Sunday 12 February 2017

Yada Hoton Gawa

Daga Malaminmu:

Dr. Muhd Sani Umar

Yada Hoton Gawar Dan Uwanka Mumuni Ba aiki Ne Na Masu Sanin Ya Kamata Ba

Wadanda suke dauko hutunan gawawwakin 'yan uwansa musulmi suna yadawa a dandalin sadarwa, wai don su sanar da rasuwarsu ko su yi ta'aziyyarsu, masu yin haka ba sa kyautawa ko kadan. Yin haka alama ce ta rashin wayewa da karancin fahimtar addini.

Gawar dan uwanka tana da alfarma da mutunci, bai kamata ka keta masa wannan mutuncin ba bayan mutuwarsa. Shi ya sa ko wankan gawa ba kowa ake sa wa ba sai wanda aka yarda da shi.

Ka duba, mutum ko barci yake yi ba zai so a dauki hotonsa ana yadawa ba, saboda ba lalle ne ya kasance cikin yanayin da zai so a gansa a cikinsa ba. Ka dubi yanayinka kai kanka, idan za a dauki hotonka kakan shirya don ganin hotonka ya yi kyawon kama, to don menene za ka rika baza hoton gawar dan uwanka bayan mutuwarsa? Kuma shin ba za a yarda da labarin mutuwarsa ba ne sai ka sa hotonsa?

Abin takaici ma wani lokaci wani ya jima da rasuwa amma idan wani ya zo magana a kansa sai ya sako gawarsa a cikin wani yanayi wanda bai dace ba sam, kuma shi mamacin da yana da rai ba zai so a gan shi a wannan yanayin ba.

Wani lokaci 'yan uwa za su yi hadarin mota suna kwance kace-kace cikin jini, sai wani sakarai ya dauko hotunansu yana bazawa wai shi a tunaninsa daidai yake yi, tir da irin wannan aiki na rashin nutsuwa.

Mu kiyaye hakkin yan uwanmu bayan mutuwarsu kamar yadda muke kiyaye shi a lokacin rayuwarsu. Allah ka ba mu kyakkyawar fahimta. Amin.

No comments:

Post a Comment