Wadanan da wasu kiraye-kirayen sune abubuwan da Malamai guda 11 su ka dukufa suna yi don fadakar da wannan gwamnati.
Saturday, 12 August 2017
A MAIDO DA SHARI'AR MUSULUNCI A JIHAR KATSINA
An yi kira da a maido da sharia'ar musulunci kamar yadda aka kafa ta a shekarun da su ka gabata. Malam Haruna Sani Na'ibin limamin Juma'a na Massalacin Jabir Bin Abdullahi da ke unguwar Kwado ya bayyana haka a wani wa'azi da aka gabatar a daren yau. Malamin ya bayyana haka ne da kuma yin kira da a kafa hukumar hisba. Daga nan Malamin ya ja hankalin jagoriri da su ji tsoron Allah su inganta aikin hajjin bana wanda shine aikin hajjin da alhazai su ka fi biyan kudi amman kuma su ka fi wulakanta.
Thursday, 10 August 2017
RAN GADIN MU ZUWA ASIBITOCIN QANANAN HUKUMOMI
RAN GADIN MU ZUWA ASIBITOCIN QANANAN HUKUMOMI
Bayan rubutun da abokina Mubarak Rabi’u (Da’awah) yayi kan abokinsa
da ya je General Hospital Katsina amman bai samu kulawa ba qarshe sai dai ya
tafi wata Private asibiti akayi mashi magani. Wannan ne ya sa mu ka shirya tsaf
domin fara ran gadin wasu daga cikin asibitocin gwamnatin jihar nan domin gano
irin matsalolin da al’umma su ke fuskanta a cikin su fatan ko za a gyara.
Cikin ikon Allah jiya mun fara ziyartar Comprehensive Health Care Batagarawa
L.G wanda shine babban asibitin da ke cikin garin Batagarawa, Batagarawa L.G
gari ne wanda babu gari mai fadin qasa a duk fadin jihar Katsina kamar sa amman
abun da mu ka gani kuma mu ka ji ya tayar mana da hankali matuqa.
ABUN DA MU KA JI KUMA MU KA GANI
Mun isa asibitin wajan 10:00pm isar mu ke da wuya mu ka shiga Male
Ward anan mu ka tarar da yara Yan Makaranta guda 3 ba su lafiya, yaran su kadai
ne sai wani yaro Prefect anan ne mu ka tambayi lafiyars u inda suka bayyana mana cewa kwanan su uku anan
amman ba wata kulawa da ake masu, ba
wani magani da aka rubuta masu ko aka basu, sai dai allurori da aka rubuta
masu, a cikin dakin na Male ward babu tsafta ko kadan don kai kace wata ‘yar
bola bola ce a ciki, sannan kofofin dakin gaba daya a 6alle su ke, ga sauro ga
sanyi don gaskiya duk mai lafiyar da ya je ya kwana a dakin to lallai shima ana
iya bashi gado to ina ga marar lafiya. Yaran wallahi sun zama abun tausai
matuqa.
Bayan mun fito sai muka nufi Female ward anan ma mun ga yadda
marasa lafiya su ke fama da kiran wani ma’aikacin jinya daga nan a kira shi ace
jinin ya qare sai ka ji acan ana qwala
masa kira ana ga allurarr an kawo.
Bayan mun fito mun samu zantawa da wani mutum a cikin asibitin inda
mu ka tambaye shi ya mu ka ga ma’aikacin can na jinya sai kiran shi ake baya nan baya can, sai mutumin ya bayyana
mana cewa ai shi kadai ne ke wannan aikin kullum haka yake fama a duk fadin
asibitin ma’aikacin jinyar shi kadai ne. hakika a yadda mu ka ga ma’aikacin
jinyar ya sadaukar da kansa ga wannan aiki sai na ga ai shi kanshi abun tausai
ne. Mun je mun same shi mu ka gaisa mu ka tambaye shi ko shi kadai ne
ma’aikacin jinya a cikin daren nan inda ya bayyana mana cewa ai duk fadin
asibitin ma shi kadai ne kodayaushe yana cikin asibitin. Ya qara da ce mana
aikin ya mashi yawa matuqa kawai dai yana yi ne don Allah, haka kuma ya bayyana
mana cewa marasa lafiya daga kusan local
govt uku duk anan asibitin ake turo su. Rimi Local G da Charanchi na cikin su inda har y ace mana yanzun haka
akwai file na wani mara lafiya da aka turo mashi daga Rimi Local govt, sannan
yace mana cikin dakin matan can akwai mara lafiyar da aka turo daga Jibia Local
govt. ya bayyana mana cewa ai qwamma ma nan asibitin duk da ana ganin ta
Comprehensive ce duk da ta Rimi General ce amman suna turo masu marasa lafiya
wanda hakan ke gwada can Rimi sun fi fuskantar wannan matsalar. Wannan yasa a
Ran gadin mu na gaba zamu tsallake Rimi da Charanchi muna fatan za a qara samun
bayani daga wajan mazauna garuruwan.
SHAWARAR MU GA GWAMNATI
1. Muna mai bada shawara musamman ga mai girma gwamna wanda kulawar
lafiyar al’ummar jihar Katsina duka tana wuyansa (ba Ciyamomi da mun ambace su)
cewa ayi kokari a inganta asibitocin nan don gaskiya suna bukatar gyara fiye da
gyaran da akayi ma makarantun boko,
sannan suna bukatar ma’ikata don da yawa daga cikin asibitocin nan ba
ma’aikatan lafiya balle aje ga masu maintenance dss. Kuma gyaran wadanan
asibitocin yafi a ciyo bashi a gina wasu asibitocin don wadanada za a gina din
suma qarshe in ba a dau matakin gyaran tsaffin ba to kango za su koma.
2. Muna da dalibai masu yawa wadanda sun yo karatun nan amman suna
nan suna zaman banza da gara-rambar yawo da CV. Inda za a dauke su lallai da an
rage abubuwa da yawa.
Wannan shawarwarin ba wanda yafi cancanta a bas u kamar mai girma
gwamna ko ince gwmantin jiha don wani na iya tunanin cewa mi ya shafi gwamnatin
jiha da asibitin Local govt to wannan sai ya koma ya qara bincike lallai zai
gano cewar gwamnatin jiha a mataki na farko ita ke da wannan alhaki. Sai kuma ga
shi duka qanann hukumomin aljihun suna qalqashin gwamna to kun ga ko anan ma
dole ne ita za a daura ma alhaki.
Daga qarshe wannan Rangadi mun yi shi ne ba don komai ba sai don
fatan za a bincika a kuma dau mataki har ga Allah ba mu yi shi ba da nufin
bayyana gazawar gwamnati ko su ka gare ta ba.
Mu kasance a ran gadi nag aba Insha Allah
Hassan Kabir Yaradua
08/10/2017
Subscribe to:
Posts (Atom)