Tuesday 3 January 2017

Majnun Laila

LABARIN SOYAYYAR LAILA
MAJNUN
Waye majnun lailah? Wani mutumne da aka yi a daular banu umaiyya abisazance mafi inganci. Sunansa shine Qais Bn Mulawwah daga kabilar Banu Amir, Qais balaraben kauyene, ya taso tare da ‘yar gidan kawunsa mai suna LAILA
BNT MAHDI IBN SA’D Amfi sanin Laila da sunan Laila Aamiriya, tare suka taso tun suna yara suna kiwon dabobi har suka girma, suka fita daga sahun yara suka kai munzalin balagha.
A Yayin da alamun nuna balaga da cikar budurci suka gama bayyana ajikin Laila sai Qais ya rude soyayyarsa gare ta, hankalinsa ya dugunzuma ya tashi.
Domin a wannan lokacin ne Qais ya
Llura da irin kyawun dirin da Allah ya
yiwa abokiyarsa Laila, a kullum
soyayyar Laila sai kara tashin gwauron zabi take yi a cikin zuciyar Qais, a cikin wannan yanayi ne Qais ya shiga rera
mata waqoqin soyayya kala-kala babu dare babu rana hakance tasa Mahdi mahaifin Laila ya nemi da Qais ya fito dan maganar aure, saboda nuna soyayya da kauna said a Qais ya bayar da raquma hamsin gidansu Laila a matsayin kudin aure.
Ana haka sai ga wani mutum da ake
kira WIRD BN MUHAMMAD wani dan
hamshaqin attajiri ne daga cikin
‘ya’yayen masarautar Banu Umaiyya,
katsahan yayi ido hudu da Laila a wata rana a cikin wani Lambu tana kiwon dabobinta. Daga wannan rana Soyayyar Laila ta hana Wird ya yi bacci a wannan dare! Cikin yan kwanaki kadan Iyayen Wird suka sauka a gidan su Laila dan neman aurenta ga dansu
Wird. A wannan rana da Iyayan Wird
suka je ga mahaifin Laila said a suka
ajiye masa Manyan Raquma guda dari (100) a matsayin kudin aure, wato ribi biyu akan abinda Qais ya bayar! Daga nan lissafi ya kwacewa mahaifin Laila, domin kuwa yayi irin mugun abin kunyar nan na nuna kwadayi da son abin duniya. Bayan haka ne Mahaifin Laila ya kira ‘yarsa Laila cikin daki yanai mata hudunbar cewar ga mai kudi dan masu mulki shi zai aurawa ita! Babbar Magana! Laila taki amincewa da maganar mahaifinta a karon farko, amma sai ya yi mata barazanar cewar zai yanka ta idan har bata amince da auren Wird ba! Kwatsam sai aka wayi gari Qais ya ji gari ya dauka da kace nace din anyiwa masoyiyarsa Laila aure, da Wird. Wanne irin hali Qais zai kasance a wannan ranar? Tun daga wannan lokacin bacci yayi hijira daga idonsa, farin ciki ya gagari zuciyarsa, damuwa bakin ciki gami da bacin Rai da takaici, zubar da hawaye babu dare babu rana,
suka kasance tare da Qais a matsayin abokai na din-din-din!
Wake waken soyayya sune zancensa, bashi da abokin hira sai wakar da yake yiwa laila ga kadan daga irin abinda yake cewa:
zuwa ga Allah nake kai kukan son laila kamar yadda maraya yake kai kukan maraicinsa zuwa a Allah.
Marayanda da kafasa ta karye gashi
kuma dangi sun gujeshe
Lallai rasa iyaye abune mai girman
gaske.
Haka Qais da aka yiwa lakabi da
“Majnunu lailah” yake bin kwararo
kwararo da saman manyan duwatsu da bakin ruwa da cikin furanni yana
rerawa Laila wadannan baituka masu motsa zuciya bai gushe ba harse da akayi masa lakabi da “majnunu laila”....!
Duk da cewa itama Laila tana matukar son Qais(majnun) amma kuma hakan baya hanata ta wahalar dashi, a wasu lokutanma harda yi masa wulaqanci, baya ga yin amfani da mallakeshi da tayi wajen azabtar dashi, dama haka
sha’anin mata yake shi yasa majnun
awani baiti yace:
“Nace da wani babban malami da na
gamu dashi a makka, dan Allah ka bani
labarin wacce take cutar dani,
azamanin da take jiji da kai (saboda ina
sonta) shin hakan da take ba laifi
bane?” Sai Malamin ya fadawa Qais
cewa: “Wallahi da sannu azaba zata
shafe ta kuma a duniya ma saita hadu
da bala’I”. Dagan an Qai yace, sai na
kasa mallakar idona sai da hawaye ya
zubo cikin sauri ya jiqa min aljihun
rigata, sai nace, Allah ya yafe mata
laifinta duk da yake a duniya dan
kadanne samunta.
Qais ko Laila Majnun Bai gusheba a
cikin wannan hali har sai da ya samu
tabin hankali. Domin ya kasance idan
yaga yara suna wasan kasa yakan zauna
tare dasu ya taro kasa ya rinqa gina
gida irin wanda yara suke yi da kasa
yana cewa cikin waqa: “abokaina kuzo
kuga gidana nida laila”....!
A yayinda al-amari ya tsananta sai
mutane suka baiwa mahaifin Majnun
wato Qais shawara da ya daukeshi ya
kaishi ka’aba (dakin Allah) ya umarce
shi da ya roqi Allah ya cire masa son
Laila! Amma saboda tsananin soyayya a
yayin da suka je dakin ka’aba sai
mahaifinsa yace masa: kama tufafin
ka’aba ka roki Allah ya cire maka son
Laila sai Majnun ya kama yace: “Allah
na tuba gareka daga dukkan laifi,
amma bazan tuba daga son da nake
yiwa Laila ba . . . ataqaice haka majnun
ya rayu cikin wannan yanayi na abin
tausayi!
Ita kuwa Laila tuni wanda ya aureta ya
dauke daga kasar Saudiyya gabaki daya
zuwa kasar Iraqi. Haka itama ta rayu
cikin wannan mummunan yanayi
abinka da ‘ya mace mai rauni said a
rashin ganin Qais ya haddasa mata
ciwon zuciya .......! Daga nan ita ma ta
kamu da ciwon zuciya saboda tsananin
soyayyar Qais Majnun! Tana cikin
wannan hali ne na rashin ganin
masoyinta Allah ya karbi rayuwarta! A
lokacin da Majnun yaji labarin
rasuwarta sai da yaje har kasar Iraqi ya
nemi inda take, da inda aka binne ta, a
makabartar da aka binne laila a daidai
gindin kabarinta ya tare.....! Bashi da
aiki sai kuka da wakokin soyayya a
gareta. Wata rana da safe sai masu
wucewa suka hangoshi (Qais-Majnun) ya kifa cikinsa akan qabarinta, ko da aka zo aka duba sai aka tarar Allah ya yi masa cikawa! Haka fa Allah yakejarabtar wasu da soyayya, dan Hakka idan kaji Hasan na sambatu akan Hasana kada ka zargeshi.