Tuesday 16 May 2017

A TABBATAR DA TSARI NA SHAR’IAR MUSULUNCI DA KUMA KAFA HUKUMAR HISBA

A TABBATAR DA TSARI NA SHAR’IAR MUSULUNCI DA KUMA KAFA HUKUMAR HISBA
SAKO DAGA MATASAN MALAMAN JAHAR KATSINA
          A wa’azin da ya gabata ranar Asabar 13/05/2017, wanda Matasan Malaman su ka gabatar da wa’azi na karshe a cikin jerin wa’azuzukan da su ke gudanarwa duk bayan sati biyu, Wa’azin ya guda na ne a cibiyar baje kolin Sunnah wato masallacin Kandahar, inda gammayar malaman suka yi kira ga wannan gwamnatin cewa suna kira gareta da ta farfado da wannan tsarin wanda aka yi fafutikar tabbatar da shi a zamanin marigayi Malam Umaru Musa Yaradau. A kuma kafa hukumar Hisba a jihar domin yaqi da miyagun dabi’u mussamman zinace-zinace, fyade, shaye-shaye da sauransu.
Malam Zakariya’u Aliyu Sandamu (Limami na 2 a Masallacin gidan Gwamnati) ya yi kira da a dauki mataki don magance matsalar fyade inda ya bayyana cewa korafe-korafe sun yi yawa game da yi ma yara qanana fyade in da har ya bayyana yadda kwamishinan ‘yan sanda ya tabbatar cewa a cikin wannan shekarar an yi ma yara aqalla sama da 100 fyade. Wanda rahoto yazo masu, akwai da yawa ma wanda rahoton bai kai ga hukumar ba.
Haka nan kuma a wajen wa’azin an yi kira ga Gwamnati da ta duba yiwuwar maida makarantun kwana da aka kashe. Sannan kuma a duba yiwuwar  bada hutu a lokacin azumi don samun damar yin ibada yadda ya kamata.
Malaman da su ka gabatar da Wa’azin
1.     Malam Zakariya Aliyu Sandamu
2.     Mal Bunyaminu Muhd Balarabe
3.     Mal Safiyyu Alqasim
4.     Mal Abdur-rahim Sabi’u R/dadi
5.     Mal Abubakar Mai Kano
6.     Mal Haruna Sani Muhd
7.     Mal Aminu Usman
8.     Mal Munir Isah Kerau
9.     Mal Abdullahi Ayuba
10.                        Mal Shamsuden Abdul-Karim
11.                        Mal Muhd  Usamatu  
Hassan Kabir Yaradua
Ya ruwaito.

16/04/2017

No comments:

Post a Comment