Sunday 25 September 2016

Tunatarwa ga Jami'an tsaro Mal Baban Hamdan

Sabon saqon Boko Haram: tunatarwa ga jami'an tsaron Nigeria.

Tun ba a yi nisa ba, Marigayi Shaikh Ja'afar Mahmud Adam ya bayyanawa duniya, ya sirrintawa mahakunta hatsarin Da'awar Boko Haram, qarshe Allah Ya rubuta masa shahada a hannun miyagu yana sallar asuba daren juma'a, Allah Ya masa Rahama Ya kyautata makwanci.

A wani wa'azin Izala da aka yi a garin Maiduguri, ana tsakiyar Boko Haram, Shaikh Sani Yahya Jingir Allah Ya qara lafiya Ya kare shi,  ya hau minbari ya bayyanawa duniya Boko Haram ba musulunci bane, kuma ya shawarci mahakunta su tsananta sa ido da tsaurara matakan daqile tunani da ta'addanci irin na Boko Haram. Sakamakon haka 'yan ta'adda suka kai masa hari da boma-bomai da bindigogi yana tafsirin al-Qur'ani, Allah Ya tserar da shi, amma an rasa rayuka, ciki har da dan Shaikh Muhammad Nasir AbdulMuhyi.

Shaikh Albani Allah Ya ji qansa shi cewa ma ya yi idan dan Boko Haram ya shigo masallacin sa, za su yi dauki-ba-dadi, sabo da yadda kowa ya fada musu a kan halaka su ke amma sun qi ji, a lokacin kuma suna nema su gagari jami'an tsaro, qarshe Allah Ya masa shahada a hannun 'yan ta'adda.

Malaman sunnah da suka rasa rayukansu a kan fada da Boko Haram ba za su lisaafu ba amma hakan bai hana su ci gaba da fafatawa ba. An ga yadda Shaikh Isa Ali Pantami da Mal Idris AbdulAziz suka yi muqabala a bainar jama'a suka bayyanawa 'yan Boko Haram kuskuren fahimtar su ga addini, tun ma Muhammad Yusuf na da rai, tun Boko Haram bata fada hannun 'yan sari irin yanzu ba.

To Malaman Sunnah ba su yi qasa a gwiwa ba, amma maganar ita ce, an san tushen aqidar Boko Haram jagoran 'yan shi'a ne, Zazzaki, wanda yanzu haka yake hannu, ya kawo ta Nigeria. An sani sarai, Zakzakiy ne ya fara cewa Boko Haram ne a wajajen 80s, ya sa mutane suka fice daga makarantu, wasu ma sun gama suka riqa yayyaga takardun su. Sannan an ruwaito shi kansa Muhammad Yusuf tsohon almajirinsa ne, daga bisani ya tuba, tuban muzuru. A bakin Zakzakiy kalmar 'bara'a' ta bayyana a tsakanin matasa, wanda har yanzu 'yan shi'a suna qudurce da ita, har da wani Chemist na gargajiya wai shi 'Bara'a Chemist'.

Ma'anar bara'a ita ce abin da Boko Haram suka yi, wato raba gari da duk wani tsarin gwamnatin Nigeria sabo da ba tsarin Allah bane, ba tare da la'akari da halin da aka sami kai a ciki na zamantakewa tsakanin Musulmi da wadanda ba Musulmi a qasa daya ba. Qarqashin wannan ne za a ji suna cewa 'ba hukuma sai ta Allah' ma'ana ba su yarda da gwamnatin Nigeria ba sai ta Zakzakiy da ta Iran kamar dai yadda Boko Haram ba su yarda da ita ba sai ta Shekau da ISIS.

Wannan ita ce Aqidar 'yan shi'a kuma ba sa musu a kan haka.

Duk wanda ya bibiyi maganganun Zakzakiy a kan Boko Haram, ya san aqidar Zakzakiy ita ce 'ba Boko Haram, gwamnati ce Boko Haram'. Mutane da yawa, la'alla har wasu cikin jami'an tsaro, basu fahimci me Zakzakiy yake nufi ba. Da yawa suna fahimtar yana nufin babu wasu mutane 'yan Boko Haram masu aqidar Boko Haram, amma ba haka bane. Zakzakiy ya san awai su, amma yana nufin su 'yan Boko Haram su ne suka fi kusa da gaskiya, ita gwamnati ita ce Boko Haram, 'yarta'adda.

Don haka Zakzakiy yana ganin za su iya haduwa da Boko Haram don a hambarar da gwamnatin Nigeria daga baya sa daidaita tsakanin su, amma ba za su iya haduwa da gwamanti su ga bayan Boko Haram ba in yaso sa sasanta tsakanin su daga bisani.

Kamar yadda zai wa gwamnati wahala ta samo kan Boko Haram cikin laluma sabo da alaqar da Boko Haram din ta qulla da ISIS, haka ma 'yan Shi'a, domin su kuma daga Iran ne kawai za a basu umarni su karba. Ita kuma Iran ba za ta bada wani umarnin gaske wanda ba na tada hankali da yi wa hukumomi bore da gwagwarmayar juyin-juya-hali ba.  Za a iya ganin haka, a yayin da mahakuntan Saudi Arabia ke hado hancin qasashen musulmi don yaqar munanan aqidu irin na ISIS da Boko Haram da Hizbolla da sauransu, ita Iran baza mugga-muggan makamai take yi a qasashe, hatta nan Nigeria an kama jirgin ruwa maqare da makamai daga qasar Iran, da kuma wasu dandazon wasu makaman a Kano a hannun 'yan shi'a.

Alhamdu lillah, malaman sunnah sun yi aiki tuquru wajen tsare tunani da aqidar jama'a, kuma ba fargabar ko wace irin matsala, amma babbar matsar da dole za ta kasance in ba a yi wa tufkar hanci mai qarfin gaske tun qafin ta fara bajewa ba ita ce ta shi'a.

Insha Allah za mu ci gaba da bayyana hatsarin 'yan shi'a a qasa da yadda za su zo su fi Boko Haram barna idan ba a dauki qwararan matakai tun yanzu ba.

Allah Ya tsare mu da tsarewarsa Ya bamu zaman lafiya a qasarmu Nigeria.

No comments:

Post a Comment