Friday 14 October 2016

IN DEFENCE OF THE SAHABA By Muhd Qaddam Sidq

http://www.dailytrust.com.ng/news/opinion/in-defence-of-the-sahaba/166730.html

Thursday 13 October 2016

MALAMI DA DALIBINSA

*MALAMI DA DALIBINSA*

DALIBI:  Ya Sayyadi wace irin falala zamu samu Idan mu ka tada hatsaniya a cikin garuruwan mu Amman da sunan Muzaharar Ashura
MALAMI: Ai kuwa kuna da lada sosai ashe ba ku ganin yadda aka zubar da jinin Imam Husain
DALIBI: To MALAM shi Imam Husain ance mutanen Kufa ne su ka yaudare shi sukai ta kiransa yazo za su yi mai Mubaya'a karshe ya fito su ka sumbule su ka bari aka kashe shi.
MALAMI: Tabbas muna da ruwayoyi irin haka
DALIBI: Ko shi yasa na ga kamar da ruwayoyin su Sayyid da ku Amirai ku ke aiki
MALAMI: Ban gane ba
DALIBI: Eh to ai na ga mu Mabiya kullum mu ake kashewa ku kuma kullum sai dai ku ce mana za mu dau fansa za mu ga bayan Azzalumai,   kuma sai ku   yi ta ingaza mu ku na labewa
MALAMI: Wannan Ai tunanin Wahhabiyawa ne

DALIBI: Madalla da tunanin da bai jefa mabiyansa halaka ba
MALAMI: To mu dai soyayyar mu Husain ta sa mu ke haka
DALIBI: Amman Malam ka karata mana a Tafsirin Suratul Bakara cewa Allah ya ce " Kar ku jefa kan ku ga halaka" to Wannan ai shi ne misalin jefa kai ga halaka
MALAMI: An ya ba ka tasirantu da Wahabiyawan Fcbk ba don na ga kwanan husuma kawai kake nema
DALIBI: Haba Malam da ga na fadi gaskiya ni duk inda gaskiya ta ke ina nan
MALAMI: To ai kuwa sai dai in ka bar tunani irin na wahabiyawa, ka ga ai murna su ke gwamnati ta hana mu addinin mu
DALIBI: Yo MALAM an hana mu Yin Sallah ne ko wani rukuni daga rukunan Musulunci?
MALAMI: Mu fa addinin mu yana tafiya ne da a bisa tsarin bin maraji'anci don haka muna yin bukukuwa Wanda ba wanda ya isa ya hana mu
DALIBI: Ko da ya saba ma dokar kasa Malam
MALAMI.: Mu fa ba wata hukuma sai ta Allah
DALIBI: Ai da Wannan ku ka rude mu Amman mun gani har Iran ba hukumar Allah su ke big ba don su ma suna da tsarin mulkin su Wanda ba na Allah ba
MALAMI: Yanzun dai mu jajanta ma Juna kan Wannan zalunci da akai mana
DALIBI: Ai ni sai dai a taya ni murna ta barin Wannan tafiyar ta rashin sanin kimar Mabiya  (Shi'a)

Wednesday 12 October 2016

GAYYATA TARON BADA KYAUTUKAN MUSABAQA DA KACICI-KACICI

FITYAH CENTER FOR DA'AWAH & EDUCATION
KATSINA GAYYATA TARON BADA KYAUTUKA DA
WA'AZI
A madadin jagoran wannan cibiya mai albarka
(Dr. Muhammad Muslim Ibrahim) ina mai farin
cikin gayyatar ku taron bada kyaututtuka kamar
haka
 Kyautuka ga daliban da su ka yi fice a Bita
(Samina)
 Kyautuka ga daliban da su kai zarra a
musabaqar Alqur’ani mai girma
 Kyautuka ga makaratun da su kai fice a
kacici-kacicin iyalai/sahabban Annabi (S.A.W)
 Kyautukan Laptop, Wayar hannu, Digital Qur’an
ga wadanda su ka ci nasara a gasar Al-Wal-
Ashab Wadda kasar Saudia ta ke gabatarwa duk
shekara.
 Kyautukan karramawa ga wadanda su kai fice
wajen bada gudummuwa.
Za’a gudanar da wannan taro kamar haka
Wuri: Masallacin Juma’a na Abu Huraira B/Head
Quarter Yan Sanda Katsina.
Lokaci: da misalin karfe 4:00 na yamma
Rana: Juma’a 13/1/1438H 14 Oct 2016.
WA'AZI
NA MATA
Gobe Alhamis 14/10/16. A dakin taro na Social
Dev. Filin Samji Katsina da Karfe 4:00PM
NA MAZA
Ranar Juma'a Bayan Sallar Isha''i a masallacin
Lantarkin Malm Mudi
Allah ya bada ikon halarta
Hassan Kabir Yar’adua
Magatakarda

Monday 10 October 2016

#ACE TO KATSINA DAGA SHI'A#

Bashir Yahuza Malumfashi
--- # Shia : Kira Na Musamman ga # GwamnaMasari
---
***
+Tare da gaisuwar ban girma ga
# GwamnaAminuBelloMasari na # JiharKatsina
nake kira da cewa ya dubi Allah, ya ceto
al'ummar Jihar Katsina daga tsageranci da
shedancin 'yan Shi'a a jihar, ta hanyar haramta
muggan ayyukansu a jihar, kamar yadda
Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi a makon nan.
*
+Babu shakka, idan ba a dauki irin wannan
mataki ba, yanzu za su maido da tsagerancinsu
kacokan ga Jihar Katsina, domin ta fi kusa da
Kaduna.
*
+Daukar wannan mataki yana da muhimmanci,
ganin cewa kwanan nan za su fara zanga-zangar
Ashura, balle kuma an hana su haka a Kaduna.
Haka kuma idan ba a dakile su ba, akwai
yiwuwar a samu tashin hankali tsakaninsu da
al'umma domin kuwa suna cin zarafin
shugabanni, suna zagin sahabban manzon Allah
(saw) da iyalinsa. Sauran al'umma kuwa ba za
su zura ido su lamunci tozarta Manzon Allah da
iyalansa da sahabbansa ba.
*
+MUNA ROKON A HARAMTA DANYEN AIKIN
'YAN SHI'A AJIHAR KATSINA DOMIN TABBATAR
DA ZAMAN LAFIYA DA KWANCIYAR HANKALI A
JIHAR.
***
--- # ACETOKATSINA---

Friday 7 October 2016

Haramta addinin Shi'a a Jahar Kaduna

*GWAMNATIN KADUNA TA SHARE HAWAYEN TALAKAWA, TA HARAMTA ADDININ SHI'A WANDA ZAKZAKIY YA KAWO NIGERIA.*

Rubutawa: *_Sheikh Baban Hamdan, Hafizahullah Ta'ala_*

A jiya ne majalisar zartarwa ta jihar Kaduna qarqashin gwamna Mallam Muhammad Nasiruddin el-Rufa'i ta haramta duk wani kai komo da sunan addinin shi'a wanda aka fi sani da Islamic Movement of Nigeria (IMN) ko Harkar Musulunci a Nigeria (Harka) wacce Zakzakiy ya kafa ba bisa qa'ida ba. Shafin BBC ya ruwaito daurin shekaru 7 ris ga duk wanda ya yi taurin kai.

Sanarwar ta zo a kan gaba, domin a yanzu haka rahotannin da suke shigo mana su ne 'yan shi'a na gagarumin shirin tada hargitsi a 'yan kwanakin nan na Ashura. Yanzu ba za mu yi wannan maganar ba tunda ga doka an yi, dama rashin doka ne ya sa muke nusar da hukuma idan mun jiwo labari, amma duk da haka ba shiru za mu yi ba.

Abubuwan lura:

1. Dole mabiya Zakzakiy ku hankalta, domin ba wata hakuma a duniya da za ta lamunci raini da cin kashin da kuke yi a qasar nan. Kun tsokano sojoji da rigima; kuka jefe su suka maida martani ba ku ji da dadi ba, ba ku yi hankali ba, kuke ganin ba a isa a lanqwasa ku ba, kuka ci gaba har kuka tabo Buratai shi ma ya taba ku.

Ba ku hankalta ba, kuka riqa zagin Buratai har da ma gwamna el-Rufa'in gaba daya. Ku na ta zanga-zanga kullum kuna artabu da jami'an tsaro, kuna cewa ku ba wanda ya isa ya hana ku wannan addinin da kuke yi; kuma ba addini bane, shirme ne.

To yanzu ga doka, wallahi kar ku ce za ku ja da hukuma, kawai ku durqusa ku tuba ku yi biyayya a qyale ku, ku zauna lafiya, amma in kuka yi girman kai, to ba a wa gwamnati haka, kuma sai ta ga bayan ku!

2. Ku tsaya ku sake karatu; duk 'yan Nigeria ba a tausaya muku, wannan ya gwada muku ba a kan daidai kuke ba. To ku sake nazarari, ko ba za ku karbi kalama ba (kalmar gaskiya) to ku daina zagin sahabbai da alaye, takamaimai Abubakar, Umar, Usman, Aliy, Amirul Muminina Mu'awiya, Abbas dan AbdulMuddalib da A'isha da Hafsa da Khadija da Hindatu mahaifiyar Amirul Muminina Mu'awiya, da sauran duk sahabbai da iyalan Manzo SAW.

Zage-zagen nan ne fa babban abin da ya jawo muku baqin jini kowa ya tsangwame ku har kuke boye kawunan ku.

3. Doka ta yi (ina ma a qara da aikin qarfi ba iya dauri ba), amma kar a manta matsalar tsaro ba ta jihar Kaduna bace kadai, kuma ba iya Kaduna ne ake da tsagerun 'yan shi'a ba, suna nan a wasu jihohin, don haka ya kamata gwamnatin tarayya ta hanzarta daukan matakan daqile shi'anci a Nigeria ciki har da wannan da Jihar Kaduna ta dabbaqa din.

4. Gwamnatin Kaduna ta sanar da sufeto janar na 'yansanda a rubuce, shi kuma ya sanar da rundunonin 'yansanda na jihohi a kan lokaci, ta yadda da an ga mutanen da ba a yarda da su ba sun taru ko sun kama hanyar Jihar Kaduna kawai a bincike su, in su ne a kama su, in ba haka ba za su aikata barnar da ake gudu.

5. Gwamnati ta sani, kamar yadda ba iya Jihar Kaduna ke fuskantar wannan matsalar ba, haka kuma ba iya qarqashin Harka 'yan shi'a ke wa zaman lafiyar qasa zagon qasa ba, duk dan shi'a wakilin Iran ne, wannan kuma ba surru bane ba kuma dan shi'ar da yake musun haka.

Don haka kar a ji nauyin magance matsala tun tana qarama, in ba haka ba, kamar yadda a baya a ka yi sakaci Zakzakiy ya zama jan wuya qafin Buratai ya take wuyan nasa, haka suma nan gaba za su yi illar da gara ma ta Zakzakiy da Boko Haram, amma in aka rufe ido aka yo komi da komi to shi kenan an huta da matsalar tsaro, sai dai a fuskanci wata kuma.

Allah Ya taimaki mai girma Gov Nasiru el-Rufa'i, Allah Ya taimaki qasar mu Ya tsare mana zaman lafiyar mu.

Daga: *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*

Monday 3 October 2016

Amfani da Kalandar Miladiyya a Saudia

Daga Shehin Musulunci a fcbk
Mal Baban Hamnda

Amfani da Kalandar Miladiyya a Saudia.

Dan shi'a ne ya yi qarfin halin yi min inbox, wai tun a sunanta ma ita qasar larabawa ce ba ta Musulunci ba, ga shi yau ta koma kalandar bature, don haka Iran ce qasar Musulunci tun daga sunanta ma.

Na so ba inbox yayi ba don kar ya musanta ya muka yi da shi, ko ya ce na sauya magana, ko mun yi abu a surru na tona, etc.

To dama dai an sani sarai Saudia zata yi anfani da watan miladiyya ne kawai wajen biyan albashi sabo da matsalar tattalin arziqi. Wannan matsalar an fara ta a manyan qasashen duniya tun kusan shekara 10 baya. Don haka Saudia ta ciri tuta da ta kawo yanzu ko gezau bata yi ba.

Abin sani a nan shi ne, anfani da kalandar hijira tana wajaba ne kawai a ayyuka na ibada, a sauran lamurra Ba wajibi bane. Tun kusan shekaru 10 baya aka yi wa malamai fatawa:

ماحكم استعمال التقويم الميلادي بدلا من الهجري لأسباب كثيرة منها دقة الميلادي في تحديد الأيام ؟

'Ina hukuncin anfani da kalandar Miladiyya a bar ta Hijiriyya sabo da dalilai da yawa, kamar takamaiman yawan raneku dake kalandar Miladiyya?'

Malamai sun kawo nassoshi da maganganun magabata kan wajabcin anfani da kalandar hijiriyya a ayyukan ibada, a sauran abubuwa suka ce:

فالأولى استعمال التقويم الهجري ويمكن أن تقارنه بالتقويم الميلادي

'abin da yafi ko dai a yi anfani da iya kalandar Hijriyya ko kuma a hada ta da Miladiyya'

وأما الاقتصار على الميلادي فيخشى عليه أن يكون فيه عدول عن التوقيت الذي جعله الله للناس مع اتباع الغير في شأنه.

'amma idan aka taqaita a iya Miladiyya to ana tsoron kar a watsar da tsarin lokacin da Allah Ya halastawa mutane shi a bi waninsa"

ثم إنه ليس عندنا نص يفيد منعه ولكن الأولى الالتزام بالتاريخ المعروف عند المسلمين المنصوص في القرآن والسنة

'duk da cewa yin anfani da kalandar da Musulmi suka fi sani, wadanda sune a aka anbace su a Qur'ani da Sunnah, shi ne ya fi, ba mu da dalilin cewa (yin anfani da kalandar miladiyya kadai) laifi ne'

Fatawa mai lamba 106346 ta ranar Alhamis 20 Rabi'ul Auwal 1429 (27/03/2008) a islamweb.

Za a a lura daga fatawar malamai:

1. Dayan biyu duk wanda aka yi dace; ko dai anfani da kalandar Hijriy ita kadai ko kuma a gwama ta da ta Miladiyya; ko su ma a kwanan watan fatawar gwama biyun suka yi.

2. Taqaituwa a kalandar Miladiyya a abubuwan da ba na ibada ba, ba laifi bane sam sam sam.

Kenan, ba wani abu da za a ce a haqiqa ya sauya a Saudiyya domin ta gwama biyun ne, kuma dama can tana anfani da duka biyun a wasu abubuwan, kawai ta shigar da albashi ne yanzu a jerin wadanda Miladiyya za ta shafa. Amma ba wai ta sauya daga Hijriyya zuwa Miladiyya bane ko kadan.

In ma kuma da duk abubuwan da ba na ibada ba, dukan su, za ta taqaita a iya Miladiyya da bata sabawa Allah ba ko kusa, kenan ba wanda yake da haqqin tuhuma ko yi wa Saudiyya kallon banza.

Iran: na san zai yi wahala dan shi'ar ya iya futowa gaban jama'a ya tada wannan maganar, domin tambayar da na masa ta gigita shi ita ce 'in ka tuhumi Saudiyya, ko zaka iya fada min da wace kalanda ake anfani a Iran?'

Duk duniya ba dan shi'ar da zai iya tsayawa ya tunkare ka da wannan maganar, domin a Iran ba wai iya ayyukan mu'a'maloli ba, hatta na ibadar ma ba da kalandar Musulunci suke anfani ba, da kalandar majusancin su suke anfani.

Kuma ba za su iya kare kan su a kan wannan ba.

To yanzu don Allah in banda dan shi'a bakin Ibnu Taimiyya ya kama shi, ta yaya me wannan zai qalubalanci Saudiyya?

Don haka dai Saudiyya bata aikata ko makruhi ba balle zunubi balle a sami damar batanci gare ta.

Allah Ya nuna mana gaskiya Ya bamu ikon bin ta. Allah Ya taimaki Shugabannin Qasa mai Tsarki Ya kare su daga sharrin maqiya da wawaye.