Saturday 17 September 2016

Mal Baban Hamdan
Sanarwar gaggawa.
A FADA A CIKA SAI SAUDIYYA: A wani zama da aka yi da babban limamin Haramin Makkah ga babban Malamin mu, Shaikh Dr Mansur Ibrahim Sokoto, Shaikh Professor Abdurrahman Sudais yake sanar da cewa akwai wata jami'a ta musamman da Qasa mai Tsarki za ta bude don horas da masu sha'awar karatun Shari'a ko Ilimin Al-Qur'ani, qafin a shiga sabuwar Shekarar 1438.
Har na cika da mamakin ga shi yau ana 14/12/1437 (saura sati biyu shekara ta qare) amma ba mu sami labarin an bude wannan jami'a mai albarka ba ballantana a fara daukar dalibai, kwatsam sai ga sanarwa ashe an bude wannan jami'a har an fara daukar dalibai kamar yadda Shaikh Sudais ya tabbatarwa su Mallam tun 20/11/1437 kuma za a ci gaba da dauka har 20/12/1437 a kuma fara karatu 1/1/1438 insha Allah.
Don haka a madadin Mallam ina shelanta sanarwar daukar dalibai maza da mata, a matakin karatun Diploma (shekara 1) ko Degree (shekara 4).
Za a iya yin karatu a can garin Makkah ga maza, maza da mata kowa zai iya yin rajistar karatun distance learning.
Ba a biyan kudin makaranta, karatun kyauta ne, kuma ba qa'idar shekarun dalibi. Admission nan take ne ga wanda zai yi karatun distance learning, wanda kuma zai je can Makkah za a ba shi admission nan take amma za a qara tantance shi.
Matan aure da ma'aikata da zaunannu wannan babbar dama ce da za a yi karatu daga gida, a sami ilimi mai nagarta ga kuma gangariyar takardar shaidar kammala degree ta Jami'ar Ummul Qura, karbabbiya a duk fadin duniya; masu sha'awar zuwa can Saudia kuwa sun fi kowa morewa.
Sunan makarantar 'Jami'atu Imam al-Da'wah' shugabanta Professor Shaikh Abdurrahman Sudais, babban limamin Haramin Makkah, ga kuma link din cike form. Da fatan za a cike kuma a yada wannan sanarwa ta shiga lungu da saqo domin yau saura kwana 6 kacal a rufe.
Allah Ya sa mu dace.
Arabic: http://mojamah.com/register.php
English: http://mojamah.com/register-en.php

1 comment: