Wednesday 28 September 2016

TABARGAZAR YAKUBU YAHYA KTN BAYAN DAWOWARSA DAGA IRAN

                             KUSKUREN MALAM

KASET NE WANDA SHUGABAN YAN SHI'AR KATSINA MAL YAKUBU YAHYA YAYI BAYAN DAWOWARSA DAGA IRAN INDA YA BAYYANA HAKIKANIN ABUBUWAN DA YA GANO WANDA DA HAR YA TUBA AMMAN TALLALABIYA TA JA SHI YA KOMA 

RUBUTAWA: Hasan Kabir Yar'adua


ASHA KARATU LAFIYA

''Kuma abin da na gani wanda ya dame ni sosai, shine kasantuwar mutanen tamanin bisa dari (80%) masu askoken Gemuna ne ga gashin baki ban san wannan rashin fahimtar musulunci ne ko rashin fahimtar sunna ne Allahu a’alam. Sannan kuma karku sha mamaki ka ga malami ya sha abaya da rawani amma ga taba. Wannan abu ya daure mini kai sosai da sosai kuma na shiga tunani me wannan ke nufi? Ko da yake na tambayi wasu daga cikin malamansu amma dai hujojin da aka ba ni basu gamsar da niba  
Kuma abin da na gani wanda ya dame ni sosai, shine kasantuwar mutanen tamanin bisa dari (80%) masu askoken Gemuna ne ga gashin baki ban san wannan rashin fahimtar musulunci ne ko rashin fahimtar sunna ne Allahu a’alam. Sannan kuma karku sha mamaki ka ga malami ya sha abaya da rawani amma ga taba. Wannan abu ya daure mini kai sosai da sosai kuma na shiga tunani me wannan ke nufi? Ko da yake na tambayi wasu daga cikin malamansu amma dai hujojin da aka ba ni basu gamsar da niba”  
“Kuma dangane da al’amarin sallah misali, har na baro ni dai sau biyu nake jin kiran sallah a rana in aka kira sallah azzahar nan take za ayi sallah azzahar sannan bayan minti biyar a maida la’asar, kuma baza’a kara kiran sallah ba sai rana ta fadi. In rana ta fadi nan take za’ayi sallar magrib sannan a maida Isha’I shi kenan kuma sai gobe da azahar ban dai ji na asuba ba har dai na baro.
Wannan shine kuma abubuwan da na gani su suka sani wani tunani da ban, da kuma jin lallai ya kamata mu fahimci hakikanin mike faruwa, banji na assubahi ba, sannan kuma na san sau biyu ne akeyi ayi da Azuhur ayi da magrib.”
“Sannan kuma kamar yadda yake acikin mazahabarsu da akidojinsu, babu shakka akwai babbancin mai yawan gaske tsakanin mazhabobin su a AKIDA da mu’amala da sauransu da na SUNNAH. Akwai babban bambanci kwarai da gaske.”
 bisa wani kodago ko kasa kanshi ake aza goshi da hanci hakanan kuma wajan tsarin sallah kai kanka zaka san babu shakka akwai bambanci in baka yi hattara ba za a barka baya don zaka ga irin jalsatul-istiraha da ake fada su alkunuti a cikin sallah da daga hannu ana addu’a da sauran abubuwa wanda a irin mazhabobi na sunnah bazaka sami wannan ba to babu shakka su suna riko da irin wadanan abubuwa. Kuma suna jin cewa kowane daya daga cikin limamansu ma’asumi ne wanda wannan ya sabawa akida na Ahlilsunnah domin babu wani ma’asumi sai Annabi da sauran annabawa (A.S) a mazhabar sunna wannan haka yake, amma su a wurinsu dole ne duk abin da Annabi yake da shi na Isma babu shakka Imamu ya sami wannan Isma din kaga wannan ya kore yi yuwan cewa mutum yana sunna kuma yana Shi’a ba zai yiwuba, sai dai in yana sunni ya koma shi’a ko kuma in shi’a ne to yabar shi’a baki daya ya koma sunnah, amma ya zama yana sunni yana shi’a wannan ba zai yiwu ba har abada.” Amma da yake Allah mai ikone akan komai bamu san nan gaba ba. saida abinda suke kokari su gina mutane akai shine a sami tafahumi da fahimtar juna, wannan abune mai kyau. Tafami shine Ahluussuna su yarda cewa shi’a musulmi ne suma shi’a su yarda Ahlussuna Musulmi ne domin alkur’ani daya ake karantawa daga dukkan bangarorin biyu, wannan mutum zai iya yarda da wannan. Wanda yake iyakar fahimta ta da abin da na gani da abin da naji da wanda na karanta a cikin littatafansu shine kamar yadda na fahimta dukkan mutanen sunnah, duk wanda yake ahlussuna ne yabar abin da yake na sunnah domin yayi shi’a saboda su ahlussunah kamar mutane ne da suke zaune akan bata da halaka ita kuma shi’a ita ce kawai tsira in mutum ba ita ba yake to ba zai tsira ba ni fahimta  dasu kenan suna ganin mutum in ba yana shi’a ba to shi tabbas halakakke ne kuma ba zai samu tsira ba saboda haka kokarinsu na yada sakonninsu da kudadansu da duk abinda suke iya wa ni na fahimci cewar kamar suna son kamar su fahimtar da musulmi cewa akan abinda suke ba dai dai bane su ko mo suyi abinda yake dai dai wanda shine SHI’A, to inko haka ne wannan al’amari to babu shakka shekarun da a kayi can baya wurin shekara dubu (1000) ana riginginmu tsakanin malaman Shi’a da Sunnah, inko haka za’a dawo da wannan mas’alar cikin al’umma tsakanin Shi’a da Sunna za’a ci wata shekara 1000 ba ayi komi ba don ba zai warware wannan rigimar ba, don ba za’a yi wu kai kana ganin babu wani ma’asumi sai Manzo wani kuma ya ce maka ga wani ma’asumi zai yi yu? Kaga ba zai taba yi wu ba. Ko kuma misali inka kabbara sallah ka dora hannuwanka akan kirji (Kabdhu) wanda yake ja’iz ne kana iyayi kuma kana iya sakin hannayen, shi kuma ba zai iya binka sallah ba saboda in ya bika sallar sa ta baci, ai kaga wato akwai mas’ala babba kenan, to kaga kenan mutum ya zama Shi’a Sunnah a lokaci guda ba zai yi wu ba kenan sai dai ya zama Sunnah ya tsaya Sunnah ya kalli Shi’a a matsayin muslmi ko kuma Shi’a ya kalli sunan a matsayin musulmi a yi ta tafiya hakanan har Allah ta’ala ya kaimu ranar hukunci kowa yaso inda yayi gaba shi kenan.
Wannan shine dan kadan daga abubuwan da ni na fahimta. Daga cikin akidoji wanda yake tabbas ko wane mai yin SHI’A zaka same shi da wannan tunani Allahumma koda bai fada maka baki da baki ba, amma inda zaka ambaci daya daga cikin sahabban Manzon Allah (S.A.W) to zai ce la’anatullahi alayhi a cikin zuciyar shi ko da bai fada a baki ba.
In ya sami dama kuma zai fada a fili in ya sami dama to zaice la’anatullahi alayhi  in kuma bai sami da ma ba a cikin zuciya zai fadi la’anatullahi alayhi, haka nan kwo ko da AISHA ce (R.A) daga cikin matan Annabi (S.A.W). wannan kuma ba wani abu bane sai abin da yake cikin akidojinsu wanda suka kirashi TAKIYYA. Wato ka boye abinda yake cikin zuciyarka ka bayyanar da zahiri amma a cikin zuciyarka ga abinda kake nufe wato kana son ka cimma wani hadafi wannan kenan saboda haka daga cikin wannan akidoji wanda ba zai taba yi yuwa ba ne mutuman da yake musulmi ya yarda da su ko kuma ya karbesu,(2) ya yi watsi da nasa akidoji alal misali kamar cewa a’imma dinsu, shugabanin su wannan a’immatu ahlul-baiti ko da yake ai’immatu ahlul-baiti shugabani ne na kowa duk wani musulmi, Annabi (S.A.W) Allah ya ce masa “Kulla asalukum alayhi ajran ilal mawaddata fil-kurba” kace masu wannan sako da na kawo daga wurin Allah ba na tambayar ku, ku bani lada ko wani abu da zai anfanar da ni a duniya abin da nake so kuyi soyayya zuwa ga yan’uwa na makusanta namakusantan Annabi (S.A.W) sune alayensa da ya’yansa da jikokinsa son su wajibi ne girmamasu wajibi ne wato daga nassi a alkur’ani da kuma sunnar ma’aiki (S.A.W). Amma kamar su misalin bangaren SHI’A sun kaisu wani matsaya da yake Annabi ne kadai ake iya kaiwa;(3) yasan sanda zai mutu kuma ma sai in ya zaba zai mutu. Kaga wannan wani abu ne wanda yake mustahili, tunda yake mutuwa bata zowa mutum sai bagatatan(4) “Wama tadri nafsun bi ayyi ardhin ta mutu” ba wanda yasan inda zai mutu ko kuma yaushe zata zo mashi. Kuma cewa Imami yasan abinda yake faruwa yanzu kuma yasan abinda zai faru nan gaba da wanda yake faruwa a baya, kaga wannan wani abune da yake Allah kawai yasan wannan,To ashe kenan wannan ya nuna mana Shi’a daban Sunnah daban wato aka’id da mazahabobi na Sunnah daban aka’id da mazhabobi na Shi’a daban basu haduwa waje daya sau dayawa na san mutane ko rudarsu akayi ko rashin sani sukanga mutum suce ga dan Shi’a wannan dan Shi’a ne da sauransu, tun muna dai cewa basu bane harmun dake mun hakura saboda ba yadda za muyi ne kawai yan Shi’a, yan Shi’a to dai hakika wannan shine Hakikanin Shi’a kuma wannan shine hakikanin Sunnah. Kuma ba zai hana mai so yayi abinda yake so ba, mai son yi shi’a.
Kaga zai iya tashi daga Sunni ya koma waje daya ya Zagi Sahabbai ya kuma Zagi Matan Ma’aiki (S.A.W)  wasu ba’adinsu ko da kuwa a cikin zuciya ko da bai fada a fatar baki ba. Wanda yake son ya zama Sunni ne, shi Sunnah zai girmama sahabbai ya kuma girmama ahlul-baiti ya kuma girmama wato addini baki daya da wannan sakon da manzon Allah (S.A.W) ya zo dashi. Ya kuma dauka musulmin duniya suna karkashin inuwa daya itace La’ilaha-illallahu Muhammadurra-sulullahi (S.A.W) wannan shi ake cema INSAF, ADALCI KENAN. Domin ba zaka iya korar dan Shi’a daga musulunci ba kamar yadda dan Shi’a ba zai iya korar musulmi daga musulunci ba, in haka ne ko dole mu samu insafi a tsakaninmu.”
Allah sarki ka ji dan’uwa tsarabar IRAN daga bakin Malam
ALLAH KA TSARE MU DAGA BATA

1 comment:

  1. Uhmm shi'anci kenan ai gaskiya malaminsu ya fada bawai tabargaza bace abinda yafi hakama zai iyaji

    ReplyDelete