BA TILASTA MATA
AKAYI BA TA MUSULUNTA
(Sheik Yakubu Musa Katsina)
 |
Maqaryaciyar jarida PUNCH wanda ta ruwaito labarin |
A yunkurin
kungiyar kiristoci ta kasa reshen Jihar Katsina na muzanta wata yarinya wadda
ta musulunta mai suna Habiba Isiyaku, (Yar garin wawar kaza dake karamar
hukumar Kankara) kungiyar ta dau nauyin wata jarida mai suna PUNCH don ta yi cin
mutunci ga Martaba Sarkin Katsina Alh. Abdulmumini Kabir Usman ta hanyar zargin
Sarkin da saida yarinyar, a wata ruwayar kuma cewa shi da kansa Sarkin ne ya
aure ta.
A ranar Talatar da
ta gabata ne (17/10/2016) Sheik Yakubu Musa Katsina ya zanta da manema labarai
inda ya yi masu karin haske akan lamarin.
 |
Takardar asibitin ce da CAN ta yo, an sanya an haife ta 2001 |
Shehin malamin ya bayyana cewa yarinyar ba tilasta mata akai ba ta
musulunta ita da kanta da ganin damarta ta Musulunta, kuma ba a fadar Mai
Martaba Sarki ta musulunta ba a cen garinsu wajen limamin garinsu ne ta musulunta. Don haka, me ye na yarfe ga sarki
da kuma jagororin Muslunci a cikin lamarin?.
 |
Ku duba suna Habiba Isiyaku |
Malam ya kara da cewa ba a san shuwagannin Addini da yarfe da
sharri ba amman sai ga shi CAN ta yi wannan mumunan yarfe inda Sakataran CAN na
karamar hukumar Malumfashi Musa Bahago ya canza wa
 |
Certificate din ta ya gwada a 1999 a haife ta |
Habiba Isyaku takardun
haihuwa. Ya yi amfani da damarsa na Principal a makarantar da yarinyar take ya
canza mata takardun haihuwa da Certificate din ta na kamala makaranta
(Correction fluid ya sa ya
 |
An goge wajan shekara an sa wani |
goge sai ya sake rubutawa da biro) . Amman cikin
ikon Allah asirin Musa Bahago ya tonu bisa kokarin wasu ‘Yan Hisba na yankin
inda su ka bi diddigin takardun yarinyar su ka gano irin canje-canje da wannan
Principal ya yi duk saboda a
 |
anan za ku ga 1999 ne aka haife ta
|
muzanta Mai Martaba Sarki da kuma addinin Musulunci.
Yarinya ce mai shekaru 18 amma su (CAN)
suka je wani asibiti a ka maida mata shekaru 14 don su ji dadin cin mutuncin Muslunci
da cewa an aurar da karamar yarinya.
 |
M. A. Ashafa |
Malam Abubakar Ashafa (Shugaban Kwamitin Musuluntarwa na Jihar Katsina)
ya bayyana mana irin yadda shugaban CAN na jihar Katsina ya nemi su je wajen
Sarki domin bada hakuri akan abun da ya ji an ce an buga a jaridar PUNCH, amma
da su ka je wajan Sarki sai ya bige da suka ga Sarki da cewa ana aurar da
kananan yara, ana kaza da kaza. Anan take Martaba Sa’in Katsina ya ba shi amsa
kamar haka “Ita wannan yarinya yanzu Musulma ce, kuma Musulunci ne zai yi
hukunci a kanta. Kuma yarinyar da ta kai shekara 9 ko ta fara al’ada to ba mai
hukunta ta sai Musulunci”. Daga karshe Malam Ashafa ya bayyana irin yadda su ke
kokarin ba yara kanana hakkin su in sun Musulunta ta hanyar ba su zabin wajen
zama, karshe yaran su za bi zama a hannun Musulmai, saboda irin muzgunawar da su
ke fuskanta in sun koma wajen iyayensu kiristoci.
Daga karshe muna kira da babbar murya ga Hukumar Ilimi da gwamnatin
Jihar Katsina su dau mataki ga Musa Bahago Principal kan wannan kulla-kulla da
yayi na canza takardun makarantar Habiba. Haka kuma muna kira ga kungiyar CAN da
ta shiga taitayinta ta daina yin katsalandan a harkar addininn wadansu.