Matsalar Yaxuwar Fyaxe! a Katsina Laifin Wa?
Kwanakin
baya wani babban jami’in 'yan Sanda ya zo ya same mu yake bayyana mana
takaicinsu musamman ogansu kwamishinan Yan Sanda na Jihar Katsina C.P Muh'd
Wakili, kan yadda yaxuwar fyaxen qananan yara ta zama ruwan dare a wannan jiha
tamu. Jami’in ya labarta mana irin qoqari da jajircewar kwamishinan 'yan sandan
kan yaqi da wannan mummunar xabi’a. Cikin jawabinsa wanda ya xau hankalina
kuma nima na shaidi hakan shine, yadda mahukunta ke wancakalar da case na fyaxe
musamman idan suna ganin za su mori wani abu daga wanda ake tuhuma.
Ina jin ban
tava baku labarin wani mai yin fyaxe da qananan yara ba wanda aka kama cikin
azumi da rana qiri-qiri da yara guda biyu.
Shi wannan mai yin fyaxen ya shahara da aikata wannan kaba’ira, kuma ko
an je ga hukuma sai ya sha, kwatsam da Allah ya yi nashi nufin sai ya haxu da
wani jajirtaccen uba mai son bi ma xiyarsa haqqi, ya zo wajenmu yana kuka cewa
don Allah mu taimaka mashi a qwato ma xiyarsa haqqinta, sai mu ka ce mashi za
mu taimaka amman da sharaxin duk rintsi duk wahala ko a xan cinna mashi kuxi ba
zai ja da baya ba, ya tabbatar mana da cewa wallahi ko mutuwa zai yi kan
a hukunta mazinacin. A hakan ne Allah ya taimaka a kai ta faxi-tashi duk da
tarin abokai da masu isa da shi mazinacin ke gare shi sai da aka kulle shi. Yanzu haka in bai sa wasa ba qila ya kusan haxa hardarshi, ga xan wanki da
yake yi ana aje mai anini, yanzun shekarar shi ta uku saura shekara ashirin da
biyu. Ba a fi sati ba wani case xin kuma wanda uban yarinyar ya salwantar da
mutuncin yarinyar shi ba. Cikin wannan labarai za mu fahimci sakacin
iyaye ma’ana da an xan basu kuxi 'yan qalilai sai su salwantar da mutunci
xiyarsu.
Mahukunta
ina nufin alqalai gaskiya suna taimakawa wajan yaxuwar wannan varna ta fuskar
qin hukunta waxanda aka kama a irin wannan laifi, shi kanshi kwamishinan yan
sanda na san wannan na daga cikin takaicinsa, don so da yawa jami’ansa za su
gabatar da mai laifi amman qarshe da sun je kama mai rin wannan laifi sai su ga
ai sun tava gabatar da shi, A vangaren jami’an tsaron ma kamar yadda vangaren
iyaye, mahukunta to suma suna taimakawa wajan yaxuwar fyaxen ta yadda za su yi
ta wahalar da miskinin uba ta hanyar zirga-zirga dss hakan sai yasa wasu iyayen
su qosa qarshe su ga kuxin da su kashewa sun yi yawa don haka sun haqura.
- Kira na musamman ga Majalisar dokoki ta jihar Katsina shi ne akwai dokar da aka yi wadda ta ke Magana kan hukunta masu wannan xabi’a, muna qara tuni da Majalissar cewa ta dubi girman Allah ta zartas da wannan doka.
- Kira na biyu ga Malamai magada Annabawa cewa, lallai Malamai suna da rawar da za su taka wajan magance wannan annoba musamman ta hanyar huxubobi, wa’azuzzuka dss.
- Kira ga qungiyoyin lauyoyi musammaan na mata cewa su ma fa suna da babbar rawa wajan share ma waxanda aka zalunta ta hanyar fyaxe.
- Kira na qarshe ga sauran al’umma shine su ne su ka fi kowa taka rawa wajan daqile wannan musiba ta hanyar kula da yara acikin ungawanni, makarantu dss.
Hassan Kabir
Yar’adua
15/11/2018