Sunday 25 September 2016

NURUN ALA NUR " BAN SAKI AHLUL BAITI BA NA KAMA SAHABBAI" (01)

*NURUN ALA NUR "BAN SAKI AHLULBAITI BA NA KAMA SAHABBAI"*

*Fitowa Ta [01]*

Daga: *_Dr Mansur Ibrahim Sokoto_*

Labarin Sheikh Ali Dan Muhammad Al-Kadhibi - Wani malami dan kasar Bahrain da Allah ya ganar da shi gaskiya ya dawo daga rakiyar Shi'a.

GABATARWA;
“Godiya ta tabbata ga Allah, godiya mai yawa, mai tsarki, mai albarka wadda ta cike sammai da qasa da duk abin da Allah ya so bayan su. Tsira da amincin Allah su tabbata ga zababben bawansa, cikamakin manzanninsa; annabi Muhammad da iyalansa da sahabbansa da duk wadanda suka bi su da kyautatawa har rana ta qarshe. Bayan haka:
Na yi wannan dan rubutu ne don in zayyana ma mai karatu wasu ‘yan nazarce-nazarce da wasu ‘yan tambayoyi da na yi ma kaina har suka ja ni zuwa ga gaskiya wacce ban taba tunanin - a can baya – zan iya janyuwa zuwa gare ta ba.
Rikici ne ba na wasa ba, kuma aiki ne ja; mutum ya bar abinda ya saba da shi kuma ya gaje shi daga iyaye da kakanni idan ya gane cewa gaskiya ita ce sabaninsa. Ba ni kadai abin ya shafa ba, da yawa wadanda suka qarar da rayuwarsu a wajen kare wata manufa ko tabbatar da wata aqida, kwatsam! Sai Allah ya ganar da su cewa ba a kan daidai suke ba. A nan ne mutum zai yi ta fama da rikici a tsakanin sa da zuciyarsa amma idan ya daure sai Allah ya yi ma sa gamon katar. A nan ne mutum zai gane cewa, riqo da rubabbiyar aqida don kawai son zama tare da ‘yan uwa da dangi bai kamata ba. Idan mutum ya yi haka to, ya yi cinikin duna wanda ba shi da riba sai hasara. A maimakon haka kamata ya yi mutum ya yi riqo da gaskiya a lokacin da ta bayyana gare shi."
Baban Khalifi
Muhammad Al-Qadhibi

TUNA BAYA;
Tun da farko na tashi a gidanmu na tarar da iyayena masu tsananin kula da riqo da addinin Shi’a. Ban yi wayon sanin mahaifina ba sai dai kawuna wanda ya riqe ni tsakani da Allah bayan mutuwar mahaifin nawa. Kawuna yana cikin shehunai masu rawani, kuma ya yi karatu a Hauza ta yankin Jadd Hafs a qasar Bahrain, bayan nan kuma ya samu qarin ilimi a babban birnin Qum na qasar Iran.
Ba zan manta yadda kawuna yake kula da mu yana ba mu tarbiyya ba, yana hana mu cudanya da bata gari don kada su gurnata mu. A ranar da ya ji ina cewa zan karanci ilimin kida a jami’a idan na gama makarantar sakandare bata ransa ya yi, sannan ya kira ni cikin lumana ya lurar da ni, ya ce, ka ga ni, sa’ad da nake yaro irinka ban samu mai dora ni a kan hanya ba. Ya rinqa rarrashi na har ya canja min ra’ayi. Wataqila da yanzu ni wani shahararren makadi ne.

Mahaifiyata ita kuma ba ta da aiki sai jiran lokutan bukukuwa wadanda ake yi akai-akai don raya addinin Shi’a. Tana bugun gaba da shiga a cikin su tana ganin – ta haka – za ta samu falalar hidimar sayyidi Husaini. Sau da yawa takan je bukukuwan ko ba ta da lafiya. In aka yi ma ta magana sai ta ce, ai shiga wannan sha’ani shi ne maganin ciwonta. Mahaifinta kuwa sana’arsa ita ce yin ganguma da ake kida da su a bukukuwan Ashura da sauran bukukuwa da makokai da ake yi a koda yaushe. Wani abin da mai karatu zai so ya sani shi ne cewa, dukkan mu muna bin tafarkin shehun malami ayatullahi.

No comments:

Post a Comment