Wednesday 19 October 2016

KO JAHILCI KO SON ZUCIYA

Dr. Muhd Rabiu Rijiyar Lemu

KO JAHILCI KO SON ZUCIYA!!

Duk wanda ka ga ko ka ji yana sukan Ahlussunnah da cewa suna kafirta musulmi, to za ka ga ko dai jahili ne, bai san addini ba, bai san tarihin kungiyoyi da akidunsu ba a musulunci, KO kuma mai son zuciya ne da gaba da sunnah da Ma'abotanta.
Wani abun mamaki zaka samu masu cewa Ahlusunnah suna kafirta musulmi suna kawar da kai daga wadanda suka fi kowa kafirta musulmi a duniya, wato shi'a, wadanda suka kafirta muminan farko, Sahabban Manzon Allah S.A.W. da duk wanda ya bi tafarkinsu har zuwa ranar Alkiyama.
Babu wata kungiya ko jama'a da suke rabuwa da addinin musulunci da suka fi Shi'a kafirta musulmi da halatta jininsu da dukiyoyinsu.
A gefe guda kuma babu wasu Jama'a da akidarsu da littafansu suke cike da ka'idoji da sharuddai na kafirtawa kamar Ahlussunnah.
Amma yaya zaka yi da jahilin da bai san shi jahili ba ne, ko kuma mai son zuciyar da ya biye mata.
Allah ka raya mu a kan Sunnah, ka kashe mu muna Sunnah, ka tashe mu cikin Ahlussunnah.

No comments:

Post a Comment