Friday 21 October 2016

BA TILASTA MATA AKAYI BA TA MUSULUNTA (Sheik Yakubu Musa Katsina)


BA TILASTA MATA AKAYI BA TA MUSULUNTA 

(Sheik Yakubu Musa Katsina)


Maqaryaciyar jarida PUNCH wanda ta ruwaito labarin
A yunkurin kungiyar kiristoci ta kasa reshen Jihar Katsina na muzanta wata yarinya wadda ta musulunta mai suna Habiba Isiyaku, (Yar garin wawar kaza dake karamar hukumar Kankara) kungiyar ta dau nauyin wata jarida mai suna PUNCH don ta yi cin mutunci ga Martaba Sarkin Katsina Alh. Abdulmumini Kabir Usman ta hanyar zargin Sarkin da saida yarinyar, a wata ruwayar kuma cewa shi da kansa Sarkin ne ya aure ta. 

            A ranar Talatar da ta gabata ne (17/10/2016) Sheik Yakubu Musa Katsina ya zanta da manema labarai inda ya yi masu karin haske akan lamarin.
Takardar asibitin ce da CAN ta yo, an sanya an haife ta 2001
Shehin malamin ya bayyana cewa yarinyar ba tilasta mata akai ba ta musulunta ita da kanta da ganin damarta ta Musulunta, kuma ba a fadar Mai Martaba Sarki ta musulunta ba a cen garinsu wajen limamin garinsu ne ta  musulunta. Don haka, me ye na yarfe ga sarki da kuma jagororin Muslunci a cikin lamarin?.
Ku duba suna Habiba Isiyaku

Malam ya kara da cewa ba a san shuwagannin Addini da yarfe da sharri ba amman sai ga shi CAN ta yi wannan mumunan yarfe inda Sakataran CAN na karamar hukumar Malumfashi Musa Bahago ya canza wa 
Certificate  din ta ya gwada a 1999 a haife ta
Habiba Isyaku takardun haihuwa. Ya yi amfani da damarsa na Principal a makarantar da yarinyar take ya canza mata takardun haihuwa da Certificate din ta na kamala makaranta (Correction fluid ya sa ya
 An goge wajan shekara an sa wani
goge sai ya sake rubutawa da biro) . Amman cikin ikon Allah asirin Musa Bahago ya tonu bisa kokarin wasu ‘Yan Hisba na yankin inda su ka bi diddigin takardun yarinyar su ka gano irin canje-canje da wannan Principal ya yi duk saboda a


anan  za ku ga 1999 ne aka haife ta

muzanta Mai Martaba Sarki da kuma addinin Musulunci. Yarinya ce mai shekaru 18 amma  su (CAN) suka je wani asibiti a ka maida mata shekaru 14 don su ji dadin cin mutuncin Muslunci da cewa an aurar da karamar yarinya.




M. A. Ashafa
Malam Abubakar Ashafa (Shugaban Kwamitin Musuluntarwa na Jihar Katsina) ya bayyana mana irin yadda shugaban CAN na jihar Katsina ya nemi su je wajen Sarki domin bada hakuri akan abun da ya ji an ce an buga a jaridar PUNCH, amma da su ka je wajan Sarki sai ya bige da suka ga Sarki da cewa ana aurar da kananan yara, ana kaza da kaza. Anan take Martaba Sa’in Katsina ya ba shi amsa kamar haka “Ita wannan yarinya yanzu Musulma ce, kuma Musulunci ne zai yi hukunci a kanta. Kuma yarinyar da ta kai shekara 9 ko ta fara al’ada to ba mai hukunta ta sai Musulunci”. Daga karshe Malam Ashafa ya bayyana irin yadda su ke kokarin ba yara kanana hakkin su in sun Musulunta ta hanyar ba su zabin wajen zama, karshe yaran su za bi zama a hannun Musulmai, saboda irin muzgunawar da su ke fuskanta in sun koma wajen iyayensu kiristoci.

Daga karshe muna kira da babbar murya ga Hukumar Ilimi da gwamnatin Jihar Katsina su dau mataki ga Musa Bahago Principal kan wannan kulla-kulla da yayi na canza takardun makarantar Habiba. Haka kuma muna kira ga kungiyar CAN da ta shiga taitayinta ta daina yin katsalandan a harkar addininn wadansu.




No comments:

Post a Comment