Saturday, 29 October 2016
Friday, 28 October 2016
WA'AZIN WALIMAR AURE
WA'AZI DA WALIMAR AURE NA GIDAN SHEIK HABIBU YAHYA KAURA
DAGA CIKIN MALAMAI
1. Sheik Abdullahi Bala Lau
2. Sheik Kabir Gombe
idan Allah ya kai mu gobe Katsinawa za su sha WA'AZI daga Manyan Malamai na Jibwis ta kasa
Wa'azin zai gudana gobe ASABAR 29/10/16 a Masalacin Kerau, Bayan Sallar Isha'i.
Mai masaukin Baki Sheik Yakubu Musa Katsina
Thursday, 27 October 2016
DON MATASA
SHIRIN DON MATASA
DA'AWAH FAMILY SUPPORT ASSOCIATION
Na farin cikin gayyatar matasa Maza/Mata zuwa shiri na musamman da ta shirya kamar haka
A dakin taro na Social Dev, Filin Samji Katsinah, A gobe Juma'a 28/10/16 da misalin karfe 3:00 pm
*YA KU MATASA KAR KU BARI A BAKU LABARI*
MUNA MAKU MARABA
Wednesday, 26 October 2016
Na Ga ‘Mutuwa’ A Ranar Tunawa Da Shahadar Husaini (R.A) (3)
Dr. . Muhd Sani Rijiyar Lemo
Na Ga ‘Mutuwa’ A Ranar Tunawa Da Shahadar Husaini (R.A) (3)
Assalamu Alaikum,
A baya mun ji yadda Marubucinmu da abokan
tafiyarsa suka auka cikin wani kango wanda
waɗansu gungun mutane suke zaune cikinsa, ana
rera musu waƙe suna amshi. To mai ya faru
bayan shigarsu. As-Sheikh Ali at-Tantawi ya ci
gaba da cewa,
“Muka tsallaka sahu-sahu muka shiga. Jama’a na
zazzaune, duk sun yi shiru, kamar mutuwa ta
gitta, bayan da shi mawaƙin ya yi shiru, da alama
dai hutawa suke yi kafin su ci gaba.
Mun kutsa ciki ne har sai da muka isa sahun
farko inda mai bayar da waƙe yake bayarwa.
Yana zaune a kan kujera, a gefe da shi akwai
wasu ƙarin kujeru waɗanda babu kowa a kansu,
sai aka ba mu muka zauna. Ba da jimawa ba aka
ci gaba da rera waƙe. Duk sa’adda mawaƙin ya
rera wasu baitoci sai ya ɗan dakata kaɗan, can
sai ka ga su kuma sauran jama’ar sun ɗaga
hannuwansu sama sun tattake sun bugi ƙirajesu
da su, ji kake wani jib!! kamar katangar wannan
kango tana motsawa saboda ƙarar wannan bugun
ƙirji da suka yi. Sannan ya sake rera wasu
baitocin, su kuma su sake jibga hannuwansu a
kan ƙirajensu, har sai da ƙirajensu suka yi ja jawur
saboda tsananin duka, gumi ya jiƙa su sharkaf.
Kowa a cikinsu yana cike da baƙin-ciki da jimami
na abin da aka yi wa Husaini (R.A), zuciyarsa
kuma ta cika da gaba da ƙiyayya ga Banu
Umayya da mutanen Sham, waɗanda wannan
waƙen ya ɗorawa alhakin jinin Husaini (R.A).
Ana tsakar haka ne, sai kawai ɗaya daga cikin
ɗaliban da muke tare da su, allurar kirkinsa ta
motsa, sai ya mike tsaye wai zai gabatar da ni a
wajen wannan mawaƙi don ya nuna masa irin
ƙaunarsa gare ni, tare da fada masa girman
matsayina da martaba ta a gurinsu. Sai jin shi na
yi yana faɗawa maƙin nan cewa, ‘Wannan babban
malaminmu ne, kuma mutumin ƙasar Sham ne,
sannan kuma babban marubuci ne, ya yi wallafe-
wallafe dadama, a cikin littattafansa da akwai
littafinsa ma mai suna ‘Abubakar As-Siddiq’, da
kuma wani mai suna ‘Umar bn Alkhattab’, da …
da…” ya ci gaba da lissafa su. Ina!! Ai ban gama
jin ƙarshen maganarsa ba, sai kawai na shiga yin
kalmar shahada, don ta zama mini ita ce ƙarshen
maganata a zamana na duniya.
Ban sake fahimtar abin da wannan ɗalibi nawa
yake faɗa wa wannan mawaƙi ba, domin zuciyata
tini ta ɓallo ta faɗo ƙasan cikina, kamar yadda
kasan irin yadda ‘lifter’ take faɗowa daga dogon
bene yayin da sarƙoƙin dake ɗauke da ita suka
tsinke. Kawai ni a lokcin na saddaƙar mutuwa zan
yi. Na juya ina ta dube-dube ko zan ga maguda,
amma ina! Wuri ya cika maƙil, ga katanga ta
kewaye ko ina, babu mafita sai wannan ƙofar
ɗaya da muka shigo daga gare ta, tsakanina ko
da ita ban da waɗannan mutane masu kirji a
waje ba abin da nake gani. Sannan me kake
zaton zai faru idan mutanen nan suka gane
cewa, ni mutumin Sham ne?! Kuma ni ne
mawallafin littfin tarihin Abubakar da Umar?! Ta
yaya zan yi in tabbatar musu cewa, babu
hannuna a cikin kashe Husaini?! Kuma babu
hannun kakanni na a ciki, saboda su ‘yan asalin
ƙasar Masar ne, ba mutanen Sham ba ne?! Don
haka su fahimci babu hannuwansu a kashe
Husaini. Wai ma tukunna ma za su ba ni damar
in kare kaina ne har da zan musu wannan
bayanin? Kuma ma idan na yi ƙokarin kare kaina,
kuna ga ma za su yarda da ni ne har su gaskata
ni?!
Daga nan kawai na sakankance na gama yawo,
yau sai buzuna, abin da ya rage mini shi ne in ci
gaba da yin addu’a a asirce, idan na zo mutuwa
in yi mutuwa mai sauƙi, amma babu maganar
kubuta.
Shi kuma abokina Anwar fa, mai yake ciki, domin
shi ne ya shigar da mu wannan matsalar. Da na
saci kallosa sai na ga kamanninsa sun canza,
launinsa ya canza kala, ya koma ruwan kalar
lemon tsami. Na kalli fuskar Sayyid mai koren
rawani ko zan fahimci matakin da yake shirin
ɗauka a kain, sai ban fahimci komai daga
wajensa ba, na dai bar al’amarina a wajen Allah.
Muka ɗauki tsawon awanni saba’in a jere cikin
wannan hali na fargaba da firgici da tsoro, babu
wani abu da ya canza. Duk wani minti ɗaya
matsayin awa ɗaya nake ganinsa. Aka ci gaba da
waƙe har aka kai ƙarshe. Can sai na kula mutane
su fara shirin fita, don na ga suna ta ɗauko
rigunansu suna mayarwa jikinsu. To daga nan ne
na fahimci matsalata dai ta zo ƙarshe, hankalina
ya fara dawo wa jikina. Na dubi agogona sai na
ga ashe ba awanni saba’in muka yi ba, mintina
ashirin ne kachal. Tsabar dai tsananin firgicewa
ne kawai ya sanya na ga tsawon lokacin. Daga
nan na yi bankwana da ‘Sayyid’ na nufi ƙofa na
fita. Na ji ni kamar na mutu na dawo Duniya.
Muka kwana biyu a Hillah. Da muka sake haɗuwa
da ‘Sayyid’ muka tattauna, sai na fahimci shi ba
mai tsattsauran ra’ayi ne ba, (ko kuma dai taƙiyya
ya yi min). Sai nake tuna masa abin da ya faru,
sai ya ce, “Ka godewa Allah da ya kuɓutar da
kai, kuma bai bar wannan jama’a sun ji abin da
wannan ɗalibi naka ya fada ba”. Sai na ce, “Ashe
kai ba za ka kare ni ba idan sun so auka min?
Sai ya yi dariya ya ce, “Idan na kare ka, ni kuma
wanene zai kare ni?! Wallahi ba wata kariya da
zan ba ka, zan ƙale ka da su, ka fuskanci
makomarka!’…”.
Wannan shi ne yadda babban marubucinmu
Sheikh Ali At-Tantawi ya tsallake rijiya da baya,
yayin da ya tsinci kansa a tsakiyar ƙatti madaka-
ƙiraza, a Husainiyya ta garin Hilla cikin Ƙasar Iraƙi.
Ya rubuta wannan labari na shi a cikin littafinsa
mai suna ‘Az-Zikrayāt’, juzu’i na 3, shafi na
379-388. Allah ka ganar da su gaskiya. Amin
Tuesday, 25 October 2016
Na Ga ‘Mutuwa’ A Ranar Tunawa Da Shahad Husaini (R.A) (2)
Na Ga ‘Mutuwa’ A Ranar Tunawa Da Shahada Husaini (R.A) (2)
![]() |
Dr.Muhd Sani R/Lemu |
muku alkawari a baya cewa, zan tsakuro muku
wani abu mai kama da taɓa-ka-lashe daga
cikin rubutun babban marubucin nan Ash-
Sheikh Ali at-Tantawi da ya rubuta ƙarkashin
waccen matashiya ta sama, a littafinsa mai
suna “Az-Zikrayaat” wato ‘Tuna Baya’. Ka da
ku manta na faɗa muku cewa, ba zan iya kawo
rubutunsa yadda yake ba, cike da fasaharsa da
taswirarsa, sai dai in kwatanta, domin an ce,
‘linzami ya fi ƙarfin bakin kaza’.
Malam dai ɗan asalin ƙasar Syria ne, amma ya
yi zaman karatu a Masar, sannan ya koyar a
Iraƙi, ya ziyarci wasu ƙasashe dadama, daga
ƙarshe ya yada zango a ƙasar Saudiya, a nan
Allah ya yi masa rasuwa a shekarar (1999
A.D). A zamansa a Bagadaza ta ƙasar Iraƙi ya
fita wata rana inda ya ga ‘mutuwa’ amma Allah
ya kuɓutar da shi, daga baya ya yi rubutu a
kan wannan labari, inda yake cewa,
“Ranar Ashura a Iraƙi wata rana ce ta daban.
Duk garin yakan koma tamkar ana zaman
makoki, kai ka ce, jiya-jiyan nan ne aka kashe
Husaini (r), ko kuma ka ce har yanzu Banu
Umayya ne ke rike da ragamar mulki; ko kuma
wadanda aka kashe Sayyidina Husaini (r) tare
da su, su ne a kan kujerar mulki. Mutane sun
manta da cewa, Duniyar fa ta canza, wasu
ƙasashe sun gushe, wasu kuma sun kafu,
komai a doron ƙasa ya canza akan yadda da
yake, kaɗai al’adar waɗannan mutane ne ita ce
ba ta canza ba har yanzu, jiya-a-yau.
Mu Musulmi duka muna son Annabi (S.A.W),
duk wanda ma ba ya son shi fiye da yadda
yake son kansa to imaninsa bai cika ba. Kuma
muna son duk mai son Manzon Allah (S.A.W).
Kuma jikokinsa Hasan da Husaini suna son shi,
don haka mu ma muna sonsu, muna son iyalan
gidan Manzon Allah duka, don haka ne ma
muke sa su a cikin salatin da muke yi wa
Annabi (S.A.W). Amma duk da haka ba za mu
taɓa yarda mu aikata abin da Annabi bai yi
umarni da aikata shi ba, don kuwa ba za mu
saɓa masa ba mu riƙa yin gaban-kanmu. Abin
da muka ga wasu mutane a Iraƙi suna yi ya
saɓawa koyarwar Annabi (S.A.W) kuma ba zai
taɓa amincewa da haka ba.
A wannan rana ta Ashura Abokina Anwar ya
buƙaci mu tafi garin Hillah (yanki ne na ‘yan
shi’a a Iraƙi) yawon buɗe ido. Sai na yarda.
Kuma muka nemi wasu ɗalibanmu su uku su yi
mana rakiya. A cikinsu akwai wani basamuden
ɗalibi, idan na tsaya kusa da shi dakyar kaina
yakan gota kwankwasonsa kaɗan, wani lokaci
ma nakan tsokane shi in ce masa, wai kai ba
ka gamuwa da matsalar iskar shaƙa (Oxygen) a
sararin samaniya idan kana tsaye?!. Amma
kuma duk da haka yaro ne mai kirki, mai
kyawawan halaye, sunanshi Abdullahi Adi. Ka ji
sunan shi ma ‘Adi’ kamar sauron ɓurɓushin
Adawa mutanen Annabi Hudu. (A.S). Sauran
ɗaliban guda biyu, ɗayansu ɗan Sunna ne,
gudan kuma ɗan Shi’a ne.
Kashe Sayyidana Husaini wata mummunar
aika-aika ce, e, zan sake maimaitawa,
mummunar aika-aika ce, a fahimci hakan da
kyau. To fa amma da jimawa wasu mawaƙa da
marubuta Adabin larabawa sun yi ta ƙarin
gishiri mai yawa a wajen bayanin wannan
‘aika-aika’ domin sun mayar da ita wani fage
na sukuwar dawakan adabinsu, da sakin
linzamin waƙoƙinsu. Lalle kam sun yi sukuwa
yadda suke so, to amma fa sun lullube gaskiyar
al’amarin da ƙurar sukuwar dawakansu.
Waƙi’ar kashe Husaini, waƙi’a ce da ta faru tun
shekaru masu yawa da suka wuce. Marubuta
iri-iri, kama daga marubutan tarihi da mawaƙa
da marubutan adabi da al’adu kowa ya yi ta
rubutu a kai, kuma kowa yana zana irin tashi
taswirar yadda waƙi’ar ta kasance. Kusan babu
wani labari mai sanya idanu su rika kwararo da
hawaye da ba a faɓa ba a kai. Duk wani abu
da yake nuna zalunci da rashin imani da
ƙeƙashewar zuciya, da nuna rashin mutunci da
tumasanci, duk sai da aka tattaro su aka zuba
su a cikin labarin wannan waƙi’a. Kai yau da a
ce Miyagun mutanen na da aka yi a tarihi irin
su, Nero ko Genghis khan, ko ma yahudawan
da suka fi su sharri a yau irin su Begin da
Shamir, su ne ake ba da labarin an yi musu irin
abin da masu ba da labarin waƙi’ar Karbala
suke faɗa, to babu shakka sai ka tausaya
musu idan ka ji, sai ka jajanta musu a kai. To
kuma balle a faɗa maka cewa, duk wannan
abu ya faru ne ga ‘ya ‘yan Nana Fatima, jikokin.
Ma’aiki (S.A.W) yaya za ka ji a ranka?!
Wannan shi ne zai sa ka fahimci dalilin da ya
sa muke ganin abin da ake yi a ranar Ashura
game da Husaini irin wanda ba a yi wa Ali ko
Mazon Allah kwatankwacinsa, alhali kuwa sun
fi shi daraja nesa ba kusa ba.
Muna tsakar yawo a garin Hillah ne, sai muka
gan mu a wani babban fili an zageye shi da
katanga, da ƙofar shiga guda ɗaya a buɗe.
Sannan muka ji wani sautin rera waƙe mai cike
da tausayi yana fitowa daga cikin wannan
kango. Muna leƙawa sai kawai mu ga wasu
mutane a ciki zaune babu komai na tufafi a
jikisu in banda abin da suka rufe al’aurarsu
zuwa cibiyoyinsu. Sun bar ƙirajensu tsirara a
waje. A tsakiyarsu sai muka hango wani zaune
sanye da koren rawani (alamar shi Sayyid ne
Ahlul Baiti). Wannan mutum shi ne mai ba da
waƙen, sauran jama’ar dake zagaye da shi
sahu-sahu suna masa amshi.
Daga nan sai abokina Anwar ya tambaye ni
cewa, ko za mu shiga wannan kangon ne? Sai
na ce mu tambayi waɗannan ɗaliban domin su
ne ‘yan gari, su suka fi mu sanin ƙasarsu. Sai
suka ce mana kada mu yarda mu shiga. Ai
kafin mu ankara shi gogan naka Anwar har ya
shige. Daga nan muma muka yanke shawarar
mu bi bayansa.
Mu kwana a nan, za mu ci gaba….
Monday, 24 October 2016
NA GA 'MUTUWA' A RANAR TUNAWA DA SHAHADAR HUSAINI (R.A) Fitowa ta 1
As-Sheikh Ali at-Tantawi kawarren marubuci ne a cikin harshen larabci. Malami ne kuma tsohon Alkali ne, sannan kuma masanin larabci ne. Ya yi rubuce-rubuce masu yawa a fannonin ilimi daban-daban, kamar Tarihi, da Tarbiyya, da Siyasa, da Adabin Larabawa, da zamantakewa da al’adu.Ni dai ina matukar sha’awar karanta rubuce-rubucensa, kuma ina jin dadinsu, saboda kasancewa Sheikh Ali wani marubuci ne mai salon rubutu na musamman. Salon maganarsa yana da matukar dadin karantawa, ga shi ya kware sosai wajen sarrafa harshen larabci. Ni dai ban taba ganin marubuci mai iya ba da kwatancen abubuwa ba kamar Sheikh at-Tantawi, gaskiya ya kware a wannan janibin, idan yana maka kwatance kamar me! Sannan baya ga haka at-Tantawi mutum ne mai barkwanci, idan ya yi wata maganar sai ka ga mai karatu shi kadai yana ta dariya ba tare da na kusa da shi ya san dalilin dariyarsa ba. Don haka yake nishadantar da mai karanta littafinsa, idan ya fara karanta littafinsa ba zai so ya bari ba.Ina cikin karanta littafinsa ne mai suna “Az-Zikraayat” wato kamar dai ka ce a Hausa ‘Tina Baya’ ko kuma ‘Diary’ da Turanci. Ina tsakiyar karatunsa ne sai kawai na ci karo da wani tubutunsa mai dauke da waccen matashiyar ta sama. Na so a ce duk masu karanta wannan rubutu nawa za su iya karanta wancan rubutu na Sheikh at-Tantawi daga littafin da na ambata a cikin madarar larabcinsa. Saboda a gaskiya ta Allah ba na zaton akwai wani harshe wanda ba na larabci ba da za a fassara wannan makala tashi da shi kuma ya yi daidai da yadda take da larabcinta, a wajen fasaharta da gwanintar sarrafa harshe dake tattare da shi, tare da abin da ta kunsa na fadakarwa da ilimantawa mai yawa.Amma duk da haka zan iya tsakuro wa masu karatu dan taba-ka-lashe daga wannan makala ta Malam at-Tantawi. Amma fa ku fahimta fasahata da fasahar yaren da zan yi fassarar da shi, ko kusa ba za a daidaita shi da fasahar Marubucinmu ba da ta yaren Laraci harshen Al-Kura’ni, kuma harshen Annabin tsira, Allah ya kara masa salati da sallama. Amma dai da babu gwamma babu dadi.Ku saurare ni ina nan tafe da tsakure Insha Allah. Allah ya sa mu dace.
KARATUN HAUZA DAGA MAJALISIN MAL BABAN HAMDAN
MAJALISI NA [ 1 ] na Sheikh Baban Hamdan
GAMUWA A KAN SAHIHIYAR AQIDA, SHINE RABA-GARDAMA A TSAKANIN MUTANE, SHINE HADIN KAN MUSULMI. SABANIN HAKA, HADIN-BAKI NE DA YAUDARAR JUNA.
MUTUM ZAI ZAMA MUSULMI NE KADAI, IDAN YA QUDURCI:
(1) BA ABIN BAUTA SAI ALLAH SHI KADAI, YA SHAIDA DA MANZANCIN ANNABI MUHAMMAD S.A.A.W.
(2) YA TSAIDA SALLAH
(3) YA AZUMCI WATAN RAMALANA
(4) YA BADA ZAKKA
(5) YAYI AIKIN HAJJI IDAN YA SAMI IKO.
IMANI, SAHIHIYAR AQIDA: SHAIKH SALIHUL FAUZAN, YACE:
وقد بقي النبي صلى الله عليه وسلم في مكة بعد البعثة ثلاثة عشر عامًا يدعو الناس إلى التوحيد، وإصلاح العقيدة؛ لأنها الأساسُ الذي يقوم عليه بناءُ الدين
"TUN DA AKA AIKO SHI, ANNABI S.A.W. YANA MAKKA SHEKARU 13 YANA KIRAN MUTANE ZUWA TAUHIDI DA GYARAN AQIDA, DOMIN ITACE ASASIN DA AKE GINA ADDINI AKAN TA"
A CIKIN LITTAFIN SA "AQIDATUT TAUHID" SHEHI YACE, SAHIHIYAR AQIDA ITACE:
الإيمان بالله وملائكته وكتبه ورسله واليوم الآخر، والإيمان بالقدر خيره وشره، وتُسمَّى هذه أركانُ الإيمان.
"IMANI DA ALLAH, DA MALA'IKUN SA, DA LITTAFAN SA, DA MANZANNIN SA, DA RANAR LAHIRA, IMANI DA QADDARA; AL-KHAIRI DA SHARRIN TA. WADANNAN SU AKE KIRA RUKUNAN IMANI"
'YAN SHI'A, WADANNAN SUNYI MUKU? IDAN SUNYI MUKU, TO KO A CIKIN DAREN NA MA, ZAMU FARA DA KALLON YADDA MUKA QUDURCI WADANNAN RUKUNNAI, TARE DA SANIN MADOGARAR MU AKAN AQIDUN NAMU.
IDAN KUNA DA ABIN DA BAKWA SO A CIKI, KO KU KARA, TO SAIKU LISSAFA SU, SAI SHIGA JERIN ABABEN DA ZAMU TATTAUNA AKAN SU, DOMIN KOWA YA SAN ABIN DA BAI SANI BA, GWARGWADON HALI, YA FAHIMCI ABIN DA BAI FAHIMTA BA.
ALLAH S.W.T. YACE:
واعتصموا بحبل الله جميعاً ولا تفرقوا
BISMILLAH...
MAJALISI NA [2] na Sheikh Baban Hamdan
RUKUNAN DA MUKA GAMU AKAN SU A MAJALISI NA [2], SUNA NAN A QUR'ANI. WANNAN NE; A GANI NA والله أعلم ; YA SA BA MUYI SABANIN WANDA YA SAME SU, SHINE MUSULMI, MUMINI BA.
ANA HAKA NE, SAI MALAMIN SHI'A MAI "ASALUS-SHI'ATI WA USULUHA, 59" MUHAMMAD HUSSAIN KASHIFUL GIDA' YACE:
الشيعة الإمامية زادت ركناً خامساً وهو الاعتقاد بالإمامة
"SHI'A SUN QARA RUKUNI NA BIYAR SHINE QUDURIN IMAMA"
ZA A IYA CEWA RUKUNI NA 6 NE, BA NA BIYAR BA, KO MUCE SUN RAGE RUKUNI DAYA, SAI SUKA QARA DAYA, YA ZAMA NA BIYAR, DOMIN DAMA RUKUNAN DA MUKAYI ITTIFAQI A KANSU BIYAR NE.
KO YAYA DAI, LAMARI NE DA YA HAIFAR DA SABANI, MUSAMMAN BAYAN HUKUNTA WANDA BAI BADA GASKIYA DA SHI BA, KAMAR YA QARYATA MANZANNI NE, WATO DAI, YA FITA DAGA ISLAM.
A "TALKHISUS SHAFIY NA DUWSIY, 4/131" DUWSIN YA CE:
ودفع الإمامة كفر كما أن دفع النبوة كفر لأن الجهل بهما على حد واحد
"YADDA KORE ANNABTA YAKE KAFIRCI, KORE IMAMA MA KAFIRCI NE, HUKUNCIN DAUKE KAI DAGA GARE SU DAYA NE"
WATA MATSALAR ITA CE, MATSAYIN IMAM. HAKANE, DUK WANDA YA YARDA SHI MUSULMI NE, TOH FA, DOLE YA BADA GASKIYA DA DOKACIN ABIN DA ALLAH YAZO MASA DASHI. AMMA ZAI GA ANYI KUDU DA KARE, IDAN YAJI SABON ABU, DA BAI GAMSU ALLAH NE YA HUKUNTA SHI BA.
INA SON A FAHIMCI, GAMSUWA KO RASHIN TA, KAN ALLAH NE YA HUKUNTA IMAMA, DALILI NE DA WANI ZAI QUDURCE TA KO YAYI WATSI DA ITA. KENAN, HANYA DAYA DA ZA A WARWARE SABANIN, ITACE TATTAUNAWA CIKIN LUMANA, DON A GAMSAR DA KOWA "EY KO A'A" BISA KARANTARWAR AL-QUR'ANI.
IMAM KHUMAINIY, CIKIN "AL-HUKUMATUL ISLAMIYYA 52" YACE:
إن من ضرورات مذهبنا أن لأئمتنا مقاماً لا يبلغه ملك مقرب ولا نبي مرسل
"DOLE NE A MAZHABAR MU, A QUDURCI IMAMAN MU SUNA DA WANI MATSAYI DA DUK KUSANCIN MALA'IKA (DA ALLAH) KO WANI MANZO DA AKA TURO, BAI KAI SHI BA"
MUHAMMAD JAWAD MUGNIYA "TAFSIRIN KASHIF 1/197" YA CE:
إن قول الإمام نبياً كان أو وصياً هو قول الله
"LALLAI MAGANAR IMAMI; ANNABI KO WASIYYI; DAI-DAI TAKE DA MAGANAR ALLAH"
MUZAFFAR A "AQA'IDUL IMAMIYYA 70" YACE:
ونعتقد أن الإمام كالنبي
"MUN QUDURCI CEWA IMAMI KAMAR ANNABI NE"
BANBANCIN SU TA FUSKAR WAHAYI NE, KAMAR YADDA KASHIFUL GHIDA' YACE A SHAFI 59:
إن الإمام لا يوحى إليه كالنبي وإنما يتلقى الأحكام منه مع تسديد إلهي
"LALLAI IMAMI BA A YI MASA WAHAYI IRIN NA ANNABI, SHI YANA KARBAR HUKUNCE-HUKUNCE NE TA HANYAR RUHI DAGA ALLAH"
A LURA CEWA WANNAN RUKUNIN DA 'YAN SHI'A SUKA QARA, YA BAYU GA BUDE KOFAR WASU HUKUNCE-HUKUNCE DA IMAMI ZAI KARBO DAGA ALLAH, YA ISAR DASU GA MABIYAN SA.
ASHE BA MATSAYIN AKE JA DASHI BA, AMMA ANA SARA NE ANA DUBAN BAKIN GATARI! ALLAH S.W.T. YA CE:
اليوم أكملت لكم دينكم وأتممت عليكم نعمتي ورضيت لكم الإسلام دينا
"A YAU NA CIKA MUKU ADDININ KU, NA CIKA NI'IMA TA A GARE KU, KUMA NA YARJE MUKU MUSULUNCI A MATSAYIN ADDINI"
KENAN, IDAN WANI YAZO DA WASU HUKUNCE-HUKUNCE SABABBI, DOLE AYI TAKA-TSAN-TSAN, DON KAR A MANTA DA MAGANAR ALLAH, A QOQARIN BIYAYYA GA ALLAH.
A HANU DAYA, ALLAH YA YARJEWA MUTANE MUSULUNCIN DA MUKA FARA DA RUKUNAN SA, GABANIN QARIN RUKUNI NA BIYAR KO NA SHIDA, WATO IMAMA DA 'YAN SHI'A SUKAYI.
TO SAI ABIN YA ZAMA WANI IRI, GASHI MUN DAUKO TAFIYA TARE, TIRYAN-TIRYAN, KAMAR YADDA QUR'ANI YA NUSASH-SHE MU, SAI 'YAN SHI'A SUKA FUTO DA WADANNAN QARE-QAREN, KAMAR YADDA SHI MALAMIN SHI'A KASHIFUL GIDA' YA FADA.
KENAN IDAN ZAMU HADU A KAN QUR'ANI, SAI MU TSAYA GA MUSULUNCIN MUTUM KO KAFIRCIN SA, GWARGWADON RUKUNAN DA QUR'ANI YA TABBATAR.
ME KUKE GANI?