HANA KARUWANCI DA FATAUCIN MIYAGUN
KWAYOYI A Karamar Hukumar Kafur
Daga Hassan Kabir Yar'adua
HARAMTA KARUWANCI DA KULLE GIDAJEN GIYA/KAYAN MAYE
A wata zantawa da nayi ta wayar tarho da kantoman riko na
karamar Hukumar Kafur a jahar Katsina Alh Hamza Umar Nasarawa (Mai Garin
Sabuwar Kasa) ya bayyana cewa sakamakon zaman da kwamitin tsaro na hukumar tayi
kan korafi da aka yi game da lalacewar tarbiyyar matasa wanda karuwanci da gidajen
giya/kayan maye ke haifarwa hakan yasa mu ka ga babu mafita illa muyi abunda
Allah ya umarce mu (masu madafun iko) muyi na hana karuwancin da fataucin
miyagun kwayoyin.
Shugaban karamar hukumar ya bayyana
cewa sun sanya dokar kulle gidajen karuwanci da sha da fataucin kwayoyi a gaba
dayan yankin na Kafur, duk wanda aka samu yana saidawa ko sha ko zuwa gidajen
karuwancin to Doka za ta hau kanshi. Daga karshe ya bayyana cewa an rufe
gidajen nan da ake masha’a.
Wannan
alkairin na da nasaba da canjin aiki da aikawa wani malamin addinin musulunci daga
karamar hukumar Katsina zuwa Karamar hukumar Kafur, wanda ya bada gudumuwa kwaran
gaske wurin tabbatar da wannan aikin alkhairin. Malamin yanzun haka yana ta
kokarin sanya al’ummar yanki bisa koyarwar addinin musulunci ta hanyar gabatar
masu da majalisai na karatu da kuma kokarin tabbatar da da’ar ma’aikatan
yankin.
Muna fatan sauran kananan hukumomi da jahohi su ma su yi
koyi da wannan karamar hukumar domin dorewar rayuwa ingantaciyya ta musulunci.
No comments:
Post a Comment