Friday 21 October 2016

BA TILASTA MATA AKAYI BA TA MUSULUNTA (Sheik Yakubu Musa Katsina)


BA TILASTA MATA AKAYI BA TA MUSULUNTA 

(Sheik Yakubu Musa Katsina)


Maqaryaciyar jarida PUNCH wanda ta ruwaito labarin
A yunkurin kungiyar kiristoci ta kasa reshen Jihar Katsina na muzanta wata yarinya wadda ta musulunta mai suna Habiba Isiyaku, (Yar garin wawar kaza dake karamar hukumar Kankara) kungiyar ta dau nauyin wata jarida mai suna PUNCH don ta yi cin mutunci ga Martaba Sarkin Katsina Alh. Abdulmumini Kabir Usman ta hanyar zargin Sarkin da saida yarinyar, a wata ruwayar kuma cewa shi da kansa Sarkin ne ya aure ta. 

            A ranar Talatar da ta gabata ne (17/10/2016) Sheik Yakubu Musa Katsina ya zanta da manema labarai inda ya yi masu karin haske akan lamarin.
Takardar asibitin ce da CAN ta yo, an sanya an haife ta 2001
Shehin malamin ya bayyana cewa yarinyar ba tilasta mata akai ba ta musulunta ita da kanta da ganin damarta ta Musulunta, kuma ba a fadar Mai Martaba Sarki ta musulunta ba a cen garinsu wajen limamin garinsu ne ta  musulunta. Don haka, me ye na yarfe ga sarki da kuma jagororin Muslunci a cikin lamarin?.
Ku duba suna Habiba Isiyaku

Malam ya kara da cewa ba a san shuwagannin Addini da yarfe da sharri ba amman sai ga shi CAN ta yi wannan mumunan yarfe inda Sakataran CAN na karamar hukumar Malumfashi Musa Bahago ya canza wa 
Certificate  din ta ya gwada a 1999 a haife ta
Habiba Isyaku takardun haihuwa. Ya yi amfani da damarsa na Principal a makarantar da yarinyar take ya canza mata takardun haihuwa da Certificate din ta na kamala makaranta (Correction fluid ya sa ya
 An goge wajan shekara an sa wani
goge sai ya sake rubutawa da biro) . Amman cikin ikon Allah asirin Musa Bahago ya tonu bisa kokarin wasu ‘Yan Hisba na yankin inda su ka bi diddigin takardun yarinyar su ka gano irin canje-canje da wannan Principal ya yi duk saboda a


anan  za ku ga 1999 ne aka haife ta

muzanta Mai Martaba Sarki da kuma addinin Musulunci. Yarinya ce mai shekaru 18 amma  su (CAN) suka je wani asibiti a ka maida mata shekaru 14 don su ji dadin cin mutuncin Muslunci da cewa an aurar da karamar yarinya.




M. A. Ashafa
Malam Abubakar Ashafa (Shugaban Kwamitin Musuluntarwa na Jihar Katsina) ya bayyana mana irin yadda shugaban CAN na jihar Katsina ya nemi su je wajen Sarki domin bada hakuri akan abun da ya ji an ce an buga a jaridar PUNCH, amma da su ka je wajan Sarki sai ya bige da suka ga Sarki da cewa ana aurar da kananan yara, ana kaza da kaza. Anan take Martaba Sa’in Katsina ya ba shi amsa kamar haka “Ita wannan yarinya yanzu Musulma ce, kuma Musulunci ne zai yi hukunci a kanta. Kuma yarinyar da ta kai shekara 9 ko ta fara al’ada to ba mai hukunta ta sai Musulunci”. Daga karshe Malam Ashafa ya bayyana irin yadda su ke kokarin ba yara kanana hakkin su in sun Musulunta ta hanyar ba su zabin wajen zama, karshe yaran su za bi zama a hannun Musulmai, saboda irin muzgunawar da su ke fuskanta in sun koma wajen iyayensu kiristoci.

Daga karshe muna kira da babbar murya ga Hukumar Ilimi da gwamnatin Jihar Katsina su dau mataki ga Musa Bahago Principal kan wannan kulla-kulla da yayi na canza takardun makarantar Habiba. Haka kuma muna kira ga kungiyar CAN da ta shiga taitayinta ta daina yin katsalandan a harkar addininn wadansu.




Thursday 20 October 2016

TARON BADA KYAUTTUTUKA 2016

Fityah Center For Da’awa and Education Katsina
TARON BADA KYAUTTUTUKAN
Musabaqar AlQur'ani
Kacici-Kacicin Alu Wal Ashab
Kyautukan karramawa ga wasu 
Kyautukan Laptop, Waya J7, Quranic Digital, ga wadanda su ka ci Musabar Al-Al Wal Ashab





 
Dr. Muhd Muslim Ibrahim (DVC AL-QALAM UNI) Darakatan Fitya

Hassan Kabir Yar'adua (Sakataren Fitya)

Bada kyauta ga makaranta da tai (1) Kulafa'ur Rashidun

Dalibin da yayi na (3) a Musabaqar AlQur'ani

Dalibar da tai na (1) a Musabaqar Alqur'ani


Kyautar Waya GALAXY J7 ga wanda ya ci gasar AL-AL WAL ASHAB

Kyautar Waya GALAXY J7 ga wanda ya ci gasar AL-AL WAL ASHAB

Kyautar Waya GALAXY J7 ga wanda ya ci gasar AL-AL WAL ASHAB

Kyautar Computer Acer ga wanda ci gasar AL-AL WAL ASHAB

Engr. Yusuf Adamu Dantsho ke amsar kyautar karramawa daga Darakta


Alh Mustapha Musa Yar'adua na amsar kyautar karramawa

Dr. Muslim, Hassan Kabir Yar'adua ke mika kyauta ga Husain Kabir Yar'adua a madadin Alh Nura Karmanje

Ibrahim Gafai ke amsar ma Alh Ali Sarkin Magina kyauta

Malama Murja Ibrahim Duwan ke amsar kyautar karramawa

Liman Abdullahi, Alh Shehu Saulawa, Alh Mustapha Musa, Dr. Muslim, Engr. Yusuf m Mal Munir Daura, daga baya Yusuf Hassan Buhari, Abdulkarim Khairu

An gudanar da taron a ranar Juma'a 12/01/1438- 14/10/2016 da gamma a Masallacin Juma'a na Abu Hurairah da ke unguwar Kwado Katsina.







         


 


Wednesday 19 October 2016

KO JAHILCI KO SON ZUCIYA

Dr. Muhd Rabiu Rijiyar Lemu

KO JAHILCI KO SON ZUCIYA!!

Duk wanda ka ga ko ka ji yana sukan Ahlussunnah da cewa suna kafirta musulmi, to za ka ga ko dai jahili ne, bai san addini ba, bai san tarihin kungiyoyi da akidunsu ba a musulunci, KO kuma mai son zuciya ne da gaba da sunnah da Ma'abotanta.
Wani abun mamaki zaka samu masu cewa Ahlusunnah suna kafirta musulmi suna kawar da kai daga wadanda suka fi kowa kafirta musulmi a duniya, wato shi'a, wadanda suka kafirta muminan farko, Sahabban Manzon Allah S.A.W. da duk wanda ya bi tafarkinsu har zuwa ranar Alkiyama.
Babu wata kungiya ko jama'a da suke rabuwa da addinin musulunci da suka fi Shi'a kafirta musulmi da halatta jininsu da dukiyoyinsu.
A gefe guda kuma babu wasu Jama'a da akidarsu da littafansu suke cike da ka'idoji da sharuddai na kafirtawa kamar Ahlussunnah.
Amma yaya zaka yi da jahilin da bai san shi jahili ba ne, ko kuma mai son zuciyar da ya biye mata.
Allah ka raya mu a kan Sunnah, ka kashe mu muna Sunnah, ka tashe mu cikin Ahlussunnah.

Monday 17 October 2016



مركز فتية للدعوة و  التربية و التعليم
Fityah Center For Da’awa and Education
No, 71, Lokon Makera. Gwale L.G.A., Kano State, Nigeria
Phone: 08160943888 Email: fityah11431@gmail.com
Katsina State Chapter: 08030524842, 07035633698



 




         










 


TARON BADA KYAUTUTTUKA WANDA CIBIYAR FITYA TA GABATAR
RANA: JUMA’A  13/1/1438H   14 OCT 2016.
Ø Kyautuka ga daliban da su ka yi fice a Bita (Samina)
Ø Kyautuka ga daliban da su kai zarra a musabaqar Alqur’ani mai girma
Ø Kyautuka ga makaratun da su kai fice a kacici-kacicin iyalai/sahabban Annabi (S.A.W)
Ø Kyautukan  Laptop, Wayar hannu, Digital Qur’an ga wadanda su ka ci nasara a gasar Al-Wal- Ashab Wadda kasar Saudia ta ke gabatarwa duk shekara.
Ø Kyautukan karramawa ga wadanda su kai fice wajen bada gudummuwa
         
  
          Taron ya gudana a  Masallacin Juma’a na Abu Huraira B/Head Quarter Yan Sanda Katsina. Da misalin karfe 4:00 na yamma, inda aka sami mahalarta kamar haka
1.     Daraktan Fitya na Kasa Dr. Muhd Muslim Ibrahim (DVC ALQALAM UNI)
2.     ALH Mustapha Musa Yar’adua

3.     Engr. Yusuf Adamu Dantsho
4.     Mal Munir Sani
5.     Mal Murja Ibrahim Duwan
6.     Mal Haruna Sani Muhd (Shugaban Fitya na Jihar Katsina)
7.     Shuwagabannin Malaman Makarantun Islamiyyu
8.     Daliban Islamiyyu

9.     Wadanda su kaci kyautuka
10.             Mambobin Fitya

11.             Sauran al’umma


Hassan Kabir Yar’adua
          Magatakarda