Saturday 17 September 2016

Ghadeer Khum 1

BIKIN IDIN GHADIR KHUM KO IDIN GHADAR KHUM (1) DARUSSA DAKE CIKIN HAJJIN BAN KWANA DA HUDUBAR GHADIR KHUM (Farfajiyar GHADIR KHUM kenan maikaratu ke gani a cikin wannan hoto) HAJJIN BAN KWANA : Shine aikin hajji da Annabi (saw) da cuncurundon SahabbanSa (raa) daga ko ina suka halarta a shekara ta goma (10) bayan hijira. KHUM : Sunar wani mutum mairine ne da ake kiran wani kwari dake tsakanin Makkah da Madina da shi, wanan wuri yana da tazarar mil uku (3km) daga Juhfa (muhallin daukar miqatin mutanen sham). GHADIR : Ana nufi wurin dake da idanun ruwan da bishiyoyi suka kewaye mabubugan ruwan. Akan haka ake hade sunayen biyu a kira wurin da sunar GHADIR KHUM. A wannan wuri ne Annabi (saw) da SahabbanSa (raa) da wadanda hanyar garuruwansu take ta kan wannan hanya, suka yada zango bayan da suka gama aikin hajjin ban kwana suke komawa izuwa gida. Anan ne yayi shaharrariyar hudubar dake a dunkule take wanke ciki da wajen Imam Aliy bn Abiy Talib (ra) da bisa yawan maganganu da koke da suka samo asali daga mutanen da yake shugabanta daga Yeman, bayan da wasu abubuwa suka faru tsakaninsa da su akan : 1. Daukarsa (zaben) wata kyakkyawan kuyanga daga cikin ribatattu. 2. Hana su amfani da kayan ado da yayi, bayan na'ibinsa ya basu dama. 3. Abinda wasunsu suka kira da kaushin hali ko tsanani daga bangarensa gare su. Akan wadannan abubuwa ne maganganu suka yi ta kai komo a tsakanin mutanen Yeman a lokacin aikin hajjin ban kwana, har ta kai ga matsayin wasu daga cikin Sahabbai (raa) da suke karkashins suka kai kokensa wurin Annabi (saw). Kasantuwar hajjin ban kwana shine mafi girma da taron jama'ar musulmi daga dukkan garuruwan musulmi da Annabi (saw) ya taba shaidawa, wadanda basu taba ganinSa ba (saw) suka ganshi, anan ne yayi hudubarSa mafi tara mutane, inda a cikinta yayi wasici da kyautata wa mata da wadanda hannuwan dama suka mallaka, kuma ya kafawa mutane hujja akan shaidar ya isar ma 'ya'yan Adamu sakon Allah Ta'alah, kuma a wannan mauqifi na Arfah ne Ayahr cikon addini : "اليم أكملت لكم دينكم وأتممت عليكم نعمتي ورضيت لكم الإسلام دينا" ta sauka gare Shi (saw). Kasantuwar wannan kadiyyar (koke da nuna kiyayya ga Imam Aliy) bata shafi dukkan Sahabbai ba, sai Annabi (saw) baiyi huduba akanta ba a cikin kwanakin aikin hajji, ta inda sakonta (abinda mabarnata ke riya cewa NADIN KHALIFANCI ne) zai isar da ita wa gaba-dayan dukkan Sahabbai, kamar yadda yayi wancan hudubar a filin Arfah, inda a wurin ya ambaci maganar kyautata wa mata da sauransu da maimaita tambaya wa Sahabbai : shin Na isar da sakon Allah? Sahabbai (raa) suka amsa da cewa : Tabbas Ka isar. Duk wannan ya faru ne akan idanu da shaidar dukkan Sahabbai da suke halarce a wurin, amma fangane da koken mutanen Yeman sai Ya jinkirta bada jawabi akai, sai a hanyar komawarsu gida bayan da ya yada zango a wannan kwari na GHADIR KHUM, inda anan ne a ranar 18th/12/10 AH yayi hudubar da sababinta shine wancan koke, kuma domin Ya bada amsa wa masu koke akan Aliy bn Abiy Talib (ra), inda a cikin hudubar yace : " من كنت مولاه فهذا علي مولاه اﻟﻠﻬﻢ ﻭﺍﻝ ﻣﻦ ﻭﺍﻻﻩ، ﻭﻋﺎﺩ ﻣﻦ ﻋﺎﺩﺍﻩ، ﻭﺍﻧﺼﺮ ﻣﻦ ﻧﺼﺮﻩ، ﻭﺍﺧﺬﻝ ﻣﻦ ﺧﺬﻟﻪ " "Duk wanda Na kasance majibincinsa, toh wannan Aliyu majibincinsa ne, Ya Allah, Ka jibinci duk wanda ya jibince shi, Kayi adawa da duk wanda yayi adawa da shi, Ka taimaki duk wanda ya taimake shi, kuma tabar da duk wanda ya tabar da shi." (bangaren wannan hadisi da tsawonsa haka yana tangardan rashin inganci, amma zamu kaddara ma gaba-dayansa ya inganta). Wannan huduba ita ce wasu Maluman musulunci suke kiranta da sunar HADISIN GHADIR KHUM, wassu kuma ke kiranta HADISIN WILAYA, a yayin da bakin haure wa Musulunci ke kiranta HADISIN DASA KHALIFA. Ga Musulmai ma'anar wannan hadisi shine qara fitar da falalar Aliy (ra), wurin nuna tsarkin ciki (zuciyarsa) da wajensa (zahirinsa) da jibintarsa ta hanyar kaunarsa da yi masa biyayya da barrantar da shi daga hikidu ko son zuciya ko kin muminai, amma sam basu fahimci ma'anarta shine NADA SARAUTAR KHALIFA bayan Annabi (saw) ba. Wannan itace tabbatacciyar fassara a janibin masu bin Musulunci sau da kafa da tsarkakakken zuciya, ba tare da NIFAQA ba. Amma akasi itace fassarar wannan huduba a janibin masu ciwon zandaqah a cikin zuci, kuma masu adawa da karantarwan Annabi (saw), wanda idan muka kaddara daukan fassararsu ga hadisin tana nufin wasici ne ga NADA SHI SHUGABA A BAYAN ANNABI (SAW) kamar haka : ١. من كنت مولاه فهذا علي مولاه "Duk wanda na kasance SHUGABANSA, toh Aliyu wannan SHUGABANSA ne" MAS'ALOLIN DA SUKE CIKIN IRIN WANNAN FASSARA : 1. Babu abinda ke nuni da hana wani ma ya zamanto shugaba a bayansa. Sannan matsayin Imam Aliy (ra) a wurin Musulmai shine yana daga cikin Shuwagabanninsu. 2. Kenan wannan fassara tana nufin Sahabbai kamar Ansar (raa) bassu fahimtar harshen larabci, domin sune yayin sallama khalifanci wa Abubakar (raa) suka ce : منا أمير ومنكم أمير "Cikinmu akwai shugaba, kuma cikinku akwai shugaba" 3. Ina laifin Sahabbai (raa) akan abinda Imam Aliy (ra) yayi shiru akai ranar da aka mika bai'a ga Abubakar (raa) bai tashi ya tunashe su wannan nadi nasa ba? 4. Wannan magana jingina wa Imam Aliy (ra) rashin sanin wannan kalma مولاه tana nada shi khalifa ne, domin kamar yadda tazo a cikin littafin (Nahjul Balagha, 1/191) ranar da mutane suka yi cuncurundo yi masa mubaya'a, sai yake ce musu : " ﺩﻋﻮﻧﻲ ﻭﺍﻟﺘﻤﺴﻮﺍ ﻏﻴﺮﻱ " "ku fita sha'ani na ku nemi wani na" Kaga da yasan wancan kalmar nada shi khalifa Annabi (saw) yayi, da sam ba zaice musu su nemi waninsa ba. 5. Ina hikimar dake cikin murtaddai (kamar yadda suka ce sahabbai sunyi ridda akan wannan kadiyyar) zasu zo gaban Imam Aliy (ra) yi masa bai'a, amma sai bai nemi su jadda kalmar shahada ba don su dawo Musulunci kafin ya karbi bai'arsu, ko karbar bai'ar kafiri ya halasta ne? 6. Ko akwai ingataccen ruwayar da ke nuna Fatima Albatula (raa) ta na sane da wannan nadin, har ta shahara da neman a zartas da shi kan Mijinta, sabanin Fadak? ٢. اﻟﻠﻬﻢ ﻭﺍﻝ ﻣﻦ ﻭﺍﻻﻩ "Ya Allah, Ka jibinci duk wanda ya jibince shi" MAS'ALA : 1. Wannan addu'a ce da Annabi (saw) yayi ga wadanda suka shugabantar da Imam Aliy (ra) a bayansa. Abinda masu irin wannan fassara suke nufi, shine wannan addu'ar da Annabi (saw) yayi bata yi aiki akan Aliy (ra) ba sai akan Abubakar Siddiq (raa). Tunda suna nufin akasin fassarar musulmai shine daidai, sai a tambaye su : ya aka yi Allah ya jibinci wadanda suka jibinci Abubakar ta hanyar shugabantar musu da wanda suka shugabantar? ٣. ﻭﻋﺎﺩ ﻣﻦ ﻋﺎﺩﺍﻩ "Ya Allah Ka yi adawa da duk wanda ke adawa da shi" MAS'ALOLI : 1. Tabbatattun tarihin musulunci sun tabbatar ba asan wani sahabi guda daya ba da ya shafe rayuwarsa bayan wafatin Ma'aiki (saw) yana adawa da Abubakar (ra) ba. 2. Tarihi ya tabbatar Abubakar da Umar da Usman (raa) basu yi adawa da Aliy (ra) ba, kenan wannan yana daga cikin hikimar kasantuwar suka yi khalifanci gabaninsa. ٤. ﻭﺍﻧﺼﺮ ﻣﻦ ﻧﺼﺮﻩ "Ya Allah, Ka taimaki duk wanda ya taimake shi" MAS'ALOLI : 1. Da irin fassarar masu fassarar wannan hadisi da nada khalifa, sai muce kenan kuna nufin wannan addu'ar ma akan Abubakar (raa) tayi aiki, domin a bayyane shine Allah ya bada nasara ga wadanda suka sallama masa khalifanci, banda akasin hakan? 2. Allah ya karfafi Abubakar da Umar da Usman (raa) saboda sun karfafi Aliy a duk inda ya kamata su karfafe shi, kamar wurin : sadar masa zumuncin kasantuwarsa jinin Manzon Allah (saw), ba shi kaso a cikin abinda aka rabauta, sanya shi a cikin majalisar koli na shawari da sauransu. ٥. ﻭﺍﺧﺬﻝ ﻣﻦ ﺧﺬﻟﻪ "Ya Allah, Ka tabar da duk wanda ya tabar da shi" MAS'ALA : 1. Allah bai tabar da Abubakar ko Umar ko Usman (raa) ba, domin babban abinda zai fitar mana da hakan fili, shine kasantuwar a tsakanin sahabbai sune Musulmai suka fi sanya sunayensu wa 'ya'yayensu, kuma sune Musulmi ke kidanya su a matsayin khalifofin farko, wanda da Allah ya tabar da su da tunin an manta da tarihinsu ko an daina ambatonsu da alheri. BABBAN ABIN TAMBAYA : IDAN WANCAN HADISI NADA KHALIFA KE TABBATARWA, SHIN DUK WADANCAN ADDU'OIN DA ANNABI (SAW) YAYI WA IMAM ALIY (RA) KUNA NUFIN KUCE ALLAH BAI KARBESU BA KENAN? Daga 'Dan Almajiri : Salihu Baban Takko 17th/12/1434 AH - 22th/10/

No comments:

Post a Comment