Wednesday 5 April 2017

Jami'ar Al-Qalam ta tallafa ma yan gudun hijira a karo na biyu

Jami'ar musulunci ta Al-Qalam dake Katsina ta qara tallafa ma yan gudun hijira mazauna jihar ta Katsina a jiya Talata 04/04/17. Shugaban Jami'ar Prof Shehu Ado Garki ne ya hannanta kayan ga kungiyar mata masu da'awa wato Da'awah Family Support Katsina wanda ke kula da yan gudun hijirar, Shugaban jami'ar  ya bayyana cewa wannan shine karo na biyu da suka bada irin wannan tallafi,  kayayyakin da aka bada tallafin sun hada da Buhun masara guda 6, sai buhun gero guda 1, sai  buhun shinkafa guda 5, kwalin supergetti guda 7, Jarkokin mai guda 3.
A garin Katsina akwai yan gudun hijira wanda aqalla sun haura mutum 800 wanda qungiyar Da'awah Family Support ke kula da cin su da shansu, mazaunin su da suturarsu da kuma maganinsu DSS. duk wannan qungiya ke kula da su. Kamar yadda Malama Asiya shugaban kwamitin Idps ta kungiyar ta bayyana. Taron bada tallafin ya samu halartar mataimakin shugaban jami'ar Dr. Muhd Muslim Ibrahim, Rajistra, Bursar, Mustapha Audu Radda (P.R.O) da sauran muqaraban jami'ar, daga bangaren Da'awah Family support kuma Akwai Malama Asiya da kuma uwar kungiyar Da'awah Family Support Haj. Amina Ahmad Bawa Faskari, Husain Kabir Yaradua sai kuma Hasan Kabir Yaradua. Daga qarshe muna kira ga al'ummar jihar Katsina musamman masu hannu da shuni da su yi koyi da wannan jami'a wajan taimaka ma yan gudun hijira wanda Duke cikin wani irin mawuyacin hali wanda ta kai wasun su har sun fara bara. Allah ya agaza masu ya kuma bamu ikon taimakawa.

Hasan Kabir Yaradua

05/04/17.

No comments:

Post a Comment