T.W.T. YA CE : NAFI QARFIN A HADA NI DA WANI; WANDA YA HADA NI DA WANI A WANI AIKI BA ZAN TABA KARBAR SA BA..." AYYASHIY YA CE ABU ABDILLAHI YA CE MA'ANAR ITA CE: التسليم لعلى لا يشرك معه في الخلافة "MIQA WUYA GA ALIY (BA GA ALLAH BA) KADA AYI TARAYYA DA SHI A KHILAFA..." SHI YASA ZAMU GANI YAZO A BIHAR 39/193 ALIY NE ZA A GIRKAWA KURSIYY YAYI HISABI BA ALLAH S.W.T. BA. ثم يوضع لك كرسي يعرف بكرسي الكرامة فتقعد عليه "SAI A GIRKA MA KURSIYY WANDA AKE CEWA KURSIYYUL KARAMA, SAI KA ZAUNA A KAI" ثم يجمع لك الأولون والآخرون في صعيد واحد "SAI A TARA MA (HALITTU) NA FARKO DA NA QARSHE A FARFAJIYA GUDA) فتأمر بشيعتك إلى الجنة و بأعدائك إلى النار، فأنت قسيم الجنة وأنت قسيم النار "SAI KA SAKA 'YAN SHI'A ALJANNA KA SAKA MAQIYAN KA (MA'ANA WANDA BA DAN SHI'A BA) WUTA; YO AI KAI NE MAI RABA WUTA DA ALJANNA" GA DAI YADDA MAGANAR TAKE A BAKIN WANI 'AYATULLAHIN' NA SHI'A, YA CE: علي ربنا يوم القيامة ... علي رب من الأرباب "ALIYU SHINE ALLAN MU RANAR ALQIYAMA, ALIY ALLAH NE DAGA ALLOLI..." MAGANAR TANA NAN A YOUTUBE. TO ADDININ SHI'A DA NA KIRISTA SHAQIQAN JUNA NE, A DUNIYA DA LAHIRA, TUNDA A NAN FB MA MUNGA KIRISTA YA MUTU A SYRIA 'YAN SHI'A SUKA YI TA YADA HOTON SA SUNA CEWA YAYI SHAHADA. ALLAH YA SHIRYAR DA MU GASKIYA, ALLAH YA TSARE MANA MUSULUNCIN MU YA RABA MU DA FITINAR ADDININ SHI'A. ALHAMDU LILLAHI WASSALATU WASSALAMU ALA RASULILLAH
Ammar AbuTurab
A GAME DA JAGORORIN 'YAN SHI'A A KASAR IRAN, BABBAN MALAMI, TSOHON LIMAMIN ARAFA, SHUGABAN MALAMAI DA MASU FATAWA NA KASA MAI TSARKI, SHAIKH ABDUL'AZEEZ ALU~SHAIKH YA CE:
"WADANNAN BA MUSULMAI BA NE...,
'YA'YAN MAJUSAWA NE...,
MAKIYA MUSULMAI NE A JIYA DA YAU, MUSAMMAN AHLUS SUNNATI WAL JAMA'A...".
«يجب أن نفهم أن هؤلاء ليسوا مسلمين، فهم أبناء المجوس، وعداؤهم مع المسلمين أمر قديم وتحديدا مع أهل السنة والجماعة»
http://makkahnewspaper.com/…/%D8%A7%D9%84%D9%85%D9%81%D8%AA…
YA FADI HAKA KENAN DA 'YAN KWANAKI, KATSAM SAI GA BABBAN BOKAN 'YAN SHI'AR KASAR IRAN, ALI KHAMENE'I YA FITO YA HALASTA WA 'YAN SHI'A GABATAR DA IBADA A KABARIN IMAMINSU HUSSAIN DA YAKE CAN KARBALA A KASAR IRAQI, A MAIMAKON HAJJI ZUWA GA DAKIN ALLAH DA YAKE BIRNIN MAKKA A KASAR SAUDIYYA, A CIKIN RANAR ARAFA DA KWANAKIN HAJJI.
KOWA YA SANI, A MUSLUNCI ALLAH BAI SHAR'ANTA TAFIYA ZIYARA TA IBADA A WANI LOKACI NA MUSAMMAN BA SAI ZUWA MASALLATAI UKU KAWAI; NA HARAMIN MAKKA, DA MASALLACIN ANNABI (S.A.W) A MADINA, SAI KUMA NA AL- AQSA A BIRNIN QUDUS.
HAKA ALLAH BAI SHAR'ANTA AIWATAR DA IBADA IRIN TA AIKIN HAJJI; DAWAFI, SA'AYI, TSAYUWAR ARAFA A KO'INA BA SAI A MAKKA. KOKKOYON HAKA, KO KISHIYANTAR HAKAN, TA HANYAR GABATAR DA SHI A WATA KASA, A WANI BIRNI, A WANI MASALLACI KO WANI KABARI KO HUBBARE, MUSAMMAN A LOKACIN AIKIN HAJJI, CIN KARO NE DA FITO NA FITO DA YAKE WARWARE SHARI'AR MUSLUNCI. SABODA ABU NE SANANNE A WAJEN AL'UMMAR MUSULMI, AIKIN HAJJI RUKUNI NE NA MUSLUNCI, KOKARIN KISHIYANTARSA RUSA MUSLUNCIN NE.
SABODA HAKA, WADANNAN MUTANE BOKAYEN 'YAN SHI'A, JAGORORIN IRAN, BA MUSULMAI BA NE KAMAR YADDA MUFTY ALU~SHAIKH TSOHON LIMAMIN ARAFA YA FADA

Thursday 15 September 2016

Engr Basheer Adamu Aliyu
FOREWARNED IS FOREARMED!
Kidnap experience on Abuja Kaduna highway:
Forwarded as received. Experience of a Snr
Military Officer on Sep 1 along Abuja-kaduna
express way.
I wish to share a terrible experience I had on
Thursday 1 September 2016, along Kaduna-Abuja
highway at about 9pm. I had good intelligence on
the security situation and considered that it was
still ok to move based on that knowledge. I and a
family friend were travelling to Abuja and we had
left by 6pm. Our car had some problems and we
finished fixing it by 8pm. We then proceeded on
the trip. We had just passed Redeemed Camp, by
Alheri, where we saw 2 white coloured J5 buses.
The last mileage I saw was 138 KM to Zuba & I
saw the 2 buses along the road parked left and
right on the shoulders. I told my friend that this
looked like a kidnap spot, that it had all the
features like a bend and a slope with the buses.
My friend then screamed that they were throwing
knockouts at us immediately I finished saying
that. I quickly realized that it was gunfire from
AK-47. Three men stood in front of the road
firing at us. I slammed the brakes, the car
veered right and I decided to continue right, off
the road. I was able to stop the car before a
ditch I saw. I tried to reverse but it didn't
engage, the car engine went off and some
attempts to restart it failed. Then one of them
ran to me, I came out of the car with my hands
up, so also my friend. Then, I turned back and
started pacing. The guy that came for me looked
like a foreigner, from Niger. Then we bolted.
They started firing at us. Then someone came
from our initial behind and started shooting at
us. We managed to cross the road with nothing
in sight; No cars etc. We couldn't even see the
road divider. Then we both crossed the road.
They chased us and kept shooting. That was
how we escaped and pinned down in the bush.
Immediately we were on the other side of the
road we entered the bushes and kept running.
During this time, for over 2hrs they came with
their car patrolling in search for us. Later the
police came, there seemed to been some
collaboration amongst them. I lost my Fone and
other valuables, but my luggage in the booth was
intact as the booth didn't open since it was a
406. It happened like a movie but its real. They
weren't herdsmen,They were the kidnappers
along that axis. They exist in some areas up
north.
Don't travel when it's dark.
Always watch out well in bends, slopes and hills.
Be careful about any checkpoints, not all
checkpoints are real.
The police helped to stop all cars when the
operation started with us to enhance smooth
operation by the kidnappers.
The kidnappers were operating under the cover
of two police checkpoints in about a kilometre
apart.
The police tried to take us back to the scene
which I refused clearly and instead called on the
army.
That was what forced the police to take us to
the nearest army post.
Don't travel when it's dark as it increases the
risk, but note also that same technique would
work even in day time.
Lessons learnt:
If uve to run for ur life take the first chance and
don't be afraid of the gun when ur running.
Usually, guns are effective at close range.
Most people including uniformed men are poor
shooters especially when it has to do with
moving targets; this fact is unknown to many
including the uniformed men.
I've seen fire but not this sort of unexpected fire.
If ur car breaks down on the road and ur
stranded, do not remain inside it or near it. My
advise is for u to cross the road and look for a
nearby village. An abandoned car would always
attract anyone including criminals. If uve to flee
into the bush in a pursuit, run in a diagonal axis
to the road.
In a near death experience u don't bother about
the things u did, u worry more about the things u
didn't do.
The kidnappers were actively collaborating with
the police.

Hk Yaradua

Assalamu Alaikum
Ina ma ku maraba

صلة الرحيم

ﻟﻘﺪ ﺃﻣﺮﻧﺎ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﺰﻭﺟﻞ ﺑﺼﻠﺔ
ﺍﻷﺭﺣﺎﻡ ﻭﺍﻟﺘﻮﺍﺻﻞ ﻣﻌﻬﻢ ﻭﺑﺮﻫﻢ
ﻭﺍﻹﺣﺴﺎﻥ ﺇﻟﻴﻬﻢ، ﻭﺣﺬﺭﻧﺎ ﻣﻦ
ﺍﻟﻘﻄﻴﻌﺔ ﻭﺧﻄﻮﺭﺗﻬﺎ ﺣﻴﺚ ﻻ
ﻳﺪﺧﻞ ﺍﻟﺠﻨﺔ ﻗﺎﻃﻊ ﺭﺣﻢ، ﻭﺻﻠﺔ ﺍﻷﺭﺣﺎﻡ ﺗﻜﻮﻥ ﻣﻦ
ﺧﻼﻝ ﺯﻳﺎﺭﺗﻬﻢ ﻭﺍﻻﻃﻤﺌﻨﺎﻥ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﻭﺍﻟﺴﺆﺍﻝ ﻋﻨﻬﻢ ﻋﻨﺪ
ﻣﺮﺿﻬﻢ ﻭﺍﻟﺪﻋﺎﺀ ﻟﻬﻢ ﻋﻨﺪ ﻣﺼﺎﺋﺒﻬﻢ ﻭﻣﺴﺎﻋﺪﺗﻬﻢ ﻓﻲ
ﻛﺮﺑﺎﺗﻬﻢ ﻭﻋﺜﺮﺍﺗﻬﻢ، ﻭﻣﺸﺎﺭﻛﺘﻬﻢ ﺃﻓﺮﺍﺣﻬﻢ ﻭﺃﺣﺰﺍﻧﻬﻢ
ﻭﺍﺳﺘﻀﺎﻓﺘﻬﻢ ﻭﺇﻛﺮﺍﻣﻬﻢ .
ﻣﺎ ﺍﻟﻤﻘﺼﻮﺩ ﺑﺎﻷﺭﺣﺎﻡ؟
ﺍﻷﺭﺣﺎﻡ ﻫﻢ ﻛﻞ ﻣﻦ ﺗﺮﺑﻄﻨﺎ ﺑﻬﻢ ﺻﻠﺔ ﻧﺴﺒﻴﺔ ﻣﻦ ﺟﻬﺔ
ﺍﻷﻡ ﺃﻭ ﺍﻷﺏ، ﻭﻳﺪﺧﻞ ﻓﻲ ﺫﻟﻚ ﻣﻦ ﺗﺮﺑﻄﻨﺎ ﺑﻪ ﺻﻠﺔ
ﺳﺒﺒﻴﺔ ﻣﻦ ﺍﻟﻨﻜﺎﺡ ﺃﻳﻀﺎً ﻭﻫﻢ ﺍﻷﺻﻬﺎﺭ .
ﺇﺫﺍ ﺃﺭﺩﺕ ﺍﻟﺨﻴﺮ ﻭﺍﻟﺴﻌﺎﺩﺓ ﻓﻌﻠﻴﻚِ ﺑﺼﻠﺔ ﺍﻷﺭﺣﺎﻡ، ﺇﺫﺍ
ﺃﺭﺩﺕ ﻃﻮﻝ ﺍﻟﻌﻤﺮ ﻓﻌﻠﻴﻚِ ﺑﺼﻠﺔ ﺍﻷﺭﺣﺎﻡ، ﺇﺫﺍ ﺃﺭﺩﺕ
ﺍﻟﺮﺯﻕ ﺍﻟﻜﺜﻴﺮ ﻭﺍﻟﻮﻓﻴﺮ ﻓﻌﻠﻴﻚِ ﺑﺼﻠﺔ ﺍﻷﺭﺣﺎﻡ، ﻓﺴﺒﺤﺎﻥ
ﺍﻟﺨﺎﻟﻖ ﺍﻟﺬﻱ ﺟﻌﻞ ﻟﻨﺎ ﻣﻦ ﻋﺒﺎﺩﺓ ﻳﺴﻴﺮﺓ ﻓﻀﻞ ﻭﺛﻮﺍﺏ
ﻭﺟﺰﺍﺀ ﻋﻈﻴﻢ .
ﻣﺎ ﻫﻮ ﻓﻀﻞ ﺻﻠﺔ ﺍﻟﺮﺣﻢ؟
• ﺻﻠﺔ ﺍﻷﺭﺣﺎﻡ ﻫﻲ ﻃﺎﻋﺔ ﻟﻠﻪ ﻋﺰﻭﺟﻞ : ﻟﻘﺪ ﺃﻣﺮﻧﺎ ﺟﻼ
ﻭﻋﻼ ﺑﺼﻠﺔ ﺍﻷﺭﺣﺎﻡ } ﻭَﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻳَﺼِﻠُﻮﻥَ ﻣَﺎ ﺃَﻣَﺮَ ﺍﻟﻠّﻪُ ﺑِﻪِ
ﺃَﻥ ﻳُﻮﺻَﻞَ ﻭَﻳَﺨْﺸَﻮْﻥَ ﺭَﺑَّﻬُﻢْ ﻭَﻳَﺨَﺎﻓُﻮﻥَ ﺳُﻮﺀَ ﺍﻟﺤِﺴَﺎﺏِ {
ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﺮﻋﺪ .21
•ﺻﻠﺔ ﺍﻷﺭﺣﺎﻡ ﺗﺠﻠﺐ ﺍﻟﺮﺯﻕ ﺍﻟﻮﻓﻴﺮ : ﻗﺎﻝ - ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ :- ‏(ﻣﻦ ﺃﺣﺐ ﺃﻥ ﻳﺒﺴﻂ ﻟﻪ ﻓﻲ ﺭﺯﻗﻪ
ﻭﻳﻨﺴﺄ ﻟﻪ ﻓﻲ ﺃﺛﺮﻩ ﻓﻠﻴﺼﻞ ﺭﺣﻤﻪ ‏) ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ِ،
ﻭﻋﻨﺪ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ﺃﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ - ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
-ﻗﺎﻝ : ‏( ﺗﻌﻠﻤﻮﺍ ﻣﻦ ﺃﻧﺴﺎﺑﻜﻢ ﻣﺎ ﺗﺼﻠﻮﻥ ﺑﻪ ﺃﺭﺣﺎﻣﻜﻢ،
ﻓﺈﻥ ﺻﻠﺔ ﺍﻟﺮﺣﻢ ﻣﺤﺒﺔ ﻓﻲ ﺍﻷﻫﻞ، ﻣﺜﺮﺍﺓ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺎﻝ،
ﻣﻨﺴﺄﺓ ﻓﻲ ﺍﻷﺛﺮ ‏) .
• ﺻﻠﺔ ﺍﻷﺭﺣﺎﻡ ﺳﺒﺐ ﻟﺪﺧﻮﻝ ﺍﻟﺠﻨﺔ : ﻳﻘﻮﻝ ﺣﺒﻴﺒﻨﺎ
ﺍﻟﻤﺼﻄﻔﻰ- ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ - ‏(ﻳﺎ ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﻨﺎﺱ
ﺃﻓﺸﻮﺍ ﺍﻟﺴﻼﻡ، ﻭﺃﻃﻌﻤﻮﺍ ﺍﻟﻄﻌﺎﻡ، ﻭﺻﻠﻮﺍ ﺍﻷﺭﺣﺎﻡ،
ﻭﺻﻠﻮﺍ ﺑﺎﻟﻠﻴﻞ ﻭﺍﻟﻨﺎﺱ ﻧﻴﺎﻡ، ﺗﺪﺧﻠﻮﺍ ﺍﻟﺠﻨﺔ ﺑﺴﻼﻡ ‏)
ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺣﻤﺪ ﻭ ﺍﺑﻦ ﻣﺎﺟﺔ .
• ﺻﻠﺔ ﺍﻷﺭﺣﺎﻡ ﺗﻨﺸﺮ ﺍﻟﺤﺐ ﻭﺍﻷﺧﻮﺓ : ﻻﺷﻚ ﺃﻥ
ﺍﻟﺘﻮﺍﺻﻞ ﻭﺻﻠﺔ ﺍﻟﺮﺣﻢ ﺳﺒﺐ ﻭﻋﺎﻣﻞ ﺃﺳﺎﺳﻲ ﻟﻨﺸﺮ
ﺍﻟﺤﺐ ﻭﺍﻟﻤﻮﺩﺓ ﺑﻴﻦ ﻛﻞ ﺃﻓﺮﺍﺩ ﺍﻟﻌﺎﺋﻠﺔ .
ﺑﺠﺎﻧﺐ ﻣﺎ ﺳﺒﻖ ﻓﺈﻥ ﺣﻴﺎﺗﻨﺎ ﻣﻠﻴﺌﺔ ﺑﻜﺜﻴﺮ ﻣﻦ ﺍﻟﺼﻌﺎﺏ
ﻭﺍﻟﻤﺸﺎﻛﻞ ﻭﻻﺑﺪ ﺃﻥ ﻳﻜﻮﻥ ﻟﻨﺎ ﺃﻧﺲ ﻭﻋﺎﺋﻠﺔ ﻧﺴﻌﺪ ﺑﻬﺎ
ﻧﺸﻌﺮ ﻣﻌﻬﺎ ﺑﺎﻟﺮﺍﺣﺔ ﻭﺍﻻﺭﺗﻴﺎﺡ، ﻓﻀﻼً ﻋﻦ ﺃﻥ ﺻﻠﺔ
ﺍﻷﺭﺣﺎﻡ ﺗﻐﻔﺮ ﺍﻟﺬﻧﻮﺏ ﻭﺗﻘﺮﺑﻨﺎ ﻣﻦ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﺰﻭﺟﻞ ﻟﺬﺍ
ﻓﺎﺣﺮﺻﻮﺍ ﻋﻠﻰ ﺻﻠﺔ ﺍﻟﺮﺣﻢ ﺩﺍﺋﻤﺎً