Monday 29 May 2017

An sanya mashi qwaya a jikkarsa a qasa mai Tsarki

HATTARA JAMA'A MUSAMMAN MASU ZUWA KASA MAI TSARKI (SAUDIYA), WASU NA SANYA
WA WASU MIYAGUN KWAYOYI A CIKIN KAYANSU!!!
A Kasar Musulunci ta Saudiya duk wanda aka
kama tare da miyagun kwayoyi suna aiwatar da
hukunci mai tsanani akansa wanda cikin ikon
Allah hakan da suke yi ya rage yawan mabarnata
a fadin kasar.
A cikin yan kwanakin nan wani bawan Allah dan
kasuwa dan jihar Kano ya tafi Kasa mai Tsarki
don yin Umrah shi da iyalinsa ashe wani azzalumi
daga nan ya sanya wa kayansa kullin tulin
kwayoyi shi kuma bai sani ba sai da ya kammala
aikinsa yana niyyar komowa gida ashe jami'an
tsaro tuni suna bibiyarsa har suka kama shi,
bawan Allahn gashi ya tabbatar da jikarsa ce
amma kuma baisan da ansa kwayar ba. Dan
uwansa yana gaya mani lallai suna da yaqinin
dan uwansu mutumin kirki ne wanda da wuya ya
aikata hakan, wannan bawan Allah yanzun haka
yana tsare ita kuma iyalinsa an maido ta gida.
Insha Allahu muna fata zaiyi nasara da wannan
zargi da ake masa kasancewar Kasar Saudia ba
azzaluma bace, Muna rokon Allah ya kare
wannan bawa nasa ya kuma tona asirin mutanen
da ke aikata wannan danyen aiki.
JAN HANKALI
Akwai barazana sosai kan irin wannan tunda
akwai mutanen da sun kware wurin shigar da
miyagun kwayoyi a kasar Saudia saboda haka ga
duk masu zuwa Umrah ko Aikin Hajji su sa ido ga
kayayyakinsu tun daga nan kasa Nigeria har
zuwa Kasar Saudiya.
Su ma Hukumominmu wajibi ne su kara
tsaurarawa don kaucewa faruwar irin wannan.
Ita kuma Kasa Mai Tsarki Allah yayi masu
jagoranci Amin

No comments:

Post a Comment