Friday 7 October 2016

Haramta addinin Shi'a a Jahar Kaduna

*GWAMNATIN KADUNA TA SHARE HAWAYEN TALAKAWA, TA HARAMTA ADDININ SHI'A WANDA ZAKZAKIY YA KAWO NIGERIA.*

Rubutawa: *_Sheikh Baban Hamdan, Hafizahullah Ta'ala_*

A jiya ne majalisar zartarwa ta jihar Kaduna qarqashin gwamna Mallam Muhammad Nasiruddin el-Rufa'i ta haramta duk wani kai komo da sunan addinin shi'a wanda aka fi sani da Islamic Movement of Nigeria (IMN) ko Harkar Musulunci a Nigeria (Harka) wacce Zakzakiy ya kafa ba bisa qa'ida ba. Shafin BBC ya ruwaito daurin shekaru 7 ris ga duk wanda ya yi taurin kai.

Sanarwar ta zo a kan gaba, domin a yanzu haka rahotannin da suke shigo mana su ne 'yan shi'a na gagarumin shirin tada hargitsi a 'yan kwanakin nan na Ashura. Yanzu ba za mu yi wannan maganar ba tunda ga doka an yi, dama rashin doka ne ya sa muke nusar da hukuma idan mun jiwo labari, amma duk da haka ba shiru za mu yi ba.

Abubuwan lura:

1. Dole mabiya Zakzakiy ku hankalta, domin ba wata hakuma a duniya da za ta lamunci raini da cin kashin da kuke yi a qasar nan. Kun tsokano sojoji da rigima; kuka jefe su suka maida martani ba ku ji da dadi ba, ba ku yi hankali ba, kuke ganin ba a isa a lanqwasa ku ba, kuka ci gaba har kuka tabo Buratai shi ma ya taba ku.

Ba ku hankalta ba, kuka riqa zagin Buratai har da ma gwamna el-Rufa'in gaba daya. Ku na ta zanga-zanga kullum kuna artabu da jami'an tsaro, kuna cewa ku ba wanda ya isa ya hana ku wannan addinin da kuke yi; kuma ba addini bane, shirme ne.

To yanzu ga doka, wallahi kar ku ce za ku ja da hukuma, kawai ku durqusa ku tuba ku yi biyayya a qyale ku, ku zauna lafiya, amma in kuka yi girman kai, to ba a wa gwamnati haka, kuma sai ta ga bayan ku!

2. Ku tsaya ku sake karatu; duk 'yan Nigeria ba a tausaya muku, wannan ya gwada muku ba a kan daidai kuke ba. To ku sake nazarari, ko ba za ku karbi kalama ba (kalmar gaskiya) to ku daina zagin sahabbai da alaye, takamaimai Abubakar, Umar, Usman, Aliy, Amirul Muminina Mu'awiya, Abbas dan AbdulMuddalib da A'isha da Hafsa da Khadija da Hindatu mahaifiyar Amirul Muminina Mu'awiya, da sauran duk sahabbai da iyalan Manzo SAW.

Zage-zagen nan ne fa babban abin da ya jawo muku baqin jini kowa ya tsangwame ku har kuke boye kawunan ku.

3. Doka ta yi (ina ma a qara da aikin qarfi ba iya dauri ba), amma kar a manta matsalar tsaro ba ta jihar Kaduna bace kadai, kuma ba iya Kaduna ne ake da tsagerun 'yan shi'a ba, suna nan a wasu jihohin, don haka ya kamata gwamnatin tarayya ta hanzarta daukan matakan daqile shi'anci a Nigeria ciki har da wannan da Jihar Kaduna ta dabbaqa din.

4. Gwamnatin Kaduna ta sanar da sufeto janar na 'yansanda a rubuce, shi kuma ya sanar da rundunonin 'yansanda na jihohi a kan lokaci, ta yadda da an ga mutanen da ba a yarda da su ba sun taru ko sun kama hanyar Jihar Kaduna kawai a bincike su, in su ne a kama su, in ba haka ba za su aikata barnar da ake gudu.

5. Gwamnati ta sani, kamar yadda ba iya Jihar Kaduna ke fuskantar wannan matsalar ba, haka kuma ba iya qarqashin Harka 'yan shi'a ke wa zaman lafiyar qasa zagon qasa ba, duk dan shi'a wakilin Iran ne, wannan kuma ba surru bane ba kuma dan shi'ar da yake musun haka.

Don haka kar a ji nauyin magance matsala tun tana qarama, in ba haka ba, kamar yadda a baya a ka yi sakaci Zakzakiy ya zama jan wuya qafin Buratai ya take wuyan nasa, haka suma nan gaba za su yi illar da gara ma ta Zakzakiy da Boko Haram, amma in aka rufe ido aka yo komi da komi to shi kenan an huta da matsalar tsaro, sai dai a fuskanci wata kuma.

Allah Ya taimaki mai girma Gov Nasiru el-Rufa'i, Allah Ya taimaki qasar mu Ya tsare mana zaman lafiyar mu.

Daga: *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*

No comments:

Post a Comment