Saturday 27 May 2017

MURIDAN DARIQAR TIJANIYYA SUN QARA YIN TA'ADDANCI


Cikin masallacin kenan yadda suka maida shi
             Duk da haqilo da tunqahon da Mabiya dariqar Tijaniyya su ke yi na cewa sun fi kowa zaman lafiya da son zama lafiya wannan bai hana su afka ma al'ummar da ke masallacin Jan Bango kusada Hasumiya Katsina ba, bayan sun afkama masu su ka balle kwanon masallacin da tagoginsa haka kuma suka ciccire fankokin cikin masallacin sannan suka jikkata mutum uku.
Duk sun dauki wannan matakin ne a cewar su don daukar hukunci akan wai wani Malamin da ke karatu ya zagi Annabin mu Muhammad (S.A.W). Dr. Djibo Malami ne wanda yake karantar da sunnar Annabi Muhammad (S.A.W) a wannan unguwa wanda ya na cikin karatu ne a ranar Alhamis 25/05/17 tsakanin magriba da Isha'i inda anan ne suka rinqa afkowa suna zage-zage abun kamar wasa har suka fara amfani da makami inda anan ne suka raunata mutum uku ciki harda Dr.Djibo. Allah ya sa ka ma hukumar yan sanda da alheri don ana cikin hatsaniyar ne Allah ya kawo su su kai kokarin kwantar da tarzomar da kuma daukar daukar Malamin domin ba shi kariya don yunkurin muridan shine su hallaka shi da duk wani dan izalar da su ka ci karo da shi.
 Muna fatan hukuma ta dauki mataki na gagawa da hukunta duk wanda aka samu da laifi, haka kuma duk wadanada aka samu da laifin su gyara wannan masallaci domin irin wannan na uku kenan yana faruwa a yan shekarun nan don in ba a manta ba waccan shekarar haka a ka yi a masallacin Juma'a na Rafukka, muridan ne su ka zo su kai irin wannan ta'asa karshe aka zo akai ta sulhu da neman yafiya wanda a wannan karo al'umma sun ce ba za su yadda da hakan ba da fatan wannan koken zai isa inda ya dace. Allah ya hada kan musulmai.

Daga kasa hotunan irin wulakancin da muridan su kai ma dakin Allah ne.




                                               


No comments:

Post a Comment